
Rasa ma me zata ce tayi sabo da bacin Rai kawai ta zurma Hijab ta figi Mota sai asibitin kudi hankalinta a tashe,test din HIV akayi Mata sai ko gata dauke da cutar itama a jikinta,sai da aka gwada ta different Hospitals Kuma duk possitive ya nuna tana da cutar, Mama ta barke da kuka a asibiti cikin bainar jama’a tana kuka Ana Bata Baki da kyar wani Dattijo Babban malami ya sata a gaba da nasihohi masu ratsa jiki sannan taji sanyi a ranta har ta mike ta samu kwarin gwiwar zuwa a daurata a magani ta tafi gida. Ko data Isa gida yaranta ta Tara kaf har Mubaraq Wanda ya rame sabo da talaucin da yake ciki ya Saba rike kudi sabo da duk dukiyar dasu Momee suka bashi ya karar da ita ta hanyar safarar kwayoyi etc.
Mama tace tofa yarana duniya Dole mu dawo mu bita a sannu,mun shuka Abubuwa Marasa kyau gashi yanzu muna karbar sakamakonmu tun daga Nan duniya ku daure ku Mata kuyi aure tun muna Raye kafin lokacinmu yayi domin mu tamu ta Kare, Mubaraq Kaine Babba ka samu ka koma wajen wacce ka yaudara tare da dirka Mata ciki ka aure ta Haka tunda ta haihu ku hada kanku ku raini yarku Ni Nan da kuke gani na da gawa kuke magana tawa ta kare.
Hafcy ta fara zub da Hawaye tace Mama bamu gane gawa ba,me yake faruwa ne,Hawaye ya tsiyayowa Mama sannan tace Dole na fada muku cewar muna dauke da cutar HIV daga Ni har Babanku,ya dauko Mana cuta ya jona min, Palon ne ya rude da kuka,ba abinda kake ji sai kukan Yan Mata sun hada Kai suna rairawa,Ana Haka sai ga Alhj Adamu ya shigo ya samesu Haka,wuri ya nema shima ya zauna Yana tambaya lfy,Mama ta zuba Masa Harara sannan tace Allah ya Isa tsakanina da Kai,ka cuceni ka shafa min cuta fasiki ba abanza ba Ashe Mubaraq yayiwa wata ciki Ashe Kai ya gado algungumi,Mubaraq Wanda tsabar bacin Rai sai yanzu ya iya magana da Mama ya Isa Haka koma mene ya rigada ya faru sai yafiyar Allah data mutanen da muka zalunta kawai zamu nema.
Washe gari Niima tana zaune a Palo Me gadi ya shugo yace tazo tayi bako,Mamaki ya kamata waye Kuma Haka ta daure ta gyara kanta ta fita dauke da yarta Khadija wacce tayi wayo bulbul da ita,Mubaraq ta gani jingine jikin mota har zata juya sai ta fasa ta Karasa kawai tare da sallama,Sai kallon Khadija yakeyi da gani yarsa ce wani son yarinyar da kaunarta ya kama shi,hannu ya Mika Aiko Niima ta Mika Masa yarsa,ya dauketa Yana ta wani murna,sai da ya Gama Mata Wasa sannan ya durkusa har kasa Yana me bawa Niima hakuri akan laifin daya aikata Mata,tana Jin Sa har ya Gama, ba wani jayayya tunda itama tasan tayiwa wasu laifi Kuma sun yafe Mata kawai tace na yafe maka, wajen Momee ta rakashi.
Momee Bayan sun gaisa ya fara neman afwa, Momee ma tasan itama tayiwa wasu laifi an yafe Mata Babu ja tace na yafe maka kuma kudi ba rokar mu kayi ba Ni na kasa tunani me kyau na baka, duk hakkin Ahleef ne ya kama mu.
Mubaraq yaji dadi sosai anan yace zai auri Niima,Har Niima tace A’a Momee tace ba damuwa idan ya shirya ya tura Manyansa.
Haka kuwa akayi Bayan wasu lokuta Mubaraq ya turo Manyansa aka sa biki Nan da 3months.
Alhj Adamu ya damkawa yaransa kaf Dukiyarsa su suke juyawa su Kuma suna kula da Shan maganinsu,gaba daya gidan sun nutsu sosai Sunyi hankali,Mubaraq kuwa suna soyayyarsu da Niima yayi wani kyau da kiba abinsa, tunda Shukura taji labarin auren Niima hankalinta ya kwanta tafi kowa Murna.
Shukura ce zaune ta rike Mara tana Mata ciwo,ga Ahleef Yana Office,wayarta ta jawo a hankali tare da dannawa Ahleef Kira,Yana dagawa yaji Muryarta wata iri,da sauri yace lfy? Kuka ta fashe Masa dashi,zumbur ya mike ba tare da Bata lokaciba ya bar Office ya figi mota sai gida,Yana zuwa tun daga waje yake faman kwala Mata Kira har ciki ya isketa tana murkususu.
Shi bai taba ganinta cikin wani Hali Haka ba,daukanta yayi Yana me ya faru da ke? Me kika ci, da kyar ta furta ka kaini asibiti zan mutu,Bai jira ta Karasa ba yayi waje da ita a mota ya sata ya Shiga suka tafi da gudun tsiya, Allah ne kadai yasa Bai tafka hatsari ba don Yana tuki Yana kallon Shukura hankalinsa tashe shi yasan Bata da ciki bare yace ko shine zai zube, kukan da take Yana Kara tayar Masa da hankali,gani yake kamarfa mutuwa ma zatayi,Nan ya fara Hawaye shima har suka Isa asibiti na kudi me tsada,da kansa ya Saba Abarsa a kafada yayi ciki da ita yana Kiran Doctor, kafin kace me har an bashi daki dake na kudine ba Bata lokaci aka fara dubata cikin gaggawa, suna gwaje gwajensu aka gano Shukura na dauke da ciki har na 2mnths, doctor ya tambayeta me kika Sha? Ko kinci wani Abu? Shukura tace zobo kawai Tasha marar sugar dake dama tana yawan Sha,Doctor yace ae to shine ya Baki matsala karki Kuma Sha sai cikin yayi kwari ya Kai 7mnths sabo da Zobo marar sugar Yana wanke dirty na mahaifa idan mace ta tafasa da kaurinsa ba sugar Tasha suna Gama jimai da mijinta to zai wahala ta samu ciki sabo da zai wanko ko mene da yake Zama a mahaifa,Haka masu ciwon Mara na period ko shaaawa idan tayi karfi tana sa ciwon Mara to suna Shan Zobo ba sugar su tafasa yayi kauri Kar a tsuga Masa ruwa,Yana magun guna da yawa ga Karin jini etc.
Nan aka yiwa Shukura abinda ya Dace ta dawo normal kamar ba ita ba,ba abinda ya sata farin ciki irin yanda aka ce tana da ciki,Ahleef Yana waje Yana jira yaji result duk hankalinsa a tashe,Magunguna doctor ya rubuta musu sannan yace Shukura ta fito su tafi an sallamesu Amma Nan gaba zata Fara zuwa awo, da murna ta fito,Ahleef tunaninsa Doctor ne sai ya fara ganin Shukura ta fito Doctor Yana bayanta.
Farin ciki ya lullubeshi Likita ya Masa bayanin komai Ahleef sai da yayi sujjadar Godiya ga Allah,Yana ta murna Shukura ta samu ciki,itama Murna takeyi suka tafi sai da ya tsaya ya siyo magun gunan sannan suka wuce gida,part din su Umma yaja ta suka Shiga,Umma tana kitchen taji Shugowarsu ta fito tana cewa ku Kuma daga Ina ko anguwa zakuje? Ahleef Yana Murmushi tare da Sosa Kai yace daga asibiti muke mararta ya fara ciwo so muna zuwa Ashe ma Wai ciki ne da ita har wata biyu, Murmushin Jin dadi Umma tayi tace Alhmdllh Allah ya raba lfy,Shukura kunya ta kamata duk ta kasa sakewa. Baba ne ya fito da niyyar fita sai yaga su Ahleef a zaune suna kallo a Palon Umma, gaisawa sukayi ya zauna sukayi Yar Hira sannan ya fita, Umma bin Bayan Baba tayi a compound ta sanar Masa Shukura nada ciki,Murna ta kama Baba shima Addua ya kwarara sannan ya fita cike da farin ciki.
Shukura tana zaune ta zame tare da kwanciya saman cinyar Ahleef suna kallonsu Yana shafa gashin kanta Umma kuwa tana kitchen abinta.
Ahleef a hankali yace na kusa Zama Dad,Yana shafa cikinta,Shukura ta dago kanta suka hada Ido tayi Masa wani fari da Ido tare da kashe Masa Ido daya a hankali tace karfa Umma ta fito zamuji kunya,tashi to mu tafi part dinmu baza a takura min ba,Kafada ta make tare da cewa nakiya kamshin girkin Nan nake son Shaka Kuma so nake ta Gama naci sabo da tun yanzu shaawarsa nakeyi, Murmushi yayi to Bari na koma Office dama ban Gama abinda nakeyi ba,dariya tayi tace ai ka dawo kenan yau sai Kuma gobe idan Allah ya kaimu, cike da Murmushi yace kin Gama maidani Mijin tace ko Honey? Yatsunsa take Wasa dasu ta danyi dariya kadan, har Umma ta shirya Dining ba tace su suci ba suka koma Dining suka zuba abinsu suna Santi suna ci sai da suka ji su dam dam sannan suka tattara suka koma part dinsu tare da bude sabon shafin soyayya suna ta jiyar da juna dadi.