JIN DADI SABONOVELS

JIN DADI SABO COMPLETE

JIN DADI SABO COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda Shukura taji ya ambaci gidan Momee sai ta hade Rai tare da Shagwabe fuska zatayi kuka tunaninta kawai Niima da Ahleef zasu hadu, Yaya dai Honey ko Zaki je muje tare da sauri tace ae zanje a tafi Dani,a ransa yake ta dariya yasan kishi ne kawai yake damun Shukura,da sauri ta haura sama kamar walkiya tayi wanka sharp sharp,Mai ma hannu da kafafu kawai ta shafa sannan ta dankara wani material me arnen tsada da kyau black and white,takalmi da Jakarta harda mayafi ma same color,powder ta shafa da Dan jambaki ta zizira kwalli a idonta abinka da me kyau sai gata ta fito wani das tana kamshi.

Mamaki Ahleef yayi abinda Shukura sai ta Dade Bata Gama shiri ba Amma yanzu gata 30mnt ta shirya ta fito,hannunta ya rike Yana Wasa dasu tayi Masa kyau matuka, Yar Jakarta ya karba ya rike Mata hannu suka fita,yau ba ruwansu da Driver ko escort shi zaiyi Driving da kansa.

Sai da ya bude mota da kansa ta Shiga sannan shima ya Shiga yaja suka bar gidan,Basu tsaya ba sai Gidan Farhan,Fatima na bude kofa taga Kawarta Shukura da matukar murna ta rungumeta kamar zasu Fadi,Ahleef yace yi min a hankali da ita pls karta Fadi ki jawo min,Dariya Fatima tayi kadan tace ayi Hakuri sannan suka zauna, gaba daya Shukura da Fatima suna zaune a 2seater.

Farhan ne ya fito daga kitchen dauke da plate da cup a hannunsa,Bai San ma Sunyi Baki ba,Yana fitowa yasha mamakin ganin Ahleef da Shukura, Ahleef yace to rufe bakin Yar talatuwa Kai Mata abincinta sai ki dawo,Dariya Farhan ya Shiga yi wlh baka da mutunci nice ma talatuwa din? to ba nata bane nawa ne bare kace, Shukura tace an dai kamaka zaka waske,Fatima tayi Murmushi tana Jin kunya tace to idan ma nawa ne Ina ruwanku Wai,Kuma ma mene a ciki,

Farhan dai da Yar jallabiyarsa tsangalalliya irin ta sabon Ango Yana hutawa ya zauna kusa da Ahleef suka tafa sannan suka tsunduma hirar duniya,Shukura Suma suna tasu Bayan Fatima ta kawo musu kayan ci da Sha,Gaskiya gidan Farhan ma ya Hadu karshe, Shukura ta zunguri Fatima suka tashi tsam sukayi Bedroom din Fatima tare da zubewa bakin Bed,Fatima ta kalli Shukura tace Shukura wlh ki yarda da maganata ciki ne dake kamar,Shukura tace ke bani da komai fa mutane ke ganin Haka,Gashi dun kin Kara fari da kiba komai naki ya karu,tabe Baki Shukura tayi tace Jin dadine kawai ki yarda Allah,kin San Hero na Yana ji dani.

Yanzu to tsuminki Zaki bani ko ki koya min mazan Nan naci garesu Farhan baya Bari ina Hutawa ko yaushe cikin yi yake,Murmushi Shukura tayi irin tsohon hannun Nan tace Zaki Saba ne yarinya Ni banga qbin naci da damuwa ba wannan abin dadi Haka to Ni wlh watarana Nike jajibo kayana yanzu idan ba ayi ba kullum bana Jin dadin duniya, Fatima ta bude Baki tace ke ko Harija ce to wannan jaraba haka, Ni bana so wlh,Shukura tace tab zauna Ni yanzu tafiyar kwana daya bazan iya ba gwara Ina kusa dashi,Ni Umma ke hada min Amma tana koya min wasu ma Ina yi da kaina,Bari zan koya Miki on WhatsApp sai Kuma zansa Umma ta Miki naki kema sai ki Aiko a karbar Miki Amma karki Bari ya gane kina yi, Fatima tace ai bazai sani ba dama hauka nake, Shukura tace harfa na maza Ana hada musu idan kina so kiji mijinki zam zam shima kina bashi kalar nasu na maza da Kuma na yayan itatuwa ingantattu,ba kawai kiyi ta gyara kanki ba shi kuma mijinki ba cikakkiyar lfy sai ku cutu,idan baya gamsar dake ma Zaki iya dinga hada Masa wasu fruits juice da abun sai ya shanye Bai sani ba ai idan sau goma kike a Rana shi zai iya dake, dariya Fatima tayi ke Dan ubanki Ina kika San salo haka? Umma ce wlh take nuna min hanya Amma ta dabara Ni Kuma sai na dau haske,gaskiya kinyi dacen suruka,Shukura tace aifa Kam Alhmdllh.

TV ce a room din Ana wani American film suka fara xxx a film din dama su ba kunya,Shukura tace ke kashe wannan abin karki sa yanzu na dauki Mijina mu koma gida,Fatima ta sheke da dariya tare da furta Amma maitar taki tayi yawa da gaske kikeyi,Shukura tace to mu fulani masu lfy ne,lafiyayyu ne mu,uhm naga Alama cewar Fatima.

Tare sukayi sallar Magrib su Kuma mazan suka je masallaci,Yana dawowa Ahleef yace Shukura ta fito su tafi,Fatima tace to Ni me zan Baki Shukura me kika gani kina so a gidana na Baki? Shukura tayi dariya sannan tace babu Hajiya Amarya mun wuce mu,har Mota suka raka su sannan suka dawo gida,su Kuma suka wuce gidan Momee.

Sallama sukayi a Palon Niima ce da Latifa zaune suna yiwa jaririya Wasa,tunda Niima taga Ahleef hankalinta ya tashi ta rasa ma Ina zata sa kanta sabo da murnar ganinsa,matukar so take yi Masa marar misali,Shukura ta koma jikin Ahleef kusa dashi ta makale kafin Nan suka gaisa dasu Niima faran faran,Latifa tace Bari na Kira Momee,Niima tace Shukura ya gida har yau Baki fara University ba? Cike da Shagwaba Shukura ta furta har yau nace ya kaini yaki sai sanda yaga dama,Ahleef kamar baiji su ba Yana Danna waya abinsa har Momee ta fito tana Shukura yau ma dake aka zo Ashe? Ae Momee Ina yini suka gaisa sosai har da Hira, Ahleef ma Haka,Sultan da Suhail suka shugo Ana ta hirar bikinsu ya kusa.

Niima in Banda kallon Ahleef ba abinda takeyi kamar zata Hadiye shi,Shukura tana kallonta duk abinda takeyi,hankalin Shukura duk ya tashi ta gama tsorata da Niima kamar Mayya.

Sultan yace Shukura yau lfy kike kuwa naganki so silent? Murmushin yake tayi tare da cewa lfy nake na gaji ne kawai, Murmushi Momee tayi tace tashi ku tafi gida Ahleef tunda ta gaji, kyaleta Momee sai munyi sallar Isha sai mu wuce, Shukura tana ji tayi Shuru da ita, Sultan sunje Masallaci sun dawo Suma su Shukura gaba daya Sunyi sallah ta dauki Yar Niima tana Mata Wasa Momee tace kowa yazo a ci abinci, a gidan suka ci suka Sha sannan yace tazo su tafi,kamar jira takeyi zumbur ta mike suka musu sallama suka tafi gida.

Ahleef kullum Kara kaunar Shukuransa yake yi suna zuba soyayya kamar zasu cinye juna har Allah ya kawo bikin su Suhail,an fara biki an Kare lfy ansha shagali ko wanne an Kai Masa Amaryarsa radeden gidansa da suke makwafta da juna,Ahleef da Shukura Sunyi rawar gani a bikin kusan komai Ahleef ne ya dauki nauyinsa.
Latifa Allah ya taimaketa a bikin ta samu wani Matashi cikin abokan angwaye Yousuf nutsatse shima da yayi shaye shaye Allah ya shiryeshi ya tuba Babban likita ne soyayya ta kullu tsakaninsu me karfi.

Hafcy tare da kannenta su Zahra aure suke so suyi yanzu koma waye sunce aura zasu yi,Amma Babu namijin dake neman su bare suyi auren duk sai na banza,Mama da Alhj Adamu suna ta Shiga cikin manya Akan a fitar da Mubaraq,Allah ya taimakesu Kuma wani abokin Alhj Adamu Asp ne ya Shiga case din Nan da kyar aka San yanda za ayi tunda kasar tamu cin hanci yayi yawa sai talaka ake kamawa a kulle Amma yaran masu kudi ko kisa sukayi ruwa Tasha.

Mama da Mijinta tare da su Hafcy murna sukeyi Mubaraq ya fito,gaba daya ya rame ya lalace ga uban duka da yaci sai Asibiti aka wuce dashi,Bayan komai ya lafa Mama tace Lallai ya shirya yaje yaga yarsa Khadija,mamaki,da tarin kunya suka rufe Mubaraq,Dana sani ya fara yi Yana zub da Hawaye, Mama ta mike tare da Shiga dakin Alhj Adamu daga kofar taji Muryar Mijin nata Yana waya da likitansa yace Doctor bazan iya fada Mata Ina da HIV ba,Idan taji da matsala,Doctor yace ya kamata a gwada ta idan tana dauke da ita a daura ta a magani,Wlh nayi mamakin ace Ni Alhj Adamu da Hiv,Sai da Momee ta Gama Jin komai Sannan ta banka cikin room tana kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button