
Baffa ne zaune kusa da Inna yace Inna ya kamata kema ki shirya Wannan lokacin mu tafi dake sabo da tafiya ta taso min zuwa birni cikin Kano zan tafi da Shukura tayi kallo Kallo kema ya dace ki bude idonki,Tsalle Shukura ta shiga bugawa tana Murna zata je Kano wannan zai Zama zuwanta na biyu kenan Kano,tace Baffa zamu je Shopirayit wai (ShopRite) take nufi,Baffa yayi dariya yana jin dadi Shukuransa tana farin ciki yace Yar Shopirayit din bantan uba Saura muje ki damu mutanen birni,dariya sukayi gaba daya tace Ai Allah sai na tambayi yan gayu sun fada min Sunan jakin Baban gida da turanci,dama na dade ina so na tambayi sunan Jakin Baban gida da turanci ban sani ba aiko wlh wannan lokacin sai na tambayi yan Birni,Baffa yana dariya yace ai da kin bari sai munje Abuja birnin tarayya sai ki tambaya a nan ai sunfi yan gayu,sunfi ilmi ga boko,da sauri tayi tafi ai wlh Kano ma sai sun sani, kuturin uba kai kaga wasu yan gayu Inna baki gani ba yanda suke tafiya kwas kwas,baku ga wani Namiji ba Allah dana ganshi fatarsa santsinta yasin kamar na Gansa kuka sulub sulub.
Dariya sukayi gaba daya Shukura tace cab Inna kinga wani da muka gani yana cin Nama a bakin titi suna Shan lemo a tasha cikin tashar Unguwa Uku ai kadanba Sumarsu tayi Ukun takan Baba Sumar nan da kake tarawa kaima ashe Baffa kaima dan gayu ne hhh sukayi dariya,Shukura tunaninta Sumar Baffa ma ta yan gayu yake tarawa bata San irin kauyencin yan Fulani bane wacce suke tarawa duguzum ba gyara,haka kuma da taga wasu a birni a tasha yan iskan tasha ne masu sa mutane a mota amma dake na kauye daban da taga na birni sai ta gansu yan gayu ne ma bata San yan jagaliya bane hh,yan Wiwi ma kuwa,wanda kuma take cewa me santsin fata Wani ne kawai fari amma ba wani dan gayu bane kawai dai yayi dan wankansa.
Yau asabar yau tun safe suka shirya tafiya Kano Baffa an siyar da shanu za aje birni harda Kudin dan karamin Hotel da zasu kama daki daya su Uku dama haka yakeyi Su Baffa an waye.
Baffa anci rawani kamar dagaci ga Sanda katuwa,Inna kuwa duk Wanda ya ganta zai rantse mahaukaciya ce sabon Kamu a haka kuma taci gayu,Ita kuwa Shukura ansa doguwar riga Baka ta makkah katuwa da ita amma ko gyale bata yafa ba dankwali kawai ta daura a kanta sai faman kalle kalle takeyi,ana mota tuni Inna bacci ya kwasheta,Baffa ma haka,Shukura kuwa taki bacci wai kallon Hanya takeyi har aka zo kano sai da ta bawa mutanen motar dariya yanda ta zura hannunta ta window tana nuna Abu da yatsa,Inna tana bacci taji Shukura ta daketa a baya tas Inna tashi…tashi…ki Sha kallo,kin gani …laaaa….Baffa…kalli…wan can zuwan Wallahi babu wannan,na rantse da Allah ba wannan abin,ikon Allah…laaaaaaaa…kaga Baffa…. Inna…kalli katon gida,Baffa yace Shashasha Banki ne wajen ajiyar kudi,Kudine a ciki mu shiga Baffa muyi kallo,ana jin Shukura ta rafka Salati kunga tallan Sabulu,Fati Muhammad ce yar Film gata a sabulu shi yasa ta kara fari nima sai na siyi irinsa,nan ma ta kalli katon Symbol Wallahi ga Sani Danja ta karanta tace An rubuta Glo yeeee tallan layi yakeyi na waya yasin na gane.
Driver da conductor ana ta dariya har suka sauka ta cika motar ita kadai, kyan Shukura yasa duk inda suka ratsa sai hankalin alumma ya dawo kansu ana kallon kyawunta. Shukura ta gigice,ana sauka a tasha sai taga wani Zabiya fari marar kyau,duk kuda na binsa,jikinsa yayi wani rodi rodi,ga Hakoransa yellow,hanci kato muni iya muni,ta kalli Zabiya (albino) ta kara kalonsa ta sheke da dariya kowa ya fara kallonta a tashar,hankalin kowa ya dawo kanta amma ko a jikinta,tana ta dariya sai kuma ta kalli Zabiya ta rufe idonta tare da cewa wayyo…Allah ni bazan so wannan ba,Baffa ai wlh gwara a yoni baka kamar bayan tukunyar Inna akan na Zama irin wannan,ashe farin ma akwai na muni,me za aci da kai ta furta tana kallon Zabiya,jikinka kamar nama ga kuda sai Binka yakeyi,Inna tace Allah kyauta miki,yo Allah na tuba ko Aishalle karshen muni a garinmu me zatayi da kai,zabiya dai bai kulata ba,tace anji kunya ana birni ba a goge baki da Brush,kalli hakora na farare wulluuuuuu…ta ware masa hakora,ai ko aka dinga dariya ana Shan kallo sai Baffa ne ya fisgi Hannunta suka tafi tare da hawa Napep,tana shiga Napep tace ko ni sai na iya tuka wannan yar motar,jibeta yar karama,me Napep ya tsaya daukan wata katuwar mata nan Shukura ta saka rigima ita ba wanda zai shigar musu wannan katuwar ta dannemu a ciki,Baffa da Inna sabo da sai abinda Shukura tace aiko suka ce baza a dauki wata ba Shukura bata so,Me napep yace sai kun kara min kudi fa,Shukura karaf tace kaine matsiyaci kaje ruga kaga shanunmu da awaki ehe.Mai Napep ya mata banza har suka isa Hotel ya saukesu,Baffa ya shiga da kansa ya kama musu daki daya tal su Uku,Baffa yace su shigo dama Shukura ta saba tun a Hanya ta cire takalminta sabo da karta bata musu Hotel gani takeyi kamar gida Ne,Inna ma ganin Shukura tayi haka itama sai ta zare takalmanta suka fara tafiya sadaf Sadaf kamar Barayi ka rantse wani Glass suke takawa a hankali.
Inna ta Rafka magana ganin alhazawa da mata masu kudi suna Hutawa tace gafaranku dai bayin Allah, Shukura wayayya tace ke Inna nan fa Kamar Makkah ne bakya ganin wajen me kyau, nan Inna ta kwala sallama da takalminsu a hannu,shuru ba Wanda ya kulasu,Shukura tace sai kinyi kalkala Inna irin na larabawa yan gayu, Shukura ta makale murya tayi Sallama aiko mutanen wajen suka sheke da Dariya tunaninsu almajirai ne suka zo bara har Hotel, Baffa yazo ya Fara Fada haba Haba Bilki kamar baki waye ba Ashe zuwa Makkah da kuke na banza Ne,Nan suka bishi har dakin da aka Kama, Shukura tace wlh kamar a Madina Baffa ta furta tare da fadawa gado tana shan AC.
Shukura ta fara shagwaba wanka Inna Baffa wanka zanyi,Haka suka rude suna lallashinta kowa ya shiga yayi wanka tare da Sallah.
Baffa yace to Alhmdllh amma baza muci abincin nan ba yayi tsada, Karaf Shukura tace ni kosai zanci da doya da kwai, Inna tace a siyomin Biredi da fanke me sugar.
Baffa ya fita ya siyo musu shi Kuma ya siyo gurasa da kuli, Bayan sunci sun koshi sai suka bazama kallon gari,wannan haske kamar a Makkah Cewar Inna,sai cikin dare suka koma masaukinsu,Inna da Baffa a kasa sukayi shimfida,Shukura kuma ita kadai a saman Bed sabo da gata.
washe gari Baffa yaje inda zai ga mutanen da zai gani dama shine dalilin zuwansa kano,Bayan ya dawo suka kuma bazama cikin gari yawo sune har countryMall,Shukura taga kofa wacce ake turawa ta Glass sai ta fara knocking Kwan... Kwan... Salamuakaikum a bude,ku bude min,a bude.sai da Ma'aikatan suka zo suka bude Mata,bayan sun gama yawonsu kaf tare da siyayya sai kawai Baffa ya Manta sunan Hotel da Address,suna ta shan wahala a cikin napep sai Baffa yace Shukura Dan ubanki baki rike Sunan ba?ke da kike yar Boko, Inna tace wlh kuwa kai mun gaji,baki Shukura ta turo yo Kai Baffa ni ina zan sani,kaine fa ka kawo mu,me Napep yace ya gaji shi tafiya zaiyi,nan ya saukesu ya kara gaba,Su Baffa dai bakinsu Kamar zai cire sabo da tambayar Hotel, Shukura ta zabura ta tare wani me Taxi yana tsayawa tace Dan Allah tambaya nake,yace ina ji,dan Allah malam kasan wani Otel me kyau jikinsa duk fulawoyi? Da bene sannan ga kamshi,yana ta kyalli...shuru tsagal Inna tace yaro da Kwan lantarki a ciki,harda Tv,Me taxi ya fara dariya ya gansu daga daji suke yayi mamaki ma da suke zancen Hotel shi bai gane ba yayi tafiyarsa.
Su Baffa sai a gindin wata bishiya suka kwana, Gari na wayewa sai Baffa ya tuna Sunan Hotel din,nan suka shiga Napep suka Koma suna zuwa sukayi wanka suka shirya suka fito da kayansu sai Tasha, Suka shiga mota sai kauyensu suna ta murna sunzo birni sunga Gari cikin mota sai ciye ciye suke.Shukura ta damu mutane da surutu har suka isa kauyensu lfy.
Kwance yake saman cinyar Momee shima Ahleef kusan irin Shukura ne yana son sa wani aiki yana kwance yana hutawa amma shi sai dai kannensa ba Manya ko iyayensa ba, in banda tunanin masoyiyarsa Niima ba abinda yakeyi son da yakewa Niima ko rabinsa Niima bata son Ahleef haka,sabo da shakuwa da kyau ga kudi shine yasa take son Ahleef sosai ba wai tayi zurfi bane, Shi kuwa Bashi da wacce ta fita a duniya.
Niima ce ta shigo daga aiki ta Dawo ido suka hada da Ahleef masoyinta ya kashe mata ido daya tare da furta sannu kamar bazaiyi magana ba,hannu ta daga masa tana zuba masa murmushinta me tafiya da zuciyarsa,sai kallonsa takeyi a ranta Tana jinjina kyau,kyan diri da kyan sura irin na Ahleef,a ranta ta ayyana dadin da zaiyi on bed take duk da cewa bata taba bin maza ba amma Tana kwadayin Ahleef wanda shi kuwa Son Niima yake tsakani da Allah ba Dan komai nata ba.
Muryarsa taji a nutse yace 5pm ki shirya zaki rakani gidan su Farhan,ok tace Tana fari da ido.
Misalin 5 na yamma taci uban wanka kamar a saceta cikin wani lace maroon color,
Hannunsa ta rike yasha azabar kyau kamar wankin engine haka yake tafiyarsa kamar wani Gomna,hannunsu rike cike da so kamar a sace su,Bayan sunje gidansu Farhan yawo suka wuce na shakatawa,Suna zaune suna shan Ice-cream sai ga wani frnd dinsa yazo zai wuce nan Ahleef ya Mike ya tafi wajensa suna tafawa suna Hira,Niima tana latsa waya sai ga motocin Gomna zuga guda sun shigo da Alama Meeting suka zo yi Abuja,Niima ta gigice kamar bakuwar kudi bayan gidansu ma sunfi Gomna kudi, sai gyara Riga takeyi tana karairaya,Ido hudu sukayi da Gomna tare da Manyan masu kudi da suke kusa da Gomna,tasan Gomna ne amma bata San Gomnan wanne state bane,Gomna shima yaga me Kyau yawunsa ya tsinke,ba bata lokaci yayiwa yaronsa magana,sai gashi Cikin Guard wani ya kawo mata card na Gomna yace gashi Inji me Girma Gomnan Taraba State Exelency Muhammad Aliyos,fit Niima ta cafke Card tare da jefawa a jaka tare da furta tnx, guard da sauri ya koma cikin tawagar Gomna,Niima kuwa wani Farin ciki da girman kai ne ya mamayeta lallai ta cika me kyau da farin jini har Gomna guda binta sukeyi, tace ahaf har wani kudi ne damu,ai kudin yan siyasa sune kudi kullum shigowa suke ta ko ina kamar banza,duk da Babana shima yana siyasa ai ba kamar Gomna ba kai zan yashi dollars fa zanyi abinda naga dama,tana wannan maganganun zucin kawai Ahleef ya dawo cikin takunsa ko ina ka duba kallonsa akeyi maza da mata,ita Kanta Niima a ranta tace Allah ya zuba baiwa a nan.
Ahleef kashe mata ido daya yayi yana murmushi sai wani lallaba ta yake yana mata shagwaba sai ta fara biye masa sai ta tuno samarinta yan siyasa masu kudi ciki harda Gomna Aliyos.