JIN DADI SABONOVELS

JIN DADI SABO COMPLETE

JIN DADI SABO COMPLETE HAUSA NOVEL

Momee Dalilin abinda Niima tayiwa Ahleef yasa Hawan jini me karfi ya kamata ta fara cuta me tsanani tun tana boyewa har ta kasa motsi gashi lokacin su Salman Sun koma Uk sai Latifa kawai, Ahleef kuma yanzu tunda abin ya faru Sam baya zama sosai a gidan yafi zama a katafaren wani gidansa daban can wata Unguwar da turawa suka fi zama ciki,ba ruwan wani da wani,kamar malaikan mutuwa haka ya koma ba fara’a ba komai ko magana sai ta kama wannan abin ne ya damu Momee har cuta ta kamata,Abba ma Yana Tunusia bai Sani ba boye masa takeyi,Ahleef ne ya shigo da safe gidan yaci uwar wanka Cikin wani yard hadadden gaske dinkin ya masa kyau sai kamshi yake zubawa,ga wani agogo malam abin kallo,Sumar nan tasa kyalli takeyi lips dinsa yana sheki jajur dasu.
Cikin takunsa na kasaita ya shiga bedroom din Momee yana bulbula kamshi,Subhanallah ya furta hangota yayi kwance ta dafe kirji tana tari tare da haki ta rame,da gudu ya karasa kusa da ita bai ma Bata lokacin yin magana ba cak ya dauketa ya sauka kasa cikin sarsarfa escort dinsa suka figi motoci sai wani katafaren asibiti Emergency,likitoci suka rufu kanta har aka samu ta farfado sai aka canja mata daki suka ce dole sai tayi 1wk Ko 2wks kafin a sallameta,Momee tana jin dan sauki tace kar Ahleef ya fadawa kowa sai ta warke,yace to Momee Tawa Allah baki lfy tace Ameen,Tunani yakeyi wacce mace zai dakko wacce zata iya kula masa da Momee.

Shukura yau titi ta yini tana yawo ga yunwa da take cinta,tana zaune jikin wata bishiya a zaune mararta ta murda ta fara ciwo sosai take ciwo da alama Period zata fara,ta Mike a hankali ciwo na cinta Bata kula ba ta tsallaka titi sai mota ta fyallo da gudu saura kadan ta maketa Allah ya taimaketa kadan ta dan bigi Kafarta sai ta fadi can gefe,dalleliyar motar ce tayi parking wani katon arne Igbo ya fito da sauri yaga jini na bin kafafunta tunaninsa motarce ta mata rauni haka bai san period take ba dama kuma ba pad jikinta,a motar ya sata ya figeta tana kuka za'a saceta,bai tsaya ko ina ba sai asibitin da aka kwantar da Momee tasu Ahleef, sai kuwa aka rasa dakin da za a kwantar da Shakura sai dakin da Momee ke ciki suka shiga neman izini tunda daki mutum daya ake bawa.

 Ahleef na zaune gefen Momee suka shiga suka nemi izini tunda dakin da aka sa Momee na mutum biyu ne normal, Ahleef yace bai yarda ba, Momee tace Son kyale a taimaketa a kawota ba damuwa.
Shukura kukan Shagwaba kawai takeyi Wanda dama ta saba,jini na bin kafafunta aka turota  Saman bed har dakin,duk ta cikawa mutane kunne.

Ahleef Sam bai ganeta ba,amma kamar ya santa amma ya manta a Ina,Momee tace sannu yarinya ko cikine daita tayi barinsa Allah Sarki gata kyakyawa Mashaallah,Likitoci sukace Ahleef ya fita zasuyi aiki yace wlh ba inda zaije me zai gani bayan sunsa wani labile Sun kare yarinyar,suna Jin Kukan Shukura tana kwarototo wayyo….Marata zata belle,meke damunki ? Kina da ciki ne ? Shukura ce tace ni Jinin Haila nakeyi ubanku ne yayi min Cikin ? Ai Dazu wani yace mu hadu a Hotel kuma banje ba wai ni zai yiwa wayo,kara ta kuma kwallawa tace wlh haka zaita zubowa haka yake min duk watan Allah, Innata ma Kafin ta mutu tace nafi wata me haihuwar ma wlh, yiiiii…. Taci Gaba da kuka nurses sai dariya sukeyi Wanda Suke Jin Hausa,Ahleef da Momee suna jinta sai dariya Momee takeyi kasa kasa,Ahleef yana ji ya daure fuska a yana wannan yarinya bata da sirri ta fiye surutu ga kukan tsiya yaja tsaki.
Anzo za ayi mata Allura ta fara tsandara kuka ita bata so,aka canja mata magani nan ma ta fara kuka ita Bata sha, Ahleef ta kaici yasa bai san sanda ya daka mata tsawa ba, Ta Cikin labile taji gaba daya ta firgita,ta kidime da sauri tace to ayi min Allurar,sai anzo za a tsira sai tace wash…ta fara guduwa Momee ce ta dan yiwa Ahleef magana Da ido wai ya kara mata magana,ba Wanda yasan fuskar kowa ta labile taji muryar dazu me shegen dadi amma ba alamar mutunci a cikinta ba shiri tace ayi min zan tsaya, sai da aka gama yi mata komai sukace taje tayi wanka,Igbon daya kadeta shine ya siyo mata doguwar Riga ta wani material me shegen kyau da tsada harda pad da parties kala biyar tunda ya basu,suka ce kwana uku zatayi a asibitin sai kafarta data ji rauni ta warke, kawai yace a bashi Bill zai biya sai da ya biya komai sannan ya samu wata Nurse ya Bata kudi kullum ana siyawa Shukura abinda takeso tana ci har a sallameta kuma su kula da ita sosai,sai ranar da za a Bata sallama zai dawo ya dauketa.

Shukura kuwa Wanka tayi ta shirya kanta ta wanke Wanda ta Bata sannan ta fito wow ba karamin kyau Material din yayi mata ba kamar a saceta,an gyara room din sai kamshi kawai ke tashi,an cire labilen da suka raba tsakaninsu da Momee,nurse ce ta shigo gashi baza ta iya tambaya da turanci ba ina zata shanya kayanta ? 

Kawai sai ta kwanta Saman Bed dinta ta fashe da kuka,tana shure shure,Ahleef sai yanzu ya tuna da mutum fa a wancan bed din,Momee tace yan mata lfy ? cikin kuka tace ni ban… Iya…turanci ba…small small nakeji kuma so nake na tambaya wannan Nurse din ina zan shanya kayana nayi nayi na tuna sunan shanya da turanci na kasa,Momee tace to ai ba kuka zakiyi ba Nima na iya ga dana ma, Shukura sai ta Mike zaune tace tsohuwa dake yaushe kika koyi turanci ? Yanzu dama irinku kuna Jin turanci a birni ? Momee tayi dariya tace ae mana, Amma Gwaggo tun Jahiliya ke Babanki wayayyene, Tab niko Inna ta Allah yaji kanta tana dariya ta karasa da wlh kwakwalwarta a dinke aka yi mata ita kamar ansa zare da Allure a dinke ta,Ahleef dariya ta kamashi da kyar ya iya dannewa,Shukura taci gaba yanzu wannan baturen danki ne ? Momee tace ae mana shine yake jinyata,Uhm kawai Shukura tace har ta kwanta ta kara mikewa zaune tace Gwaggo wai dan Allah ya sunan jakin babangida da turanci dama tun Baffa yana da rai nake ta so muzo birni na tambayi yan gayu,Momee tace ke kin cika surutu ki kwanta ki huta Nurse ta kawo miki abinci kici,Shukura tayi dariya tare da cewa dan baku San wace ni ba,kaf garinmu babu kamata,miskila ce ni,shuru shuru bana magana yanzu ma dan ku yan gayu ne kawai shi yasa nake so na karu daku kafin na tafi.
tsaki Ahleef yaja ba shiri ta kwanta tayi luf,nurse da kanta ta shanya mata kayan ta Bayan room dinsu,an kawo mata abinci shinkafa da miya tare da yankan nama biyu, bude abincin Shukura tayi da sauri ta rufe tana ni bazanci wannan ba shinkafa da miya tsura sai gutun nama ina laifin ace da salat ma tare da Ko balangu ne daban Bazan iya cin wannan ba sai ta fara kuka tana da Baffa na yana da rai wlh saniya zai yanka min ma,Momee tace ikon Allah ki dinga hakuri da lamarin duniya tsaya a kawo min abinci sai kici,ba a fi 5mnt ba sai ga Driver me aikin Momee ta aiko da abinci iri iri.

Momee tace taso ki iba, Tana daga kwance tace dan gidan Gwaggo dan zubo min naci dama ta saba bawa iyayenta Umarni,ko kallonta baiyi ba waya yake latsawa,ba shiri ta mike har gaban Momee sannan tace sannu da jiki,Momee tace yawwa ebi ki tafi,nan fa ta fara kici kicin bude Flasks kowanne ta kasa budewa har nishi takeyi Momee tana ta dariya,sai da tayi ta gaji sannan tace kai ni na gaji gaskiya,Momee tasan Ahleef bazai bude mata ba sai tace bari na bude miki,jin Momee zata bawa kanta aiki kawai sai yace kwanta Momee ya fisgi flask daya ya bude,ya bude sauran ma wani kamshi ya daki hancinta,Shukura tace zanci wlh na gode,ta dauki plate ta ebi farfesu,ta ebi naman cikin miyar,sai ta ebi chips duk wani abin dadi shi ta iba, karshe ta kalli shinkafar fara ta zaro mata ido tare da cewa ke yar gidan kowa ce me za aci da ke in banda kisa mutum basir Bazan taba ibanki ba,Macaroni ma ta kalleshi tace ga kayan dadi wa yake ta kai me za aci da kai da wasu kofofinka kamar na hancin mutum.

Momee ta fara dariya, Ahleef a ransa yace wannan kawai yar iskar kauyece yana dariya a ransa, ita kuwa ko rufe flaks din batayi ba ta koma gefen gadonta ta fara ci, Ahleef cikin Isa yace wa zai rufe miki Flasks din ? Dan mitsitsin lips dinta ta turo zata yi kuka tsawa ya buga mata Idan kika Sani magana…kafin ya karasa har ta diro gaban kayan ta fara rufewa daya bayan daya da kyar, Momee tace Bata da lfy fa kana takura mata Son,Momee bari naje na dawo,ok kaini bakin toilet sai ka tafi,bayan ya kai momee tayi fitsari ya kara riketa ya kwantar da ita Saman Bed sannan ya fice abinsa.Shukura tana gama cin abincinta ta kwanta sai bacci ya kwasheta me karfi.
Bata tashi ba sai Cikin dare karfe 11pm tana bude ido Momee ta hango tana sallah saman sallaya Ahleef yana gefe saman Bed yaci uban wanka Cikin 3qtr da yar armless yana karanta jarida ya harde kafa daya kan daya,Shukura a ranta cewa take gaskiya ya hadu Ban taba ganin irinsa ba a duniya,a hankali ta Mike Bata Sani ba garin bacci pad ta goce ta Bata kayanta kadan Ahleef yana gani ya runtse idonsa yana Jan tsaki an kawo musu kazama daki a haka gata kamar me tsafta,sai da ta shiga toilet ta fara takaici Allah yasa dai dan Gwaggo bai gani ba, sai da ta gyara kanta tsaf ta fito tare da cewa Gwaggo dan san min turarenki,murmushi momee tayi ta mika mata kala uku ta shafa,Mikewa Ahleef yayi tare da cewa bari naje na kawo miki abincin zan aiko a kawo miki,Momee tace ga Shukura taji sauki tunda siyo min zakayi kuje tare Idan kun dawo sai ka Bata ta kawo, da sauri yace no Momee pls wannan kazamar ? Bata rai Momee tayi kawai da sauri yace am sorry Momee ke zo mu tafi,Shukura ta tsaya kallonsu suna birgeta yace kazama i’m talking to u da sauri ya fita cike da gadara,tabi bayansa da gudu gudu sauri sauri,jikin wata rantsatsiyar mota ta hangoshi ya bude side din Driver yashiga yau ba Escort da sauri cike da kauyanci ta zaga itama ta rasa ina zata bude kawai ta finciki murfin mota kamar zata balle shi, da kyar da kokawa ta bude gaban motar ta shige shima ya shiga yana dariyar kauyancinta a ransa yace mace har mace haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button