MISBAH BY SA'ADATU WAZIRI GOMBE

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI – My Blog

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 3  BY SA’ADATU WAZIRI

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

ba zan taba zama sanadin samun matsalar zumuncin da iyayen Deeni da na Farida suka gina ba, tun kafin ma Deeni ya san da ni.”
Nan take ta yanke wa kanta hukuncin abin da za ta yi. A hankali ta matsa ta kunna wutar falo, haske ya mamaye falon sannan matsa gareshi tare da shafar kansa ta ce, “lafiya kuwa, Deenina da ba ya son duhu yake zaune cikin duhu? Ni dai na san ba karamin abu ne zai sa Deeni ya manta Misbansa a gidansu ba.” יי
“Wa ya taba min miji, hala (poultry) dinka ne ya samu matsala, shi ne ka dai na san zai iya daga ma hankali.” Nan ya dago kai ya kalle ta, ta sakar masa murmushi, wani irin sabon son ta ya ji yana shigar sa yana tsuma shi, shi kam bai san yawan son da yake yi wa Misbah ba. Ganin fuskarta mai kwarjini da cikar kamala ya sa ya ji ya samu wani irin sukuni da natsuwa, ya ji wani irin sukuni a zuciyarsa.

Kwanciya ya yi a jikinta tare da kankame ta yana fadin, “ina sonki Misbahna, ba ni da kamarki a rayuwar nan, yana fadi yana fidda wani irin numfashi, santinsa ko na tattare da wani irin shauki na tsananin kaunar ta, ita ma kankame shi ta yi ta ce, “ina sonka nima Deeni, so sosai, wanda ba shi da iyaka.
Lumshe ido ya yi yana shakar kamshin jikinta mai sanyi da dadi tare da jin tsananin son ta da shaukinta na ratsa shi, ita ma ta ba shi hadin kai sosai saboda ganin yana bukatar hakan, duk kuwa da cewa zuciyarta bata mata dadi, tana jin tsananin son Deeni tattare da wani irin kishi wanda ya jefa zuciyarta cikin kunci. Deeni da Misbah ba su gushe a wurin ba har sai da suka yi kwanciyar aure, suka faranta ran juna, wanda wannan ba karamin natsuwa da nishadi ya sa su ba.

A wannan dare Deeni ya yi iya kokarinsa ya fada wa Misbah abin da ya faru tsakaninsa da Farida, sai dai ya san abin da zai biyo baya game da wannan maganar, don ba shiryawa za su yi ba. Ya san Misbah na da hakuri da juriya, amma in ta tashi da rigimarta, ko yaron goye bai kai ta ba, musamman a kan maganar yanzu sai ta birkice, ya rasa gane kanta, ga shi kuma alkawari ne suka yi wa juna ba sirri tsakaninsu ba boye-boye, “amma gaskiya ba zan iya fada maki wannan maganar ba Misbah, yanzu sai na rasa kanki, ni kaina ina cikin rudani balle ke.”


Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana cikin wannan zancan zucin, sai Bahijja ta tashe shi ta ce, “Deeni, ni kuwa ya kuka yi da Farida ne?” ta tambaya cikin zakuwar ji yadda suka yi, saboda tana da tabbacin cewa Deeni ba zai boye mata komai ba, hakan nan tashin hankalinsa na maganar da suka yi ras! Ya ji gabansa ya buga amma sai ya yi ta maza, ya kau da kai, ya ce “ta ce za ta yi kokarin fara makaranta in Allah ya kawo miji sai ta yi aure.” ya ba ta
Amsar bai gamsar da ita ba, amma kasancewar maganar daga bakin mijinta ya fito wanda ta yarda komai rashin dadinta Deeni na rufe ido ya fada mata. Sai dai, sam zuciarta ba ta samu natsuwa ba, to me ya faru Deeni, me ya ruda shi, tamkar ya san me ke yawo a zuciyarta, ya juyo suka kalli juna, ya lura tana masa kallon tambaya, ya janyo hannunta ya hada da na shi tare da manna ta a jikinsa kamar yanda suka saba idan za su yi wata magana mai mahimmanci, ya ce, “Misbahna ina sonki so sosai, so na gaskiya, ban taba hada sonki ba da na wata ‘ya mace, tun lokacin da na sanki na fahimci ina sonki, ban kara jin son wata diya mace ba sai ke, ban taba tunanin hada ki da wata mace ba. Kuma ni Deeni ba ni da wani ra’ayi na kara aure wannan ra’ayi na ne, sannan son da na ke maki ba zai taba barin na yi adalci tsakaninki da wata ba.
“Allah da kanshi cikin suratul Nisa’i ya ce: ‘idan kun san ba za ku iya adalci tsaka matan ku ba to, ku zauna da mace daya, shi ya fi alheri,’ to ina
Www.bankinhausanovels.com.ng
da tabbas din yin rashin adalci tsakaninki da kowacce irin mace dan haka maganar sake aure ma bai taso ba.
Nan ya shiga jaddada mata irin kaunar da yake mata, saboda tsananin shakuwar da ke tsakanin Misbah da Deeni ba macen da za ta iya jure wa wannan. Bahijja dai ta san tabbas da wata magana a kasa. Nan ta yi saurin dago kai ta kalle shi ta ce, “Deeni, maiya kawo wannan maganar, akwai matsala ne?”
Ya kallet a ya ce, “Bani da damar bayyana sirrin zuciyata sai da matsala ko hakan laifi ne?”
Kafin ma ta ba shi amsa ya janye daga jikinta tare da juya mata baya, ta bi shi da kallo ba tare da ta ce mishi kala ba saboda sanin halinsa, ya hau dokin zuciya, sai kuma ya sauko, sai dai wannan ya tabbatar mata cewar tabbas akwai wani abu a kasa,
akwai abin da yake boye mata, hakan nan ta ji nata
ran na baci, don haka ita ma sai ta kwanta ta juya
masa baya. Hakan suka kwana a wannan ranar,
sabanin da, da suke barci manne da juna. Tun daga ranar Farida ta sa Deeni a gaba da maganar lallai sai ya aure ta, tare da tuno masa soyayyarsu ta baya da irin tsaninin son da yake mata, hakan ya sa ya rage zuwa Kaduna, hakan ya sa ta canza salo ta hanyar tura masa sako ta waya, wanda hakan shi ya fi daga masa hankali fiye da komai.
Wanda tabbas duk ranar da Bahijja ta gani a wayarsa to, daga ranar babu sauran zaman lafiya
Www.bankinhausanovels.com.ng
tsakaninsu kuma zargi ba zai taba kArewa a tsakaninsu ba, hakan ya sa ya canza layin da ba kowa ne ya san da shi ba sai Bahijja, duk lokacin da yake wani aiki mai muhimmanci sai daya layin ya sa wannan dayan. ya cire
Wannan ba karamin kuntata ran Farida ya yi ba, wanda ita dai ta daura damarar auren tsohon masoyinta da soyayyarsa ke azalzalarta a kullum, son Deeni karuwa yake a zuciyarta yayin da kishin Bahijja kamar zai kashe ta, tabbas da da yadda za ta yi da ta raba Deeni da Bahijja wanda ba ta taba sanin cewa Bahijja ita ce Misbha ba, don kuwa wannan sirrin daga Deeni sai ita suka sani.
Deeni bai bata loka ba, ya gama abin da ya kawo shi Kaduna  suka koma Lagos ba shiri, yayin da yacewa mahaifinsu ya kamata tunda Lukman  kaninsa ya tasa a sa shi ya fara koyon aiki in suna hutu, tunda ya kusa kammala jami’a, in ya gama kawai sai ya ci gaba da aiki.
Tafiyar su Deeni ya fi komai ciwo gurin Farida, sai dai hakan bai sa ta hakura ba, ta sha alwashin duk yadda Deeni ke gudunta sai ta jawo shi, ta dawo da shi rayuwarta, ita ta na da tabbacin da kaunarta a zuciyar Deeni.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mama na zaune a falo Farida ta fito ta same ta, bayan ta zauna ta dube ta cikin fara’a ta ce, “Yawwa mama, da ma ina son mu yi wata magana da ke.”
Nan da nan maman ta mai da hankalinta gareta ta ce, “To Farida, ina jin ki, wace magana ce.” Sunkiyar da kanta ta yi ta ce, “Da ma maganar makaranta ce da muka yi kwanaki can da Deeni, na yanke shawarar zan koma karatu, na ga yanzu ana sai da Jamb form, na saya har na cike, sai dai a Lagos nake son zuwa, can na yi, in na dace ma su ba ni kwas din da na nema wato (Accounting), a can Uni Lag din na nema saboda ina da bukatar canjin wuri, sannan yara suna cewa za su gidan Uncle Deeni hutu, ina ganin idan kun amince sai mu tafi hutun da su, sai na rubuta Jamb dina kafin hutun ya kare.”
Mama ta yi dariya ta ce, “amma kuwa na ji dadin wannan shawara da kika yanke, tabbas kina bukatar canjin wuri da yanayi, ai can Lagos ma gida ne, sai inda kika zaba, in can gidanmu ne sai a yi wa masu aiki waya su gyara, in kuma gidan su Deeni ne duk daya ne.
Nan taji an sosa mata inda yake mata kaikayi ta ce, “Ina ga gara wurin su Bahijja, can ai ba za mu ji dadin zama mu kadai ba.
“Haka ne, in ji mama, ta fada sannan ta ci gaba da cewa “to sai ku sa rana, ku shirya ku tafi, zan yi magana da baban naku zan fada masa.

1 2Next page

Leave a Reply

Back to top button