NOVELSUncategorized

KWARATA 85

???? —— 83
     Da farko dai Dikko mutumin kirki ne a wurinta , nagartaccen namiji mai zama , tsayayyen namiji mai lafiya da cikar zati da kwarjini , jarumin namiji ba lusari ba , idan akace mutum bashi da mutunci ko rashin ragowa idan dai baiyi maka ba tou kai mutumin kirki ne a wurinka , duk halin mutum na kirki dana banza idan dai bai nuna a kanka ba tou
bazaka sheda mugayen halayenshi ba , Dikko yana da mutunci amma shi baya shiga sabgar kowa , ko a baya data sanshi da lafiyarshi tasan baida haƙuri haka kuma bai ɗaukar sakarci da shirme , kayi ta magana yana jinka saidai yayi kunnen uwar shegu dakai , yana da tausayi sosai amma yafi tausayin mata a rayuwarshi.

    Baya dariya baya murmushi idan kuma ka cika shi da surutu zai tsare ka da dara²n idanuwanshi har sai kaji tsoro kai da kanka zaka lallaɓa ka tashi ka kama gabanka , baya sabgar mata baida budurwa ko ɗaya amma yana da dawakai masu lafiya da ƙoshi , babu hoton mace a wayarshi amma zaka iya samun hoton doki babu adaɗi a wayarshi , ya yadda da doki sosai kuma bayajin wahalar sayenshi baida magana sai ta doki dan ko yana zaune da abokanshi idan suna fira masu zancen “yan mata sukeyi , masu mata suka labarta nasu shi zaice dokinshi kaza² , sai zancen kayan doki maganar polo kalamanshi dai suna tsayawa akan doki ne kawai da abinda ya shafi dokin , idan ance masa shi baya budurwa zaice shi baya san raini dan yaji yadda su kansu suke magana akan matan , kuma yana ganin yadda matan gidansu ke ranfa da maza , gashi kuma suna faɗar irin halayen da matan ke musu , kanaji da girmanka da shekarunka ƙaramar yarinyar daka haifa tayi maka rashin kunya shi duk sabgar da zata zo da raini ko rashin kunya baya ciki shi yasa bai shiga sabgar kowa saita doki , dan doki idan ya sanka kaine kake cidashi kake shadashi akwai ragowa tsakaninka dashi amma idan ya tashi aure zai auri cikakkiyar mace data san kanta mai shekaru da yawa shi gaskiya bazai auri “yar ƙaramar yarinya ba dan idan ya auri yarinya shi kanshi saiya raina kanshi ƙaramar yarinya mai ƙananan shekaru bata dace da rayuwarshi ba…

    Murmushin ƙarfin hali Suwaiba tayi tare da goge hawayen dake kwance a saman fuskarta , a bayyane tace ashe dai da rabon sai ka auri ƙaramar yarinya , yarinyar ma ta ƙasan² shekaru , yaushe kuka haɗu kukayi soyayya har aka kai matakin aure …..? Hmmm koma dai miye Suwaiba ba damuwarta bane ba ,

Marin birich a jahar Lagos , madakata ce ta mutanen da basajin magana ko kuma nace wanda suka gagara , madakata ce ta mutanen da suka fi ƙarfin gida ko suka aikata ɓarna saisu gudu daga jahohinsu sai suyi ma kansu masauki a wurin domin tsira da rayuwarsu , mazauna wurin gafurtacci ne kuma gagararri wanda suka ansa sunansu wurin rashin jin magana ko iskanci.

    Duk irin matsalar da kaje da ita a wurin sai kaga wanda ya shafe taka ya burjeta murus , idan kuma zancen iskanci ne da duk wata ƙaramar rashin kunyarka tou fa daga wurin dai an rufe littafi , idan ko ke karuwa ce a iskanci har kika je Lagos kikayi rayuwa a ƙarƙashin gada tou lallai iskanci daga kanki an kashe boss , duk namijin da yaje wurin shima dai abin kwatance ne tou ina ga mace kuma….?

       Matsalar iyaye itace ta kaini garin Lagos kuma nayi rayuwa a wurin dana faɗi sunanshi daga sama , auren soyayya nayi dani da mijina wanda ni dai Allah ya sani dama bawai wani cancan nake jinshi a raina ba , na aureshi ne saboda girman dukiyarshi wanda mu a zuri’armu attajiri ne sosai dan talaucin mu , ni bana sansa kwata² amma ina nuna masa soyayya saboda kuɗinshi shi yasa yayi tunanin ina sansa har a zuciyata , 

   Tou mundaiyi auren na soyayya kamar yadda mutane suke kallo a zahirance amma a baɗinance ni a wurina kuɗinsa na aura , tunda aka ɗauramin aure dashi iyayena sukayi min huɗuba cewa nadai gansu a gidan haye suke zama tou inyi ƙoƙari na ƙulla musu mazauni kafin mijina ya sakeni dan masu kuɗi basu cika zama da aure ba nayi ƙoƙari na gina kaina kafin yayi min wurgin kashi a shara , a nawa ganin nidai ina kallon anyi ma masu kuɗi fahimta ce mara kyau domin auri saki hali ne , kamar jini haka yake gudana a cikin zuciyar mai irin ɗabi’ar danshi auri saki babu ruwanshi da mai kuɗi babu ruwanshi da matalauci haline ne kuma yana ƙarkashin zuciyar maishi.

    Tunda aka kaini gidan mijina duk ƙarshen sati sai an aiko ƙanina daga gidanmu wai in bada kuɗin zubin adashe , akan me zance babu ? Dan ko shi ƙanin nawa idan yazo sai ankai ruwa rana nake haɗa masa kuɗin motar komawa dan mijin dana aura mannanu ne bashi da alkairi ko kaɗan dan ko kuɗin cefane ya bada idan ya dawo sai anyi lissafi saiya ƙwaƙwale canjin shi tass ya barni zero ɗina.

   Mahaifiyata data ga kullum ƙanina yana zuwa yana dawowa babu kuɗi satin gaba yana zuwa ta tattaro ta taho da kanta , nasha zagi sosai tace ina nan na shige cikin a c na manta da ita , ina nan kullum sai naci nama nasha ruwan lemu , da safe naci shayi da burodi na barta a daura tana can kullum safiya tana karo da zazafen tuwo , taɓarya zata kasheta saboda daka da wahalar rayuwa , ina shafa ruwan sabulu mai ƙamshi idan zanyi wanka tanayin wanka da garin omo sai Allah ya tsenemin tunda na barta take shan wahalar rayuwar.

Na nuna mata cewa kuɗin bafa a hannuna yake ba nima a ƙarƙashin wani nake sai abinda aka bani , kuma bani nake da alhakin kula da ita ba taje tayi haƙuri taci abinda Allah ya hore mata tace bata yadda ba dole irin abinda naci irinshi zata ci , kuma saina shiga adashen nan duk abokan aure na babu wacce bata mallaki ƙaddarar dabbobi ba dan haka nayi ƙoƙari na samu.

Duk yadda naso na nusar da ita ƙin yadda tayi wai a dole saina samo idan ya shiga wanka in riƙa lalube masa aljihunsa dan wallahi ta aiko satin gaba bata samu kuɗin nan ba kashe wannan auren zatayi dan bata ga amfanin aure babu ci gaba ba , nace tou , data tashi tafiya saida ta tunbiji kayan abinci shinkafa taliya makaroni kuskus ta ɗauke sauran madararmu duk abinda ta gani gidan saida tayi gaba dashi buhu guda ta cika na shinkafa da abinda ta tattara daga gidana.

     Bayan mijina ya dawo ya shiga store ya fara dube² dama wannan shine al’adarshi duk daren duniya idan ya dawo saiya duba kayan abinci , idan kuɗi ya bani saiya anshi canji , idan naman abinci ya kawo saiya irgashi , tun daga store ya fara faɗa wai yau yaga abinci yayi ƙasa bayan yabarshi da yawa kafin ya fita , ina na kai mishi abinci ? Nace ina kuwa za’a kai abinci inda ya wuce cikin ciki……..?

     Karfa na raina masa hankali haka yai ta zazzaga ruwan wulaƙanci karshen film in dai yace min dangi ɓarayi sata kamar ɓere zai maida abincin ɗakinshi duk safiya zai auno min gwangwani ɗaya tunda na zama ɓarauniya ba ruwanshi da baƙo kuma idan taliya ya bani ita zanci daga rana har dare , in shinkafa ne itama haka , ya kwasa rashin mutuncin shi daga baya ya kwashe komai zuwa ɗakinshi , binshi nayi ina bashi haƙuri ya basar ya shige toilet , yana shiga naci gaba da bashi haƙuri ina ɗaga kayan daya cire , kayi haƙuri don Allah , a dai² lokacin dana ƙwale² aljihunshi tas , bazan ƙara ba , a dai² lokacin dana ajiye wando na ɗauki rigarshi , na bari don Allah na kwashe kaf kuɗin masu yawan gaske na fita daga ɗakin , ban nufi ɗakina ba na nufi bayan gidan na tona rami na rufe su na maida busashshiyar ƙasa na rufe nayi ma wurin alama da tsinken tsintsiyar kwakwa…..

     Ɗakina na koma naci gaba da kuka ban ƙarawa , a haka ya sameni yana ina kuma kika kaimin kuɗin na , rigima ya kaure tsakaninmu tashin hankali na kada Allah maimaita mana anyi shi , kuma tun daga wannan ranar ban ragawa aljihun mijina ba , ba aljihu kaɗai ba ko wanka ya shiga haka zan bincike kaf ma’adanar kuɗinshi , kafin wani lokaci na ƙware da wurin iya sata , kuɗi kuwa duk satin duniya sai anzo an ansa a gidanmu.

    Mijina kuwa sai ya daina shigowa da kuɗi gida ya riƙa barinsu a mota , dana duba naga babu komin dare saina lallaɓa na cire makullin naje na buɗe na kwashe kaf kuɗinshi , koda ya kai ƙarata gidanmu iyayena cewa suke aljannu ne dansu “yar su ba ɓarasuwa suka haifa ba , suka ɗauremin ƙugu naci gaba da tsula tsiyata….

     Daga dai ƙarshe mijina ya samu kwanciyar arziƙi dan haka mahaifiyata ta murje idonta tas ta kashe auren nan mijina yayi kuka ya shiga tashin hankalin rabuwa dani ni dama can bana wani sansa , bayan mutuwar aure na gama iddah na sake auren wani amma baikai mijin dana baro rufin asiri ba , shima haka na taso tattalin arziƙinshi saidai na ƙareshi kaf nayi gaba abuna , kuma har zuwa wannan lokaci iyayena basu sayi gida ba , aure na gaba mijin wayayye ne domin shi a banki yake ajiye kuɗinshi ban wani daɗe ba na kashe auren dan zuwa wannan lokacin nima na goge da idan babu malasa gaba nakeyi abuna , bayan wani lokaci na sake aure na auri wani manomi bagidaje ne dan haka shi amfanin gonar na riƙa siyarwa , shima ya gaji ya sakeni daga haka ban sake aure ba dan duk wanda yazo ce masa akeyi ni ɓarauniya ce , wannan dalili yasa ban sake auruwa ba ,

     A gida zaman dai babu daɗi dan banda aure kuma banda inda zan samo kuɗi aka fara hantara ta a gidanmu , dan haka na fara sata da maƙota cikin ƙanƙanin lokaci na zama mashahuriyar ɓarauniya a cikin anguwarmu , ko shaguna naje sayayya danaga ba’a kallona sai inyi sata in gudu….

      Duk wannan ƙoƙarin da nakeyi a haka banyi ma iyayena ba dan haka na haɗa dai da “yar bariki ta , ina karuwanci ina sata kuma har yanzu basu sayi gidan zama ba , ganin haka yasa idan na sato na daina basu naci gaba da sata ina ɓoye abuna , wulaƙanci a gidanmu kuwa na dare daban na safe daban , a wurin iskancina na haɗu da wani babban attajiri shine ya ɗauki hayata ya tafi dani Lagos , a ranar daya kwana dani a ranar na ɗauke jakar kuɗinshi na gudu ,

    Ban bar Lagos ba na nemi matattarar “yan iska wanda suka gagara shine aka bani tayin marin birich ranar da naje da ƙarfin bala’e aka ƙwace kuɗina , naga iskanci da ƙaryar rashin kunya , naga dabar data girmi irin wacce nake gani a garin Daura , naga karuwancin daya girmi nawa naga salon sata wanda ya girmi tawa , wurin yamin nayi zamana da safe zan fita cikin gari nayo iskanci na dawo , wata na biyar a wurin mai hali baya barin halinshi nayi sata naci bugun rabani da yaro kuma sunce sai sun kasheni haka suka ɗaureni a jikin ƙarfe suka watsamin fetir suka cinnamin ashana dan sunfi ƙarfina ina ji ina gani zan mutu kuma gani ɗaure , a dai² wannan lokacin ne Allah ya kawo Dikko , dashi da abokinshi shima kuma kanshi baisan haka wurin yake ba yayi rakiye kawai ni bansan abinda yakai su shi abokin nashi ba.

Dikko yasha dariya sosai sannan ya ɗauki ruwan wani gahurtaccen ɗan daba daya zuba a bokiti zaiyi amfani ya sheƙamin a jiki wutar ta mutu , tun bai gama zuba ruwan ba ɗan daban yasa yaranshi suyi ma Dikko gunduwa² wanda ya kunna min wuta kuma yasa yaranshi su sake tashin wata wutar amma akan Dikko , saboda wurin gungu² ne na sansasanin “yan iska , kowa da zugarshi kuma kowa yana da yaranshi mutanen dai sun kasu kashi daban².

     Wanda Dikko ya rako ya ruga da gudu ya duƙa gabansu yace su rufa mishi asiri Babanshi yake neman gwamna karsu kashe shi , ashe ma basu zama gwamnan ba ? To ko ɗan shugaban ƙasa ne sai sun kunna mishi wuta , su kuma dabar wanda aka ɗaukar ma ruwa suka ce ko gwamnan ne sai sun fyeɗeshi harya isa ya shigo da’irarsu ya haresu ? Shi kuma Dikko yana kwunce Suwaiba daga ɗaurin da akayi mata kuma har yanzu bai daina dariya ba…..

    Kawai dai anyi tashin hankali mara kyau dakel aka samu aka fitar da Dikko daga wurin da taimakon wanda abokin Dikko yazo wurinshi , kuma duk tashin hankalin nan da Suwaiba ya tafi , tun a mota Dikko ke kuka wai yanajin tausayin sauran matan da aka baro shi wannan wane irin rayuwa ne ? Me yasa mata zasuyi iskanci wai…….? Ya bani shidai baya so yaga mace tanayin abu da bai kamata ba shi dai zai koma ko zai mutu saiya fitar da duk wata mace a wurin , abokinshi yace tou ka rufawa kanka asiri dan ka sake ka koma wurin nan saidai wani ba kai ba , Dikko da kafiya cewa yayi saiya koma su kashe shi , duk haƙurin da aka ba Dikko ya kafe kai cewa saiya koma a kashe shi…..

     Nice na bashi haƙuri nace kar ya koma dan na fahimci shi ma’abocin tausayin mata ne amma yana da kafiya idan ya duƙe akan abu sai yayi , nace kayi ka haƙuri ka ƙyalesu duk wacce ka gani itace taje da kanta take zama , kuma idan ka koma zasu nemeni su kasheni , daga haka yayi shiru dai bai sake magana ba , ni bansan abinda abokinshi yaje yi ba , kuma bansan dalilin da yasa shi Dikko yayi rakiya ba , dalilina na bashi haƙuri nasan idan har tsautsayi ya maidashi sai sun kashe shi har lahira….

     A cikin jirgi muka zo kano daga Lagos jikina yana ta raɗaɗin wutar data ci jikina sama² , a kano aka ɗaukemu a cikin wasu irin zafafan motoci har katsina , saida ya kaini asibiti aka dubani.

     A gidansu Dikko kuwa mahaifiyarshi tayi tashin hankali akan bazan zauna ba , ta zage shi so babu adadi tunda yace kiyi haƙuri Momy zata zauna bai sake magana ba yaci gaba da sabgar gabanshi , ita irin mutanen nan ne masu ƙyanƙyamin mutane , ankai ruwa rana Dady yace tunda Babanshi yace saina zauna babu wanda ya isa ya hanani zama.

   Tunda nake zaune a gidan banda wata damuwa domin Dikko yace duk abinda nake so na faɗa masa , shike ɗauke da duk wata ragama tawa duk abinda nake so zan rubuta a rubuce na bada akai mishi , baida hankali wurin kyautar kuɗi hannunsa a sake yake yana da alkairi sosai amma bashshi da mutunci idan aka taɓoshi duk gidan sai kowa yaji masifarshi yana iya sati yana masifa akan abu ɗaya bai gaji ba dan bai gajiya da fitina gashi da kafiyar bala’e idan ya duƙe kai akan abu babu gudu ba ja da baya….

    Tabbas Dikko yamin gata yamin halakci fiye da tunanin yadda mai tunani zaiyi zato , ko tafiya yayi ya dawo haka zai jibgomin tsaraba ta sutura saboda duk yadda zan faɗi gayun shi bama zan iya musultawa ba , yanda yake ɗan gaye saida ya tabbatar ya maidani “yar gayu ta gaban jarida , kuma nayi masa koken rashin mazaunin iyayena shi ya tsayar dani akan ƙafafuwana lokaci guda nasha gaban duk wani mai tayarmin da ƙura ya kulleni da motar hawa ta abun kwatance a idon duniya…..

     Amma sai na ƙulla aminci da abiyar zaman mahaifiyarshi , ita tana jawoni a jikinta saɓanin mahaifiyar Dikko dan haka aka shiga neman kai ƙarshen rayuwar Dikko dani , itace take aikena nemo mata asiri tana san ganin ƙarshen Dikko tace yadda itama bata da namiji babu wacce ta isa tayi namiji a gidan , tun da aka haifi Dikko take neman sa’arshi bata samu ba kuma baza ta daina ba haka kuma bazata gajiya ba har sai ranar da Dikko ya daina numfashi.

     Ina cikin ƙulun bitar bin malamai da bokaye Al ‘ Ameen ya saƙo cikin aiki ta hanyar bina da yayi ban sani ba har inda zanje , bayan ya tabbatar da komai yazo ya zayyana min hankalina ya tashi kuma na firgita amma sai yacemin na haɗashi da matar Dady na faɗa mata cewa shima yana san ganin bayan mai gida ne kuma yana shirye akan zai bata taimako ko wane iri take so.

      Tayi na’am da haka itace ta bada kuɗi Al ‘ Ameen yaje ya samo asiri aka haɗa manyan masifa aka binne a wani daji sai iskokai suke gadi ana biyansu da jini duk karshen sati , wanda kuma ake so yaci a abinci shine idan yaci zai riƙa haukacewa duk lokacin da yayi fushi yana maganar kisa , iskokai kuma sune zasu riƙa shafarshi , Al ‘ Ameen yace zai iya bashi , tou shine maganin daya bashi a London , dan rigimarshi shine suka juya abun da faɗanshi shi yasa duk lokacin da yayi fushi sai ya riƙa cewa saina kashe ka……………. Farkon asirin rashin lafiya ya farayi kaɗan² Dady yasa aka dawo dashi nigeria baida lokacin tafiya ya tsaya yana ta siyasa , Dikko yayi ciwo na tashin hankali babu wanda ya bashi tashi a duniya , saida aka saka mishi robar hanci kowa ya haƙura dashi , shine Dady yaita rashin lafiya sakamakon ciwon Dikko har ya samu ciwon zuciya saboda tunani , aminin shi Dady shine ya gano ciwon Dikko asiri ne ya kuma faɗawa Dady ciwon Dikko bana asibiti bane ba dan wasu Allah ya basu lilimin gane sihiri , kuma ya miƙe tsaye ya gano cewa Dikko ana so ne ya mutu ta ko wane hali idan bai mutu da kanshi ba yayi kisa sai a yanke mishi hukuncin kisa kuma shi ya samo duk wannan magungun nan da ake mashi amfani dasu ,

     Abinda yasa Dikko yasan ina da sa hannu a rashin lafiyarshi , mai aikin Momy taji muna magana da Al ‘ Ameen a palo ni kwata² bansan tana nan ba kuma bansan ta shigo ba , Al ‘ Ameen yana magana ƙasa² yake faɗamin boka yace abokin Dady ya miƙe tsaye akan saiya gano duk wani mai sa hannu a rashin lafiyan mai gida shine boka ya bada wasu layu yace aje a tsakiyar gidan nan a rufe ana rufesu an rufe zancen , zaici gaba da magana aka kirashi a waya ya fita bayanshi na bi muka bar ɗakin gaba ɗayanmu , tou itace taje ta faɗawa Dikko iyakar abinda taji amma bata san da waye nake maganar ba , shine yazo yace min ni bazaimin komai ba amma in faɗa masa ko waye yake da saka hannu kuma waye zai binne layu a cikin gidansu , kafin inyi magana shine ya nufi wurin Mom inshi wai tazo taji da kunnenta an haɗa kai da Suwaiba an cuci rayuwarshi sai idan yayi magana ace bashi da haƙuri ya cika masifa , sanin halin Dikko yasa kafin ya dawo na gudu dan nasan duk da yace bazaimin komai ba nasan sai yayi idan har ya riƙeni mai kwatata a hannunshi sai Allah shine na gudu Dikko baisan daga inda nazo ba kuma baisan ina zan koma ba tsintoni yayi kuma na gudu abuna , ashe Al ‘ Ameen shine yayi sanadin zamana gurguwa , ya bini ya kasheni gudun karna tona musu asiri , shine ya ɗiɗɗirka min alburusai a ƙafa , wanda na faɗi bansan ina kaina yake ba saidai na gannin da yankakkin ƙafafuwa.

     Bansan Sultana ba ina jinya aka ajiyemin kwalba da waya , na kira Malamin na bashi shi kuma malamin ya kira Bello ya bashi bayan sunyi ciniki ya ƙara masa akan farashin da ita matar data bani ya maida ma Bello kwalba , bansan Sultana tana auren Dikko ba , abinda yasa kuwa na koreta daga wurin nace mata bana san matsala ta sake shigowa rayuwata dan bansan ita kuma abinda rayuwarta ta dosa ba……….

Lahaula wala kquwwata illah billahil ‘aliyyul azeem Dikko ya furta suna fita daga cikin gidanshi ya dawo daga sumar da yayi , a ɗiymuwance yace ina ne nan ina kuma zamuje ? Kallon kanshi yayi sannan ya kalli inda aka kwantar da kujerar gaban mota Sultana kwance , laluba aljihunanshi yayi sannan yace ina wayoyina ? Ya tambayi Ashiru , ban ɗauko ba , to koma , da rubos Ashiru ya koma har ƙofar get in gidan , yana tsayawa Dikko ya fita da sauri yaje ya ɗauko wayoyin ya dawo , yana shiga mota ya kira waya , bayan an ɗauki waya yake sanar da M D in asibitin yana da maralafiya suna zuwa babu jimawa dan a shirya ma zuwan nasu , ya kuma faɗa masa abinda ya faru , na cikin wayar yayi magana shi kuma bai sake magana ba ya tsinke kiran , kallon Sultana yayi yaga tana ciccire² ko fizge² kawai dai { Convulsion } salati yayi tare da cewa kai bi tacan , da sauri Ashiru ya juya sitiyari yana cewa Dady yace mu haɗu dashi gida , Dikko yace ba gida ba takamin motar nan da gudu kayi ta can yana nuna mishi hanyar da zaibi da hannunshi idonshi yana kan Sultana , gudu Ashiru yake falfalawa amma Dikko cewa yakeyi kaje ׳……………. Ƙannenshi “yan ɗayan ɗakin dake binsu suna ganin Ashiru ya canja hanya suma suka bi bayanshi da gudu kamar yadda suka ga Ashirun nayi.

  Dikko yana tsinke kiran M D ya kira doctors team on call su tanaji ɗaki a amenity DK yana zuwa da mara lafiya kuma su shirya ma zuwan mara lafiyar da zai kawo.

     Cikin ƙanƙanin lokaci suka iya asibitin ƙashi kuma har yanzu Sultana bata daina fiffizgewa ba , tuni an shirya ma zuwansu a saman ɗan gadon da ake ɗaukar marasa lafiya aka ɗorata aka shiga da ita cikin accident and emergency ,

    Taimako na farko da aka fara bata allura akayi mata diazepam dan dakatar da wannan fiffizgewar da takeyi , cikin mintuna 3 gaba ɗayan jikinta ya saki ta daina ciccire² a mintuna biyu da suka sake bugawa ta ɗauke gaba ɗayanta wato ta tafi bacci…..

     Daga A & E aka wuce da ita amenity nan aka bata ɗaki , cike da tausayi Dikko yabi Sultana dake kwance a saman gado da kallo mai nuna da yana tausayinta sannan ya juyo ya kalli Ashiru dake bashi waya Dady yana kiranshi , ansar wayar yayi sannan yace ma “yan uwanshi suje waje , tashi sukayi suka fita har Ashiru , magana yayi da mahaifinshi bayan ya gama ya zauna a gefen gado ya riƙo hannun Sultana yana shafa fuskarshi dashi , da hannunshi na haggu kuma yana shafa gefen fuskarta ya tsareta da kallo yana mai addu’a ubangiji ya taƙaita wahala yasa An mata karta samu damuwa , likitoci suma kuma suna jiran farkowarta su ɗauki BP { Blood Pressure } nata sai ansan abinyi……..

          A hankali ya mayar da hannun nata ya ajiye tare da cewa wannan fa shine wauta bugun mace da mangariba , wayarshi ya ɗauka yana ƙara kallon hoton da Yazeed ya turo mishi shida An mata , yayi rantsuwa kuma ya ɗauki alƙawari da zuciyarshi Al ‘ Ameen Yazeed da Suwaiba idan ya barsu sun huta bai yafewa kanshi ba , Allah dai ya bawa An mata lafiya…………





01/12/2019 ????????



*JAMILA MUSA…* ????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button