
AsmaBaffa
[7/22, 1:09 PM] Sis Asma: ????????????
JIN DADI SABO
3
Official
By
AsmaBaffa
Naku ne Fans na ko ina.
Hannun Niima ya kamo yana kare mata kallo,wani yarr taji a jikinta shima haka a hankali yace I love u Niima dan Allah ki rikeni amana karki barni duk da nasan bani da wani Asali iyayenku sune gata na dan Allah karki kyaleni ki taimaka min ta wannan hanyar kadai zan iya sakawa da Momee da alkhairi tare da Abba shine na aureki ina matukar Sonki Niima,hankalin Niima ne ya Tashi gaskiya ita yanzu bata son auren nan idan tayi aure shike nan Namiji daya tal zata dinga kulawa mijinta,ba samari duk masu kudin nan baza ta kula kowa ba, a hankali tace ina sonka nima ai baka da matsala Dani,Murna ta kamashi yace yanzu dai na fadawa Abba a sa mana Rana ko? Uhm Kawai tace tana wasi wasi a ranta,sai kallonsa takeyi kamar mayya ,Kalli mijinki da kyau Babyna,kunya ce ta kamata ta mike tsaye tare da cewa tashi mu tafi Hearty.
Soyayya sosai take nunawa Ahleef bata nuna masa akwai matsala,shi kuma ya gama sakin jiki da ita sai kashe mata kudi yakeyi sosai,so iya so tare da kulawa yake nuna mata,ita kuwa bata wani caring dinsa amma tana nuna tana sonsa,sai wahala yake a kanta,Har Abba ya dawo sukayi shawara da Momee suka yanke hukunci,nan Abba ya nemo danginsa Maza da mata,tare dana Momee suka yanke ranar aure nan da 4mnths,Wasu a dangi suna ta gulma za a aurawa Niima Marar asali Dan gidan raino dan tsuntuwa,Niima munafuka a gaban dangi sai ta zauna tare dasu a dasa gulmar Ahleef da ita, tace sam ita bata sonsa Abba da Momee ne suke so nanfa Zance ya zaga dangi ai auren dole za ayi mata Ahleef kadai ke sonta sabo da yaci dukiyarsu sabo da yasan bashi da gado,Haka Niima tabi itama kawayenta tana fada musu sai tsinewa Ahleef akeyi shi kuma bawan Allah bai san komai ba murna kawai yakeyi kamar me, Momee da Abba ma murna Sukeyi Sosai.
Shukura zaune take gefen Inna dake dama fura,Shukura tace Inna Sosa min bayana,Inna ta jawota tare da kwantar da ita a cinyarta kamar jaririya ta fara sosa mata baya,ita kuma tana Inna nan nan,Tana kwance tace Inna miko min Plate din can na cinye awarata,Inna ta dauko mata,sai da ta cinye sannan tace Bari nayi wanki Inna, Inna tace wanki? A'a kwanta ki huta zan wanke miki su,Shukura tace Allah bar min ke Inna, Tana kwance Inna taje ta wanke mata kaya tas, da yamma Inna na aikin tuwo Shukura tace kawo nayi miki tankade Inna, a'a Shukura zaki bata kayanki zauna ki Huta abinki,Shukura kuwa ta fice yawonta cikin kauyen.
Tun safe Shukura yau da period ta tashi tana shan wahalar ciwon Mara Dama idan tanayi Sai kuka takeyi harda shagwaba ma abin nata,Inna kuwa harda kuka tana tausayin yarta,Baffa kam yau ko kiwon shanu bai fita ba sha lele ba lfy,sun rufu a kanta sai addua suke mata har ta samu bacci ya kwasheta,da yamma kuwa ta tashi sosai taji sauki har ta fito Tana wanke kayan da Jinin ya bata tare da panties dinta,bayan ta wanke tace Inna…zo ki karba ki shanya minsu,da sauri ta karba ta shanya mata Kuwa,Baffa ne ya shigo da sauri ya manta ma da wata Sallama so yake yaji jikin Shukuransa.
Shukura tana so ta fadawa Baffa Pad dinta ta kare dama ita take zuwa cikin gari can jikin wani asibiti ta siyo abarta Sabo da kauye ma basu wani santa sosai ba Da tsumma suke kunzugu,sai tace Baffa kaje bakin asibiti kace a baka Biredin mata,Baffa ya washe baki ahh lallai sauki ya samu Shukurere ta har Biredi zaki ci,wanne kala?,murmushi Shukura tayi tace Baffa a bakin asibitin Ishu kawai ake samo shi,kace biredin mata zasu baka haka ake fada a kauyen,Baffa harda tuntube wajen sauri yana zuwa kuwa yace a bashi biredin Mata aka bashi ya biya kudin duk tunanin Baffa wani Bread ne Me dadi a ciki,ya kawo mata gashi Shukurere ta aci da yawa kinji tace to Baffa,yace wannan katon Bread ai sai da lemo Shukura, Inna tace kayi sauri ka siyo mata Maltina tunda tafi Sonta,nan ma jikin Baffa na rawa ya siyo mata Maltina me sanyi yace tasha da biredinta.
Sosai suke ji da Shukura gata sai wanda ta gani,kullum haka take a rayuwarta cikin gata da jin dadi sabo da haka kuma mutanen kauyen sai suka tsaneta sosai kowa burinsa ya zaiga Shukura ta tozarta ta wulakanta amma ba dama Allah ya riga ya bata masu hassada sai kallo.
Ahleef tare da Farhan suna garden sai shirye shiryen biki sukeyi sosai ganin saura 2mnths bikin sai matsowa yakeyi, Ahleef ya Kalli Farhan cike da iyayinsa da ya saba yace Man ina ganin Matsala a wajen Niima abin yana damuna,na tambayeta ko da matsala tace a'a,murmushi Farhan yayi shima da Iyayi yace kai dai tsoro Kake ji so yayi maka yawa,hmm baza ka gane ba sam ba caring yanzu wani shareni takeyi na rasa me nayi Mata gaisuwa ma yanzu sai taga dama,bata ma so mu hadu,kasan fa mata haka sukewa ango idan za ayi musu aure haushin angon suke ji,pls ka daina damuwa tunda har itace ta Amince idan bata sonka baza ta yarda ba, Kai wace ta isa taganka tace bata so ko baturiya yace ai tayi karya,Ahleef yayi murmushi yace haka Momee ma tace dana fada mata amma wlh kaji na rantse da matsala a wajen yarinyar nan sai dai kawai Addua.
suna zaune saiko ga Niima tazo tana tafka uban Selfie ita da kawayenta su biyu ta Kalli su Farhan shekeke tare da galla musu harara,sai suka matsa gefe kawayenta suna yaushe zamuje Government House dinne? Tace munyi waya execelency na yace Next wk yana nemana,sannan jibi Senator dina zaizo gida wajena ban San ya zanyi da wannan angon nawa ba, dariya yan matan sukayi tare da cewa ai ba a daura ba bare ya Hanaki kula wasu shegen angon naki sai shegen iyayi ga rainin hankali dan kawai yana da kyau da kudi, daya a ciki tace Niima Allah yayi Miki baiwa da miji kamar Ahleef amma kina so ki cuci bawan Allah,Niima ta turo baki tare da cewa ke kin san dai nima kyakyawa ce ga farin jini idan ma yatafi dubu zasu zo min mutimin da ba'a san asalinsa ba har wani kyansa za a gani,idan kuma kudi ne ga Manyan kusoshin Gomnati nan duk ina dasu kuma nima ina da kudin haka ubana Ma.
Su kansu kawayenta sunga haukar Niima tare da butulci.
Niima haka kullum burinta ta dinga gulmar Ahleef Tana aibatashi tana zaginsa cikin mutane har zancen ya Fara dawowa kunnen Momee amma tayi shuru taga gudun ruwan Niima yarta.
Shiko Ango kullum yabon Amaryarsa yakeyi sonta na karuwa a ransa kullum yana manne wajen Abba da Momee suna shawarar biki.
Kwanaki na ja biki saura 1wks ango ba zama Amarya kullum cikin bakin ciki take bata shirya aure ba za a tauye mata rayuwa,yanzu idan ta yarda da auren shike nan Alhazawanta sai mijinta kawai.
Shukura kwance take cikin dare Tana ta kwasar baccinta taji kamar hayaniya a hankali ta bude idonta ta kunna torchlight kenan taji ashar da zage zage,ai sai ta kashe torch ta leka ta window nan take ta hangame baki tare da fara Hawaye taga Baffanta da Innarta an dauresu ga wasu jibga jibgan arna sunkai su 15 dauke da bindigu,Baffa taga sun kafe da mari,da sauri ta bude kofa ta fito da gudu Tana kuka tana rokonsu su bar mata Baffanta itama mari suka zuba mata nan take ta sume sharaf a kasa Inna ta fasa Ihu sabo da rashin Imani wani yasa wuka yayi mata yankan rago,Baffa ya rafka salati tare da dafe zuciyarsa nan ya fadi matacce zuciyarsa ta buga.
Arnan dariya suka dinga Yi ta mugaye sannan suka kada shanu da dabbobin Baffa kaf suka tafi dasu,a garin basu kadai ba har sauran fulani da dama wasu an kashe su an tafi da dabbobinsu, Tunda Shukura ta suma bata farfado ba sai da gari yayi haske lokacin Mutane sun cika gidan taf,da kuka hade da salati ta farka Tana Ihun Baffa…Inna…. Wayyo…nan tayi arba da gawarwakin Inna da Baffa sai ta haukace gaba daya tana birgima da ihu tana na Shiga uku ina zan sa kaina na huta,gatana ya kare Inna… Baffa sambatu takeyi Kala kala sai da kowa ya tausaya mata harda masu kuka gaba daya ta haukace bata san inda kanta yake ba, har akayiwa Inna da Baffa sutura tare da kaisu makwancinsu ana ta zaman makoki,Shukura kuwa suman ta yafi sau goma tana farfadowa kamar zata sheka lahira,sai maza ne suka riketa aka shiga yi mata addua tare da Kiran Nasuru me Chemist yayi mata allurar bacci ya sa mata Drip nan bacci ya kwasheta,bata farka ba sai dare Ta dora daga inda ta tsaya ana mata nasiha amma abanza cewa take ni bazan Hakura ba, in Allah ya yarda kuma sai iyayenku sun mutu Allah yasa babanku da babarku su mutu suma,bazan ba kowa hakuri ba sabo da nima bazan hakura ba.
wata tsohuwa tukuf ta shigo gaisuwa gidan Shukura wacce ta gama rama sallolinta Tana kuka ta Kalli tsohuwar tace ai gwara da wannan ce ta mutu tunda ta tsufa bata da amfani mene amfaninki,wata ma cikin dangin Baffa na sallama tace ga wannan Ma shekara nawa kullum cuta takeyi ai da ita ta mutu,matar tace Allah sarki yar nan kowa na can ne lokaci nane baiyi ba.
Wasu yan mata su biyu sunzo gaisuwa Zaraf shukura tace ga Baban wannan Ma shanyashi ake a Rana sai an kwantar sai an tayar mene amfaninsa Ai ni wlh iyayena sunfi na kowa Amfani, ana mutuwa amma mutuwar su Baffa ta musamman ce..ba shiri Nasuru me Chemist yazo ya kara dannawa Shukura allurar bacci da Drip, bata farka ba sai washe gari,ba laifi ta dan dawo hankalinta amma sai taji masu zaman makoki dangin Baffa suna lissafa mutanen da arnan suka kashe a garin,nan Sai ko akaji Shukura ta kece da dariya tace Alhmdllh uban kowa ya mutu wlh tunda ubana ya mutu uwar kowa ta mutu tunda na rasa tawa,yanzu har Dantani Baban Aishalle ya mutu?kai Alhmdllh amma Allah na gode maka,yawwa gwara Kowa iyayensa su mutu duk mu zama daya,ai wlh bazan Kara jimamin mutuwa ba, Ni mutum ya sake yace min ubansa ko uwarsa ta rasu sai dai aga ina nishadi wlh.
Wani ne ya rafka sallama tare da cewa bayin Allah Ashe arnan Jos har rigar yan jalo suka je sunyi kashe kashe da yawa yafi na wannan kauyen namu,ayyiriri nanaye akaji Shukura tace yawwa su dandana suma suji Me naji.
Kwana uku kullum sai anyiwa Shukura Allurar bacci bata ci bata sha sai an mata Jan Ido har akayi Bakwai.
Kullum Shukura bata daina kuka tana Tuna iyayenta zata fashe da kuka,haka har aka kwashe 40days Dan abinda Baffa da Inna suka mallaka aka siyar gaba daya har gidan da Shukura ke ciki,dangin Baffa dama tunda akayi bakwai suka tafi da Shukura gidansu,haka aka raba gado yanda Allah yace aka bawa shukura kudi dubu Dari biyar kasancewar Kauye ne filaye da gonaki basa tsada,Shukura ba kunya ta karbe kudinta a ledar Viva tana kukan su Baffa.
nan ta samu Kudin nan ta Fara dagargazar dadi,ba irin shawarar da yan Uwa basu ba shukura ba yanda zatayi da kudinta ta Samu ci gaba amma tace a’a Sabo Da tun farko bata da mafadi sai abinda taga dama take yi ba a sata ba a hanata, gashi bata daukan ko tsinke a gidan dama sun San halinta ganin maraicin da take ciki suke daga mata kafa,ga shegen iyayi wajenta, kudinta ta sasu gaba tayi kyauta taci dadi,yauma da Yamma liss taga wani katon zabuwa Tana yawo tace nawa wannan Zanbon Goggo ko na uban waye zan siya a siyar min shi,Goggo ta tabe baki tare da cewa nawa ne kuma ni dubu biyu zan siyar,nan ta zaro 2k ta biya tasa yara suka Kama mata shi aka yanka Sabo da Kiwa ma wata budurwa ta bawa tace gyara naman nan ki soya min Zan baki Dari biyar,jiki na Rawa budurwa ta Karbe tayi yanda take so, ta karba tare da figawa mutanen gidan nasu sabo da bata da rowa,zama Tayi da Maltinarta a gefe tana ci tana kora Maltina sai kuma ta fashe da kuka ta tuno Baffanta da Inna yanda watarana ma abincin a baki suke bata ana lallabata taci,haka takeyi kullum barnar kudi ga Dunkuna tana faman yi iri Iri har shopping taje cikin garin Jos ta siyo cosmetics da turaruka masu kyau,abinda kawai take birge mutane dashi addini ne da ita sosai bata wasa da addini.
A kwana a tashi Dangin Baffa suka takura su ta ishesu tayi girma da yawa dole sai tayi aure ko su bata duk wanda suka ga dama,ita kuma tace ba wanda ya isa yayi mata dole,su kuma Suka ce baza ta ja musu abin kunya ba sai dai ta bar musu gida baza su iya da halinta ba, Kawunta ta samu tace Kawu kasan bana Zance bani da saurayi kuma ina so na cikawa Baffa burinsa na zuwa abuja nayi kallo kallo.
Takaici ya kama Kawu kawai ya jawo sanda ya fara zane Shukura Yana Karuwanci zaki shiga tsinanniya,sai da ya farfasa mata jiki abinda iyayenta ko zagi basu taba yi Mata ba, haka suka bi suka tsaneta a gidan da sauran dangi bata da ikon magana sai duka kuma yanzu aiki ake sata sosai a gidan kamar jaka lallai taga maraici, ko wanke wanke idan tayi To ranar da zazzabi zata kwana bata saba ba,Kwatsam sai Kawu sukayi shawara a junansu suka zabowa Shukura miji wani Me kiwon Shanu Halilu,Halilu Dan shaye shaye ga neman mata kaf garin an sanshi,Shukura bata da labari sai da bikinta ya rage saura 1wk taji ana kiranta da Amarya tana tambaya taji a garin ana ta mata dariya anga karshen iyayi da jin dadi.