
watansu biyu da haduwa ya sanarwa danginsa ya samu mata,sune suka tallafa akayi masa komai cikin talauci sosai akayi bikin,yan unguwar haka suka dinga surutu Amadu ya auri balarabiya yar gudun hijira ba a San asalinta ba etc,cikin bakin talauci na karshe suke Zaune lfy sai uwar soyayya da suke zubawa.
Sun kwashe kimanin shekaru goma sha biyar tare amma basu samu haihuwa ba, tun suna sa rai har suka hakura gashi basu da kudin zuwa asibiti ko maganin gargajiya haka suke ta addua.
Saudat sarkin hakuri, watarana tana zaune makociyarsu ta shigo tare da kawo mata Maganin sanyi Infection na gargajiya, tace Saudatu ga maganin sanyi ba a son mace ta zauna Bata shan maganin sanyi lokaci zuwa lokaci,Godiya tayi tare da karba,wata uku tayi tana amfani da maganin cikin ikon Allah sai ga Saudat da ciki murna ba a magana,har cikin ya cika wata tara ta haifi danta namiji kato kyakyawan gaske ajin karshe,ko ina zuwa akeyi kallon jaririn Sabo da kyansa,ranar suna yaro yaci suna Ahleef,Ko hakikar suna ba a yanka masa ba Sabo da talauci,bayan wata uku da haihuwa talauci ya kara zurfafa musu sai kawai sukayi shawara cewar gwara su koma Nigeria da zama garin kasuwanci ko Allah zai sa su samu aikin yi,basu tsaya ko ina ba sai Nigeria Cikin Kaduna state.
Cikin ikon Allah wani hamshakin me kudi ya dauki Amadu gadi a bakin gate tare da bashi daki da toilet a gidan yace ya kawo iyalinsa su zauna tare,Zama yayi zama Sun kusa shekara lokacin watan Ahleef bakwai Me kudin ya biyawa Saudatu da Amadu aikin hajji tare da jaririnsu,sannan ya siya musu katon rago aka yankawa jariri Ahleef na Hakika, bayan sun Dawo da wata biyu lokacin Ahleef ya cika 1yrs Allah yayiwa me gidan da suke aiki rasuwa,bayan rabon gado gidan ya tarwatse Gaba daya yaran Alhaji suka koresu gida ya zama na gado, Shine silar barin gidan gaba daya basu San inda suka nufa ba,ruwa,iska,rana sanyi duk ya kare a kansu har Allah yasa wani mutumi ya gansu ya tausaya ya basu wani dan karamin daki dake a kofar gida kamar na maza,anan suka raba suna zama, Ahj Amadu ya koma dako a kasuwa ita kuma tana wanki da guga.
watarana ta bar Ahleef a Daki ta shiga wani gida karbo ashana zata hura wuta a waje ma suke girki kowa a titi yana kallonsu,kuma bandaki daya suke shiga da wasu kartin maza samari hakan ma tausaya musu sukayi ganin basu da inda zasu shiga idan shiga bayi ya kamasu,Allah yasa Saudat me tsananin tsafta ce kullum toilet din samarin a wanke kal ita take wanke musu kuma suna jin dadi.
Tana shiga karbo ashana ashe wasu samari masu satar yara suna siyarwa matsafa suna fakonta a unguwar su biyu,jira dama suke su samu dama, Ranar ba kowa a layin kawai suka fada dakin tare da fesawa yaron Powder ta bacci suka sakashi cikin towel tare da fita da gudu suka fada motarsu sai birnin tarayya Abuja dama abinda ya kawosu Unguwar kenan.
Saudat tana fitowa neman duniya Bata ga Ahleef ba haka ta haukace Ko ina tana tambaya mutane Sun tausaya mata,Shi kanshi Amadu Kuka wiwi ya dinga yi da yaji cewar dansa da suka fi so a duniya an sace shi, Kullum cikin kunci suke gashi Saudat ta nace ita tasan danta yana raye,kuma idan an sace yara Kudu ake kaisu dan haka ita wai dole sai Sun bar arewa,haka ya lallabata ta hakura har suka kara samun wani ya dauki Amadu yake kula da flowers na gidansa,part guda ya basu suke zama lfy, har suka kwashe shekaru ashirin da biyar a gidan,Sai me gidan ya fara neman Saudatu yana so yayi lalata da ita ganinta kyakyawar gaske tafi matarsa,Amadu yana Jin labari ba yanda Amadu ya iya haka ya kwashi matarsa har zuwa Abuja City, Cikin sa’a kwanansu uku da zuwa suka samu wani attajiri Alhaji Dauda ya daukesu aikin gadi a gidansa, ita kuma Saudat zata dinga yiwa yaransu wanki, kaf iyalan Alhaji Dauda basu da tarbiya bare mutunci,shi kadai ne me dama dama, boysquaters ya basu a nan suke zaune,cin mutunci iri iri ake musu a gidan haka suke hakuri,ganin haka yasa Saudat ta fara Soya doya da kwai a bakin wata yar kasuwa kusa da wani katon mall na kece raini,Idan tayi wankin da takeyi da yamma sai ta tafi wajen sana’ar soya doyarta,dake ta iya sai take samun kudi sosai har masu kudi suna tsayawa su siya Sabo da tayi mugun iyawa kalarta daban ce kowa yaci sai ya kara,ta tsare mutuncinta normal.
Rayuwa kullum ja take dake dama basu samu haihuwa da wuri ba,Har aka kwashe shekaru 5yrs yanzu kenan yayinda Idan An hada da shekarun tun haihuwar Ahleef shekaru 31 kenan,har yau dansu Ahleef na ransu suna fatan ganinsa nan gaba, yanzu Idan kaga Ahleef kaga iyayensa baza kace su suka haifeshi ba, Sabo da Sun tsunfa Sun manyanta sai ka rantse kakaninsa ne tunda dama sai da suka manyanta sannan suka samu haihuwa,gasu kuma kullum a wahala suke da gwagwarmayar rayuwa shiko Ahleef yana cikin daula.
Bayan barayin Sun sace Ahleef suna ta sheka gudu a hanyar Abuja sojoji suna tsaida motoci ana dubawa Cikin sa’a aka kamasu tare da fito dasu su biyu daga motar,jaririn yana hannunsu suka fara dukan barayi tare da tambaya ina suka samoshi,Daya cikinsu sojojin yana rubuta komai a littafi,Cikin barayin suka ce wlh satoshi mukayi dama sana’ar muce mu Sato yara muna siyarwa da Matsafa, Wannan yaron ma sunansa Ahleef mun dade muna bibiyarsu har muka samu nasara,sunan yaron Ahleef min San iyayensa….kafin y’a karasa daya abokin satarsa ya rada masa Mu gudu fa daji,ba tare da tunani ba suka arce da uban gudu da niyyar su boye a daji,Sojoji suka fara Harbinsu ta ko ina nan take duk suka zube kasa matattu.
Bayan komai ya kammala suka dauki Jariri da sa hannun Gomnati aka fara cigiyar iyayensa a kafafe na Media Amma ba a dace ba yaro Ahleef har ya kwashe 1mnth a gidan raino.
Abba Alhaji Sulaiman Yahaya da Matarsa Hajiya Amina Momee Asalin yan Nasarawa lafiya ne gaba daya har Momee danginsu Suna can duk da cewa suna zumunci sosai da danginsu duk da cewa iyayensu Sun rasu tuni dama amma Momee Babanta yana raye can garinsu,suna yawan kai masa ziyara tunda sunyi sunyi ya dawo Abuja yaki.
Momee da Abba mutanen kirki ne masu hakuri ga tausayi,tunda sukayi aure Allah bai basu haihuwa ba har suka kwashe 8yrs haka,shine Momee ta bawa Abba shawara yaron Ahleef da suka gani a tv ana neman iyayensa ba a samu ba ita tana so suje ta karbi rainonsa yaron ya Bata tausayi gashi kuma Allah bai Bata Haihuwa ba, nan Abba ya Amince da sa hannun Gomnati aka basu yaro tunda anyi cigiya a Media iri iri amma Allah bai sa an samu iyayen jariri Ahleef ba.
Su Momee
Cikin so da Gata hade da Amana suka rike Ahleef,Momee bayan Ahleef ya cika shekara 6. Momee ta samu ciki ta haifi yarta Niima kyakyawa,Ahleef lokacin yana primary schl ta masu kudi,bayan 3yrs Momee ta Haifi yan biyu Salman da Suhail,Ahleef secondary schl da university gaba daya a London yayi su, cikin gata ya karanta Harkar kasuwanci har sai da ya gama Masters ya dawo Nigeria,Lokacin Sun shaku da Niima tana University amma a Nigeria tayi,Ita kuma Niima Bata wani son Ahleef Sabo da gani takeyi iyayenta sunfi sonsa kuma ba su suka haifeshi ba, sai take kishi da bakin ciki Sabo da Momee tafi sonsa Abba ma haka,su kuwa su Salman ba ruwansu suna kaunarsa kamar dan uwansu na jini,Dama tun Ahleef yana yaro su Momee basu boye masa ba yasan komai shi ba dansu bane.
Bayan Shekaru masu yawa Momee ta haifi autarta Latifa wacce yanzu take 14 to 15yrs,Ahleef yana gama secondary schl Abba ya bashi jari da Company har biyu kyauta tare da sa hannun lauyoyi da yan uwansa Sabo da halin rayuwa tunda yasan Bashi da gadonsa shi yasa ya bashi tun yana da rai.
yana juya Kudin da kula da Companies Kafin kace me sai ga Allah ya bunkasa abin ya zama Me dukiya na sosai yayi suna a duniya har yafi Daddy ma kudin,suma su Salman suna fara university aka basu nasu harkar,Niima ma haka,Momee ma haka,kowa a gidan da nasa na kansa yake amfani babu Wanda ya dogara da na wani sai Latifa yarinya,Duk gidan yan boko ne Abba kuwa dan Boko ne dan kasuwa kuma dan siyasa Wanda ya rike mukamai da dama manya yanzu haka shine Sakataran Gomnati na kasa baki daya,gidane Na Tarbiya basu da wata matsala har soyayya tayi zafi tsakanin Ahleef da Niima wacce ake tunanin aurensu kwanan nan.
Ahleef Yana da addini ga ilmi,bashi da wata matsala sai watarana yana da raini sama sama,ga Gadara da takama kuma yana fama da iyayi etc bashi da abokin da ya wuce Farhan,Farhan shima namiji ne kyakyawa halayyarsu daya da Ahleef yana da haske amma ba can ba,yafi Ahleef fara’a kawai,tun suna yara tare suka taso iyayensu masu kudi ne suma su Farhan, amma shi Lawyer ne.