JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka yake yaqarsa ya danni zuciyarsa a hankali wutar sha’awarta take ruruwa a zuciyarsa har ya kasance idan baiji ko ganta ba yakan rasa nutsuwarsa gabadaya akwai ranar da baya mantawa ya dawo Yana kwance a falo itakuma tana kitchen kasancewar yanzu batada aiki saidai tayi masa list na kayan girki wai ya siyo mata girkin yan gayu take koya gurin Maman Humaida to shima dake dan zuga gwaiwa ne ta hau qaya haka zaije ya lodo mata duk abinda ta buqata.
To yau dinma hakance ta faru takanas saboda siyayyar ta ya dawo yana bata ta fice a gdan bata shigo ba sai gaf da magrib gabadaya hankalinta yayi gaba tama manta da Baffa’am din nata yana gidan tana shigowa ta yage hijjab din ta jefar daga ita sai towel din da bai rufe mata cinyoyinta ba wani shocked ne ya hadu a jijiyoyinsa lkcn data kunna hasken daya kashe na falon yabi santala² santalan cinyoyinta da kallo yanajin tsartsatsin wutar azabar feeling yana bijiro masa.
Juyowar da zatayi suka hada ido taja baya da sauri tace “lah Baffa’am dama kananan” bai iya bata Amsa ba saboda yanayin da yake karba ya wucce tunani bin sassan jikinta kawai yakeyi da kallo abubuwa suna bijiro masa wawuyar kam bata gane komai ba tazo ta zauna kusa dashi tace “yau shinkafar zuma Mmn Humaida ta koyamin da miyar qwai Baffa’am in kawo maka zakaci?” Tana mgnr tana maida hankalinta garesa idanunsa daya jima da lumshewa tun zamanta ya bude akan qirjinta ya janyesu zuwa kan fuskarta suka shiga cikin nata sun wani qanqance sun kada sunyi jawur hakan yasata saurin zamewa takai hannunta cinyarsa tace “Baffa’am bakada lfy ne?”

Janye hannunta yayi cikin yanayi na dimuwa da tashin hankali ya miqe zaune gabadaya tsigar jikinsa ta gama tashi tana jorner masa hannunta sai yaji kamar ta ninka masa yanayin da yake ciki idanunsa suka qara qanqancewa jikinsa har wata rawa yakeyi shi kansa idan ya shiga irin wannan yanayin tsoron kansa yakeji da sauri ya miqe yabar gurin zuwa dakinsa saboda saqar da zuciyarsa takeyi masa ba mai kyau bace, ci gaba da ganinta a haka zai iya janyo afkuwar komai, tunda Allah ya hadasa da ita yake addu’ar kada Allah ya kawo ranar da hankalinsa zaikai gareta harma yaji wani abu game da itan Amma Ina ya makara.
Key yayiwa dakinsa ya fada katifarsa cikin yanayi na gushewar hankali ya rinqa miqa Yana shafa mararsa zuwa twins dinsa yana danna saman dick dinsa a hankali tare da mulmula kanta yana nishi Yana jan numfashi, ya dauka dogon lkc a haka kafin ya samu relief ya sake gyara kwanciyarsa rigingine Yana mayar da numfashi zuwa lkcn ya fara azabtuwa da feelings Yartasa tabbas idan yaci gaba da kadaicewa tsakaninsa da ita to kuwa zaayi abin kunya wanda baya fata burinsa bai wucce yaga ya samu damar aurar da ita da qimarta ba zaiji kunya zaiyi kaico ace shine ya zama silar lalata amanarsa da Allah ya dauka ya bashi.
Juhud ta jima a tsugunne a gurin tana tunanin abinda damun Baffa’am din nata duk jikinta yayi sanyi ko kadan batason taganshi cikin yanayi daba na walwala ba, miqewa tayi ta shige dakinta ta Sanya rigarta ta zauna tayi tagumi tana tunanin halin da Baffanta yake ciki miqewa tayi ta fita ta nufi dakinsa ta qwanqwasa ta jima tana bugawa kafin taji an murda qofar an bude ganinta a tsaye yasashi furzar da iska yace mata.

“Ya akayi? Yanayin da yayi mgnr yasata dagowa tayi saurin sunkuyar da kanta bazata iya kallon idanunsa ba yau bataga alamun rahama a tattare dashi ba, tsawa ya daka mata data sanyata ja baya da sauri tayi qwalqwal da ido hawaye ya balle mata ya cafki hannunta yace “ba mgn nakeyi miki bane?” Cikin in…Ina da rawar murya tace “bansan laifin da nayi maka ba Baffa’am am don Allah kayi hqr bazan qara ba banason ganinka da fushi bayayi maka kyau….” Yanda ya kafeta da idone yasata katse maganar ta zauna a gefen katifar ta kama shusshura qafa tana kuka, abin ya bashi dariya yarinyar kullum qara sangarcewa takeyi ya lura shagwabarta bata tashi sai taganshi cikin yanayi kawai ta mayar dashi wani qaramin yaro shima Kuma da sakarci sai biye mata yakeyi.
Ganin da gaske takeyi ba shiru zatayi ba indai ba rarrashinta yayi ba yasashi zama yace “to me kikeso nace miki ne na fada miki banason kina zama tsirara ki rinqa suturce jikinki Meenah kinqi gani kikeyi kamar takura miki nakeyi haba don Allah kasheni kikeson yi ko?” Dagowa tayi da mugun sauri tace “kisa Baffa’am nidin?” Daga mata kai yayi da karsashi yace “Yeah indai kikaci gaba da nunamin kanki a yanayin da kika zomin yau zan hadiye zuciya na mutu ko Kuma naje nakai kaina gurin yan boko Haram su kasheni Kinga kin huta sai kiyi rayuwarki ke kadai…….” Baiyi aune ba yajita a jikinsa ta maqalqaleshi tana kuka tana cewa “ka daina fada Baffa’am banason ka mutu ni ka daina Allah na daina kaji?”

Sosai yaji yanayi a jikinsa tabbas lkc yayi daya kamata ya nisanta kansa da Meenah shaidan ya fara galaba ga zuciyarsa falsafa tana neman qwace masa dole ya nemi wata mafitar, janyeta yayi yace “shikenan na daina cewa kema ki daina tashi kije dakinki ki kwanta dare ya fara Saida safe” miqewa tayi har taje bakin qofar ta dawo tace “bazaka mutu ba ko?” Jinjina mata kai yayi yana kallonta tayi dariya ta fice ya miqe ya rufe qofar ya dawo ya zauna Yana tunanin mafitarsa ta gaba.
Wayarsa ya dauka ya lalubo number mahaifinsa bugu biyu ya daga cikin barkwancinsa yace “soja marmari daga nesa yau ranar tunawa da iyaye ce ta duniya kenan?” Murmushi yayi a kunyace shi kansa bazai iya tuna rabon da ya Kira mahaifin nasa ba kusan tun farkon dawowarsu Maiduguri daya kirasa yake fada masa yayi masa mata a daura yar sarki Badamasi yayansa me rasuwa tun ranar ko Mai martaba ya kirasa baya dagawa shi a dole yayi fushi,
Ajiyar zuciya yaja yace “dama wata alfarma nake nema gurinka Abba don Allah karkace aa nasanka me tausayi da jinqai ne kai Kuma nasan idan kaji zaka jinjinawa qoqarina wajen ceton rayuwa da nayi” murmusawa Mai martaba yayi yace “inajinka Abdulrasheed meye Kuma ya faru?” Nan ya zayyanewa mahaifin nasa komai a qarshe yace “so yanzu wata tafiya ce ta tasomin zuwa Benin shine nake neman amincewarka na kawota nan gida Katsina suci gaba da rayuwa dasu Ya’isha da Amrah Abba inajin yarinyar a cikin jinina banson wani abu ya taba martabarta shiyasa kaga inata takatsantsan wajen kiyaye amanarta” shiru Mai martaba yayi Yana nazarin kalaman dannasa can yaja fasali yace.

“Kayi ganganci Rasheed ka zauna da yar Amana dagakai sai ita Ina tunaninka ya tafi da tun farko bakaji a ranka Bari ka kawota cikin yan’uwanka ba haba Son wannan tunanin naka na quruciya yaushe zai barka kawai ka dauki yarinya kuyita yawo a daji babu lissafi haka, shi da da dukiya ai na kowa ne Allah kadai yasan me morarsu sannan shi riqon maraya alkhairansa yawa gareshi, yanzu kam dare yayi Amma gobe lallai ka taho da ita itama zatafi samun sakewa cikin yan’uwanta mata”
Dadi sosai Rasheed yaji ya miqe yace “ok Abba na gde sai kajimu” kashe wayar yayi ya fita daga gdan bashi ya shigo ba sai wajen daya na dare da kaya niqi² ya ajiye a falo ya shige dakinsa ya kwanta, batasan bikin da akeyi ba tun asuba ya tashi cikin bacci taji ana buga qofar ta tashi ta bude masa baiko kalleta ba yace “kije kiyi wanka ki shiryo tafiya ce ta sameni ta gaggawa zan kaiki Daura zaki zauna a gdanmu nasan zaki samu sakewa fiye da nan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button