JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Sallallamin da suka jiyo a falon ne yasasu miqewa da sauri ya bude qofar ya fita ta rufansa baya sukaja baya da sauri sukayi turus ba itaba shima Saida ya firgita da ganin dogon gadon na daukar gawar asibiti a falon suka kalli juna lkc guda qirjinsu na bugawa da qarfi gadone guda biyu kowanne jini ke diga a jikinsa gadai mutane fal dakin Amma an rasa Wanda zai bude gawarwakin shigowar Alh Aminu ce tasa kowa zubansa ido ya nufi gadon farko ya janye mayafin fuskar gawar ta bayyana nade da bandeji Juhud ta dafe qirji da sauri tana furta “Innanillahi wa Inna ilaihir raji’un” Ba kowa bace face “Aunty Zulaihat kwance sambal babu rai a jikinta sai ta biyun Ado drive ne shima rai yayi halinsa, nandanan gurin yayi tsit Mom taja wata doguwar ajiyar zuciya inda Rasheed ya dubi Juhud itama shi take kallo babu wani gigitaccen alhini a tare dashi saima shafa gemunsa da yakeyi ya juya ya fice daga falon da sauri.
Matsawa tayi kusa da Addah Abulle tace “ina Ya’isha da Amrah?” Dafa kanta tayi tace “suna asibiti Amrah ce taji jiki sosai karaya uku sai Yayanku Kareem da suka dauko a airport shima yananan sai abinda hali yayi Ya’isha kam dressing kawai zaayi mata zuwa gobe ma zaa iya sallamarta….. Tunda ta ambaci Kareem jikinta ya dauki rawa cikin kuka da rawar murya tace “ya….ya taho batare daya sanar da kowa ba Addah shima mutuwa zaiyi kenan don Allah kice kada ya mutu……… Tana fadin haka wani amai ya taso mata me qarfi tayi qasa da sauri ta fara sheqashi Addah ta rirriqeta tana aman kamar zata amayar da hanjin cikinta daqyar suka samu ya tsaya sukayi hamdala Addah Abulle tajata daki tace “ki nutsu ki kwantar da hankalinki insha Allahu babu Wanda zai Kuma mutuwa ki kwanta ki huta ke dama ba isasshiyar lfy ba bari a gama sutarar wadancan sai azo a dubaki”……..

Oum Hairan
[7/24, 3:02 PM] Oum Hairan: JH018littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki

Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566
Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde

Masu fitarmin da littafi kunajamin zagi kuyi ku da Allah keda kika karanta baki biyani haqqina ba kike zagina kema haka????????.
Tun kafin na fara rubuta littafin Juhud nayi bayaninsa 50% is true so nasan inda lbrna ya dosa duk wani abuda zan rubuta zanyi shine daidai da abinda yake true bazan karkace daga wannan bigiran ba am sorry masu cewa ya kamata Kareem ya mutu da masu cewa Banyiwa Rasheed adalci ba baikamata yazama silar lalacewar Juhud ba. Duk wannan ba kwaskwarima ta bace abune daya faru da gaske banida ikon canzashi????.

Tunda ta kwanta jikinta ke rawa zuciyarta take tashi zazzabi me zafi ya rufeta hakanan ta wanzu a dakin hawaye nabin kuncinta tabbas Allah shine buwayi gagara misali yanzu duk irin tanadin da Zulaihat keyiwa aurenta ashe batada rabon kasancewa da mutumin da takewa tanadin tausayin kanta ya kamata a fili tace “Allah na tuba Allah” sai Tara na dare aka dawo daga suturarsu Aunty Zulaihat mutuwar ta Sanyaya jikin kowa Zulaihat mace me shiga rai me hqr da daukar duniya baa bakin komai ba ta wucce sai labarinta.
Koda suka dawo Juhud tanajin Mom da Addah suka shigo tayi likimo kamar me bacci Mom ce ta taba jikinta tace “inajin zazzabin nan nata ne me zafi ya sake dawowa Allah dai ya yaye dare yanzu yayi Dr Razaq yana asibiti saidai zuwa safiya sai yazo ya dubata” juyawa sukayi suka fita taja fasali ta gyara kwanciyarta itadai ranar bata rintsa ba ga zazzabi ga radadin zucci ga babu abokan tattaunawa, washegari da asuba Mai Martaba ya kirasu dukkansu bayan anyi addu’a yadanyi shiru na lkc kana ya Dora da cewa “haka Allah yake ikonsa ubangiji ya jiqan wadanda suka mutu”

Amsawa sukayi da Amin ya sake duban Juhud yace “naso na daura aurenki da Kareem koda kuwa bayan an daura zai mutu ne so shi ya buqaci abari ya samu lfy tukunna inyaso sai a hada dana yan’uwanki to Alhmdllh hakan ma yayi saboda haka zan daura auren Rasheed da Hidaya qanwar Zulaihat a yau dinnan a masallacin fada insha Allahu kowa zai iya tafiya” idanun Rasheed nakan Juhud ta miqe zatabar gurin taji yace “Mai Martaba ka hqr da yimin aure na fada maka ba aurene banaso ba hasali na fada maka muradina ka karba kabani abinda zuciyata takeso zaifi Mana kwanciyar hankali dukkanmu”
Ficewa tayi batare da sanin wainar da zaaci gaba da toyawa ba ta nufi cikin gdan daidai lkcn da Muntaz suka shigo da Ya’isha ta tareta da sauri suka rungume juna suka fashe da kuka Juhud tace “ina Amrah da Ya Kareem Ya’isha?” Numfashi ta sauke tace “ya Kareem da sauqi fah sosai don yanzu ma da zsn taho Saida yace na gaisheki damuwarsa kece yace kada ki sawa ranki damuwa komai zaizo da sauqi da yardar Allah”
Wata ajiyar zuciya ta sauke me qarfi tace “anjima zanje na ganoshi in naji jikina da sauqi” dubanta Ya’isha tayi tace “wai har yanzu jikin ne ke nifa Ina tsoron wani abu Juhud Anya ba cikine dake ba?” Dafe qirji tayi tace “na shiga uku ni Aminatuh Ina zan samu ciki?” Murmushi tayi tace “kina tunanin takunki da Ya Rasheed zai boyemin ne wlh karki sake kiyi ciki ki shiga ukun da gaske donshi namiji babu ruwansa”

Kallon Ya’isha takeyi da mugun mamaki tace “Karkice komi wlh tun ranar farko na fahimci shine yayi barnar da kike cewa baki saniba yasan nasani har kirana yayi yayimin kashedin idan wani ya sani bayan Ni to na kuka da kaina hakan tasa nayi shiru na zubanku ido, takun naku salon Yana birgeni sosai saidai inajin tsoron bacin rana fah” fasali Juhud ta sauke tana neman gurin zama tace “idan hakan ta kasance ya zanyi ta Yaya zan gane inada ciki?” Matsowa Ya’isha tayi tace jikina duk ciwo yake Bari nayi ruwan dumi nazo mu fita musan abinyi” shigewa tayi bathroom ta sakarwa kanta ruwa ta jima sannan ta fito tace “naga tashin hankali jiya tabbas Allah ne yayi da kwanana a gaba nice fah a gaban mota Ya Kareem da Amrah da Zulaihat suna baya kawai saiji mukayi kamar an daga motarmu anyi sama da ita an dokata jikin wani dutse Wai ashe tayace ta cire nidai ban qara sanin meye ke faruwa ba Saida na farka naganni a gadon asibiti ake cewa motar tana dira qasa murfin ya bude da gangara daji daqyar aka laluboni sukuma tayita qoli dasu har saida masu qararren kwanan suka mutu sannan ta kife aka debi Amrah da Ya Kareem akayi asibiti dasu zuwan Mai Martaba ne ma yasa akan da wata bayan Amrah da Ya Kareem shine suka bazama nemana suka tsintoni a cikin wani rami”
Da wannan ta gama shiryawa cikin wasu riga da wando ta dora doguwar riga suka fito Juhud na riqe da key din mota a hannunta suka Isa parking space din suka dauki motarsu suka fito daga gurin a harabar gdan suka hangi Rasheed zaune can nesa da yan zaman mokokin yana kada key a hannunsa saurin zuge glasses din motar sukayi suka fice Ya’isha ta tabota tace “guy dinnan takunsa na bani citta…..”

Juyawar da zatayi taga motarsa a bayansu tace “mun shiga uku Meenah yi kwana shiga layin layin Bashar muje shop Ya Rasheed ya biyomu” zuba idanunta tayi akan mirrow din ta zuge glasses din suka hada ido ya daganta gira ta hade rai Yana biye dasu sukayi parking suka fito shima ya fito ya harde jikin motarsa yana kallonta ta fito tana gyara mayafinta fuskar nan kamar an aiko mata da mala’ikan mutuwa suka shiga Mall din a zahiri ba siyayyar ce ta kawosu ba Ya’isha ce ta sace jiki ganin ya shigo Yana duba wasu dogayen ruguna ta samu ta nufi Pharmacy din cikin Mall din ta siyo tsinken test na ciki da wani qwaya da ake Kira Messofem ta hado mata da Vitamin C cikin aljihun wandonta ta zuba tarkacen ta sako audugar mats cikin ledar da multi-Vitamin ta nufo Mall din lkcn ya qaraso inda Juhud ke zaban mayukan shafa ya tsaya a bayanta tanajinsa ya Dora hannunsa saman bombom dinta ya sauke ajiyar zuciya ya kwanto da kansa kafadarta yace.
“Meye kike son siya ne kin kasa daukar komai” zuciya taja ta juya zata tafi ya riqo hannunta ya daganta gira yace “zan samu ganinki?” Murmushin takaici tayi ta juyo a fusace tace “na tsani mutum me naci wlh a rayuwata kai Wai bakada aiki sai baqin naci nifa Baffa’am ka takuramin ka hanama rayuwata sakewa wai ya kakeso danine……”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button