NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 47

*_NO. 47_*

………….Aunty Ummy ce tai Knocking glass ɗin motar da Yaa Amaan ke ciki har yanzu yanata aikinsa hankali kwance, gefe ɗaya raɓar AC na ratsa sa.

       Saida yaja wasu seconds kafin ya ɗago manyan idanunsa yana kuma ɗan ɓata fuska ya sauke glass ɗin a hankali.
       Aunty Ummy dake tsaye ta ranƙwafo tana faɗin, “Angon nan kodai ɗaukarka zamuyi mu kaika?”.
     Guntun murmushi yayi kaɗan yana buɗe murfin da faɗin, “Uhm-Uhm Aunty, zanma kai kaina ne, dan nafiku zumuɗi, nabaku dama ku gama nakune”..
    Dariya sosai tayi ita da aunty Nurse dake bayanta, a ransu suna mamakin irin wannan dogon sharhi haka tamkar ba shiba.
    Shikam tuni ya basar kamar bashine yay maganarba, aunty Nurse ta karɓi kayan hannunsa daya tattaro a motar, bata yayi babu musu. Gaba yay suna binsa a baya, Aunty Nurse da aunty Ummy na tsokanarsa suna ƴar dariya.
    Uffan baicema kowannensu ba har suka isa ƙofar sashensa, juyowa yay ya amshi kayansa a hannun aunty Nurse yana musu alamar sai da safe da hannu.
    Basu ja zancenba suka juya shi kuma ya murɗa ƙofar ya shiga da sallama a ƙasan maƙoshi.
    Sosai ƙamshin turaren da aka saka ya tasiri a ransa, ya shaƙa ya lumshe idanunsa tare da takawa cikin falon sosai ya ajiye kayan hannunsa a kujerar farko.
     Babbar rigarsa ya zare, ya bar ƴar ciki kawai da wandon, dama hular a hannu ya shigo da kayansa, hannayensa duka yasa a ƙugu yana bin ko ina na falon da kallo, komai ya masa ƙyau tamkar shiya zaɓa, ya sauke idanunsa akan ƙofar bedroom ɗinsa yana ƙiyasta yanda zasu kwashe da ƙwailarsa (Ummu team bani na faɗaba Yaa Amaan ne kuma????????⛹????‍♀️).
             A hankali ya taka zuwa ga ƙofar, ya kama handle ɗin ya murɗa sai yaji gam a lamar a kulle take. Wani lallausan murmushi ya suɓuce masa yana girgiza kansa da kai hannu ya shafi girarsa. Hannunsa ya janye daga handle ɗin ya zubasu a aljihu gaba ɗaya, tsaye yay ya zubama ƙofar ido yana nazari. tsawon mintuna uku kafin ya sauke numfashi ya tako zuwa cikin falon.
        Zamansa yay cikin kujera kawai ya maida kansa ya jingina tare da lumshe idanusa ya faɗa duniyar tunani. Shi kansa bai san iya adadin lokacin daya ɗauka a haka ba, har aka kashe Gen… Saboda wuta da aka maido.

       Ummukulsoom kam tunda ta kulle ɗakin saita cire kayanta ta canja dana barci, dan a ganinta hankalinta kwance zatai barcinta ita kaɗai a ɗakin.
      Bayi ta shiga taɗanyi uzurinta, komai an kuma canjasa saɓanin sanda aka kawota da farko, bayan ta kammala ta fito.
    Gadon ta haye kewar bily na dawo mata sabuwa fil a zuciya, tsawon shekara shida basu taɓa rabuwa ba, duk inda ɗaya tasaka ƙafa ɗaya na tare da ita, sai gashi yau zasu kwana mabanbanta gidaje, bayan suna a cikin gari ɗaya. Ta share hawayen fuskarta tana gyara kwanciya, sama-sama tai addu’ar barci ta ɗora tunaninta daga inda ta tsaya.
          
        Amaan ya buɗe lumsassun idanunsa jin agogon dake falon ya buga ƙarfe ɗaya, iskar daya zuƙa ya turo ta bakinsa da hanci, kafin ya miƙe cike da takun dake nuna gajiya da kasala tattare dashi, harma da ƴar yunwa.
   Dani ya fara zuwa ya buɗe kwanikan dake wajen duka, gasashshen namane mai romo a kula, sai abinci da akaima dahuwa ta musamman, duk haɗuwar abincinnan bazai yuwu yacisa ba, dan dare yaja, ko yaci takura masa zaiyi. Maidawa yay ya rufe ya sakko daga ɗan tudun dani ɗin ya nufi ƴar durowar dake gaban tv, keys ya ɗakko aciki, da alama dai Ummukulsoom tayi bonono rufe ɗaki da ɓarawo????????.
      Sai da ya ɗauki lap-top ɗinsa da babbar riga da hula a hannu sannan ya nufi ƙofar ɗakin ya zura key ɗin, cikin sa’a kuwa ya shiga alamun ta zare wanda ta kulle da shi. Ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke tare da murɗewa….

      Da sauri Ummukulsoom da barci ya fara figarta ta buɗe ido jin ana taɓa ƙofa, tashinta zaune jiki na rawa yay dai-dai da shigowar Amaan cikin ɗakin, maida ƙofar yay ya  kulle kafin ya cigaba da takowa idonsa a kanta yana haɗiye murmushin dake neman kufce masa da ƙyar ganin yanda ta tsaya tamkar wata status tana kallonsa.
    Basarwa yay ya ajiye kayan hannunsa gaba ɗaya kan gadon ya zauna a bakin gadon shima. Takalminsa ya hau ƙoƙarin cirewa ba tareda ya ma nuna yasan da ita a ɗakinba, sai da ya gama tsaf sannan ya juyo ya kalleta gira a ɗage, sam fuskar babu walwala tamkar kullum, amma ƙasan ransa cike yake da farin cikin wannan ranar mai cike da tarihin da bazai mantaba.
      “Na miki ƙyau ne ƴammata?”
     Harara ta zuba masa tana ɗauke kai. Shima ya ɗauke nasan kan yana faɗin, “Bandama ƙarfin hali mai fada da masarautarsa har a nuna masa ƙofar da zai shiga?”.
      Sharesa tai ta fara yunƙurin sauka a gadon, baice mata uffanba, sai ma ya miƙe hankali kwance ya hau cire botirran gaban rigarsa ƴar ciki, tsaye Ummukulsoom tayi tana jiran ya matsa ta ɗauki key dake bedside drawer ɗin dake gefensa bayan ta ɗauki hijjab ta saka akan kayan barcin jikinta duk dama masu kaurine , kuma basu kama mata jikiba balle fidda mata tsiraici.
      Fahimtar hakan da yayne yasashi shareta ya cire rigarsa, ya zam daga shi sai dogon wandon da bes ɗinsa faɗa ƙal.
    Ƙin kallonsa tai, saima ƙunƙuni take a ranta wai wannan ai iskancine.
   Baisan tanayiba, ya kwashi key ɗin data ajiye da wanda shi ya shigo dasu ya nufi bathroom ɗin batare daya tanka mata dinba balle kallon inda take.
     “Nikam bazan kwana da ƙato ɗaki ɗaya ba, ka bani key na fita sashensu Momcy”.
     Saida ya kama Handle ɗin ƙofar toilet ɗin sannan ya juyo fuska a matuƙar ɗaure, da hannu ya nuna mata hanya alamar taje mana, yay shigewarsa.
    Takaici ya kume Ummukulsoom, ko motsawa a wajen kasa yi tayi, yaufa za’ayita kenan, dan koma mi zaiyi yayi ya gama bazata kwana a ɗaki ɗaya da shi ba…..
     Tana wajen tsaye tajiyo motsin ruwa alamar wankama yakeyi, ta harari bayin ta koma gaban mirror ɗinsa dake cike da turare da mayuka da kayan dai tsaftar jiki kala-kala, stool ɗin ta janyo ta zauna zaman jiran fitowarsa.
     Baifi mintuna ashirin ba ya fito.
    Ɗago kai Ummukulsoom tayi da hanzari ta kallesa, cikin azama ta janye idanunta saboda daga shi sai towel yellow ya fito, sai ƙarami a hannunsa yana goge kansa da bawani gashin kirki, dan askewa da yakeyi saboda yanayin aikinsa.
        Murmushin mugunta yayi, ya tako zuwa wajen mirror ɗin, gabanta ya tsaya yana kallonsu shi da ita ta cikin madubin tsawon seconds goma sha biyar kafin ya janye idanunsa ya matsa sosai gaban madubin ya ɗauki abinda zai ɗauka ya bar wajen.
     Sam batai zaton zai iya yunƙurin shiryawa a ɗakinba a gabanta, sai taga ya nufi drawer ɗinsa hankali kwance ya ciro kayan barci masu taushi farare tas.
     A saman gado ya ɗorasu, ya rufe durowar ya koma bakin gadon ya zauna ya ɗauki mai yana shafawa.
    Sosai kunya ta lulluɓe Ummu da mamakinsa, ga barci na fisgarta saboda hayaniyar biki ta kwana uku.
    Kanta ta ɗora saman madubin yanda bazata gansaba. ya kalleta kawai yana ɗaukar kayansa ya hau sakawa hankali kwance. Harya gama ya dawo gaban mirror ɗin ya ɗau turare ya fesa bata motsaba, gaba ɗaya ji take ta gama takura, yau kam taga ƙarshen rashin kunyar gayen nan.
     Wata kujera dake gefe ya jawo ya zauna kusa da ita, ya ɗora hannunsa a kan bayanta.
    Gabanta ne ya faɗi, dan haka ta ɗago ta kallesa da sauri, ganin yanda ya shige mata sosai ta ɓata fuska tare da yunƙurin miƙewa. Cikin sa’a ya jawota gaba ɗayanta ta zauna bisa cinyarsa, ram yay mata yanda bazata taɓa iya motsin kirki ba ma balle yunƙurin tashi.
     “Fushin da jan ajin ya isa hakanan mana matata”.
    Hararar da ta ruɗa dukkan kuzarinsa ta zuba masa, harga ALLAH inta hararesa yana tasiri a jikinsa fiye da zatonta. Lumshe idanunsa yayi ya buɗe a kanta yana jan numfashi da ƙyar da haɗiye busashshen yawun daya daskare masa a maƙoshi, dama tun jin jikinta da yay a jikinsa sosai jijiyoyin jikinsa suka saki……
       “Kariga da kayi saken da bazaka taɓa daina ganin wannan fushin a fuskar Ummukulsoom ba, Abubuwa uku idan sun tafi ba su dawowa: Magana da lokaci da mutunci. Mutane iri uku ne: Wasu kamar guba suke, gudunsu akeyi. Wasu kamar magani suke, akai akai ake nemansu. Wasu kamar abinci suke, a kullum dole ne a nemesu. Yi ƙoƙari ka zama wanda a kullum ake neman sa saboda amfaninsa”.
      A hankali ya kuma lumshe idanunsa tare da manneta da ƙirjinsa sosai, kalamanta na shiga kowanne kafa ta jinin jikinsa, yasan maganace ta faɗa masa cikin hikima, a hankali yakai bakinsa kan kunnenta yace, “Ba ka sanin daɗin lafiya sai idan ciwo ya sameka. Ba za ka san daɗin zaman lafiya ba sai ka gamu da tashin hankali. Ana sanin daɗin haɗuwa ne idan rabuwa ta zo Ummukulsoommm”.
      Yanda yaja sunan natane a cikin kunnenta ya tilastata sake cusa kanta ƙirjinsa, dan gaba ɗaya tsigar jikinta ta tashi, a tare suka sauke ajiyar zuciya, ya sassauta mata riƙon dayay mata alamar ya bata damar tashi.
    Da sauri ta yunƙura ta sauka, sosai maganganunsa suka bata mamaki, kenan yana nufin tun bayan rabuwarsu ya damu da ita komi?. Kallonsa ta ɗanyi taga shima ita yake kallo, tai azamar janye idanunta zuwa wani wajen.
     Kaɗan ya sauke numfashi yana tasowa shima, hannunta ya kama ya kaita saman gadon ya zaunar, kafin ya kama kafaɗunta gaba ɗaya ya kwantar da ita.
      Ita dai kallonsa take kawai ta kasan ido duk sai kuma jikinta yaɗanyi sanyi, bai sake cewa komaiba ya fara mata addu’ar barci, sai da ya kammala tsaf ya tofa mata tare da jan bargo yaɗan lulluɓa mata zuwa ƙirji, ya zame mata hijjabin jikinta. Duk yanda taso hanashi sai ta kasa hakan, dan wani kwarjini taga ya mata fiye da zatonta, shi kansa wani girma ta ƙara a idonsa da mutunci, baiyi zaton tanada sauƙin kai irin haka ba, dan harga ALLAH ya ɗauka yau bazama ta barsu su rintsa ba saboda tanadin rashin mutuncin datai masa. ya kuma yarda duk ɗan gaske baya yarda tarbiyyar gidansu da mutuntakar musulinci. Kansa ya duƙo ya bata sunba akan laɓɓanta daketa motsi alamar sonyin magana amma ta kasa, ya sumbaci goshinta sannan yayo ƙasa inda bata taɓa zatoba nanma ya sumbata. 
    Sosai ta waro idanu waje saboda matuƙar mamakinsa, ya sakar mata lallausan murmushin daya kusa sumar da ita a wajen. Ai babu shiri taja bargon ta rufe har fuskarta tana juya masa baya.
      Miƙewa yay yana cigaba da murmushinsa, ya zagaya ta can ɗayan gefen ya kwanta yana tunanin yanda zai iya kwanciya bashi kaɗaiba a ɗakin, ya riga da ya saba da kwanciyarsa shi kaɗai babu motsin kowa, harga ALLAH jinsa yake duk a takure, to amma ya zaiyi, yana buƙatar matarsa kusa dashi fiye da komai a halin yanzun.
     Harya kammala addu’arsa ya gyara kwanciya Ummu bata sake motsawa ba, addu’a dai take a ranta ALLAH yasa ba a ɗakin zai kwana ba, sai dai jin ya kwanta bayanta tasan addu’arta bata karɓu ba kenan.
     Abinda ya sata samun nutsuwa dashi sam bashi da wani rawar kai irinna angunan wannan zamanin da suke nuna kamar jikin macen ne mafi kwaɗaituwa a garesu, banda wannan sunbatar tata da yay a ƙirji yanzu bai taɓa kai hannunsa wani sashe na jikinta ba koda wasa, tasan kuma bawai dan baya buƙatar baneba, kawai dai shi komai nasa na nutsuwa ne da dattako.
     Tun tana fargabar ko zai far mata har taji ya fara sauke numfashi a hankali alamun barci yama fara tafiya da shi kenan.
    Itama dama barcin takeji, tsabar tsorone ya hanata yi, gashi dare yaja kusan 2:15am na dare, cikin ɗar-ɗar dai itama barcin yay gaba da ita.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡    

    Da asuba shine ya fara farkawa, ya buɗe idanunsa a hankali ya sauke akan fuskar Ummukulsoom data juyo tana fuskantarsa yanzu ba tare data saniba, sai dai tana a inda take alamun batada mirgine-mirgine wajen barci.
    Fuskarta tayi fayau tamkar tana murmushi, ƙyaƙykyawace mai yawan kwarjini da cikar haiba, komai nata yana da ɗaukar hankali musamman murjajjen jikinta da sam babu rama a tare da ita, luuu yay da idanu ya kuma buɗewa a kanta tare da kai hannunsa ya shafi laɓɓanta da babban ɗan yatsansa.
    Yanda ya keyinne ya saka Ummukulsoom kawo hannu cikin barci ta riƙe nasa tare da rungume hannun a ƙirjinta tana gyara kwanciya.
     Idanu ya tsura mata yanajin fitar murmushi a ƙasan zuciyarsa, sai dai sam babu akan fuskarsa, bai janye hannun nasa ba kamar yanda bai iya janye idanunsa da suka ƙara girma saboda barci daga kanta ba.
    Kuma motsawa tayi sai taji ƙamshin turarensa ya yawaita a hancinta, hakan ya tilasta ta buɗe idanunta dake cike da barci dan ta manta a inda take gaba ɗaya.
         Idanun Ummukulsoom kan bada wani yanayi na musamman a lokacin data tashi a barci, cikinsu yaɗanyi jaa su kumburo daga waje, ta buɗesu da ƙyar a kansa saita jasu suka koma tamkar zata lumshe ta sake buɗewa da azama ganin namiji a kusa da ita sabanin Bily da tasaba gani.
    Tuni Amaan yayi doguwar shiɗewa akan wannan salo na Ummu da sam ba yanga bace ko ɗaukar hankali.
    Saurin ture hannunsa tayi ta juya bayanta tana dafe ƙirjinta ta sauke numfashi.
     Shima ajiyar zuciya ya sauke ya yunƙura ya tashi da ƙyar dan jikinsa ya masa nauyi sosai alamun barcin bai ishesa ba. Bai ce da ita komaiba ya nufi bayi ɗaura alwala.
     Koda ya fito baiyi mata magana ba, dan yasan idonta biyu, ya ɗau jallabiya ya saka bayan ya zare kayan barcinsa sannan ya fice.
       Ummu tai ajiyar zuciya tana mamakin kanta, sai kace Amaan yazo mata da wani asiri, koda yake duk fa sonta da bashi laifi inhar zata tuna a zamansu na baya bai taɓa cutar da itaba, harkarta ce kawai baya shiga, sakin da yay mata da kausasan kalamansa ne kawai suka kasa barin ranta, *_ƙwaila mara zurfin ilimi…,_* wannan kalaman sune mafi ciwo da take ganin da wahala ta iya mantasu harta bama Amaan kanta da rayuwarta yanda kowacce mace kanyi a gidan mijinta……
   Jin an ƙwala kiran sallar shiga massalaci yasata tashi itama tai alwala domin gabatar da salla.

     Tana zaune bayan idar da salla ya shigo, sallama kawai yay ta amsa, daga haka babu wanda ya kuma tankama ɗan uwansa, ya ɗauki kayansa na trianing ya shiga bayi, mintuna kaɗan ya fito, a bakin gado ya zauna yana ƙoƙarin ɗaura igiyar takalmansa.
     “Ina kwana” Ummu ta faɗa cikin kauda kai gefe.
      Bai amsa ba ya cigaba da ɗaura takalman, tasan kuma sarai ya jita, juyowa tai ta kallesa cike da takaici, hakan yay dai-dai da miƙewarsa suka haɗa ido, fuskar dai tana a yanda ta santa a tamke, zuwa yanzu hakan baya damunta dan shi da Dad ta gama sallama muskilancinsu…….
     Wani ɗan tsigunnon da yay a gabanta na gayune ya dawo da ita hayyacinta, kuncinta ya sumbata cikin lumshe ido da buɗewa yana faɗin, “Amincin ALLAH ya tabbata ga zuciyar da bata fushi Matar Ajiwa”. Ya ƙare da busa mata iska a kan fuska wadda ta tilasta mata kallonsa.
    Ido ɗaya ya kashe mata yana mikewa ya fice abinsa ba tare daya damu da rashin amsawarta ba.
    Ta daɗe tana kallon ƙofar tamkar zata sake ganinsa a wajen, “Amaan” ta faɗa akan laɓɓanta ba tareda tasan dalilin ambaton sunan nasa ba. Har yanzu akwai barci a idonta, dan haka ta miƙe ta koma kan gadon ta kwanta zuciyarta na tunano mata Bilyn ta, ko yaya ta tashi itama? Oho.
    Babu jimawa barci ya kwasheta.

       Sai da gari yay haske sosai Amaan ya dawo gidan, a tsakar gida ya iske Dad zaune akan farar kujera yana duba wani littafi na addini, ga Coffee da aka haɗa masa ajiye a copy table ɗin da ke gabansa.
        Ƙarasowa Amaan yayi inda Dad yake, ya zauna kan ɗan dakalin da aka zagaye flowers ɗin gidan dashi yana faɗin “Barka da safiya Dad”.
    Kallonsa Dad yayi fuskarsa kadaran kada han yace, “Barka dai Fodio, yaya ɗiyata?”.
     Moso yaɗanyi kaɗan yana ƙara jinjina irin son da Dad kema Ummukulsoom, ya amsa da cewa, “Lafiya lau Dad”.
     “To Alhmdllh” Dad ya faɗa yana ɗaukar mug ɗin Coffee ɗinsa yakai baki.
    Buhayyah data ƙaraso ɗauke da gorar ruwa a kan karamin tire da kofi ta ajiye a table din tana gaida Amaan.
    Sau ɗaya ya amsa ya ɗauke kai, sai da yaga zata bar wajen yace, “K kawo min cup”.
     “To yaya” ta amsa da girmamawa.
    Babu bata lokaci ta dawo wajen, sanin Coffee zaisha ya sata ba tare da tama tambayesa ba ta duƙa ta haɗa masa.
    Amsa yay ita kuma ta bar wajen, yana sha suna ƴar maganar data shafesu shi da Dad, ya daɗe bai samu irin wannan damarba ga Dad tun bayan rabuwarsu da Ummukulsoom, shiyyasa sai yaji sam bayason tashi ya barsa. Shi kansa Dad zaman nasu yana sakashi shauƙi da nishaɗi, yanason Fodio, sai dai shi yana dannewa ne saɓanin Momcy data gaza.
       Anan Momcy ta fito ta samesu, gaisawa sukai da Amaan itama tana tambayar Ummukulsoom da gajiyar biki.
      Ya amsa yana maijin nauyin iyayen nasa.
    “Fodio tashi kaje ciki baka ganin lokaci yaja kabar min yarinya ita kaɗai”.
        Miƙewa yay tare da sakin guntun murmushi jin furucin Dad ɗin nasa.
       Momcy ma murmushi tayi.

        Falon tsaf alamun an gyarashi, duk zatonsa Ummukulsoom ce ma shi, bedroom ɗin ya nufa, ya murɗa ƙofar ahankali ya shiga, tana kwance abinta tana shan barci, ya taka zuwa gaban gadon, kallon kusan mintuna biyu yay mata ya bar wajen zuwa bayi, baya gajiya da kallon ko kaɗan.
     Harya fito daga wankan Ummukulsoom bata tashiba, shiryawa yay cikin ƙananun kaya marasa nauyi ya fito falo ba tare da ya tasheta ba, dan ya lura tanajin daɗin barcin sosai……….✍????

_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863


*_ƴan Niger kuma_*

_ZAKU BIYA NE DA KATIN;_
*_MTN ko MOOV_*

*Novel 1 Naira 200 = 350fc,*
*Novel 2 Naira 300 = 500fc*
*Novel 3 Naira 350 = 550fc*
*Novel 4 Naira 450 = 750fc*
*Novel 5 Naira 500 = 850fc*

 _TA NUMBER;_
 *+22795166177*   


Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button