JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Qit ya sanqame layinsa ya zubawa wayar ido cikin tashin hankali shikam yaga ta kansa a duniya kamarshi ya hada mata biyu ta yaya zaima fara zama da Hidaya bayan bayasonta meyesa bazasu qyaleshi da muradinsa ba wannan wanne irin qarfa² ne? Takun da yaji ta bayansa yasashi juyawa suka zubawa junansu ido kowa da abinda ke ransa kafin daga bisa Juhud ta janye idanunta daga garesa cikin sanyin yanayi tace “Ina kwana” daukan tea flast din yayi ya nufota ya miqa mata yace “na tashi lfy Amma ban riski yinin lau ba” da rashin fahimta ta dubesa yaja numfashi yace “kome zaayi babu me rabani dake Meenah inasonki wlh kin kasa ganewa don Allah ki cire kowa a zuciyarki kisani nine ya kamaci kibawa kyautar zuciya” wani gwauron numfashi ta sauke ta juya ta fito falon ta aje tea flast din ta juya zata tafi yayi saurin shan gabanta yace “waike wacce irin zuciya ce dske ne….”
Hannunta ta Dora a bakinsa ta dago idanunta da suka ciko da qwallah tace “ina tuna Alkhairanka na baya gareni inajin tausayin kaina dakai banso muka riski kanmu a halin daka jefamu ba zuciyata tafi aminta da nabarka na nemawa kaina wata mafitar saboda zamana dakai akwai matsala….”

Tunda ta fara mgnr ya zubanta ido har ta gama sannan yaja kujera ya zauna ya fara hada tea din bayan ya hada ya miqa mata zatayi masa gardama ya dakanta tsawa dole ta nutsu ta karba tanasha daqyar bai sake kallonta ba har ya gama ya haura sama ya sako kayansa ya fice tanaji ya kulleta a gdan, ta zauna tanata kukanta daya zame mata jinin jiki Saida bacci ya dauketa sannan ta hqr ta kwanta a falon tayi baccinta isasshe. Yammaci har dare bai dawo gdan ba ta cika da tsoro gashi ya karbe wayarta batason yasan da wata a hannunta shiyasa ta kasa kiransa tananan zaune a falo har goma ita dama gata matsoraciya hakan dole ta tashi ta haura sama ta rufe ko Ina na gdan tana cike da tsoro bacci ya dauketa.
Washegari ma hakanan ta yini sur har dare bai dawo ba sai Daren ne Ya’isha ta kirata take fada mata ashe Katsina ya tafi yaje ya tashi hankalin gdan sarautar akan aurensa da Hidaya duk wani Wanda yakejin ya isa yayi masa mgn yaqi ji yaqi gani qarshe ma cewa yayi don wannan banzar kucakar akeson daga masa hankali to taje ya cike saki ukun inda me magana yayi. Yana fadin haka ya fice Mom ce tayi qarfin halin tsaidashi da cewa “amma lallai Abdulrasheed kakai da mara neman albarka mahaifinka yayi maka zabi kace bakaso harma ka yanke wannan mummunan hukuncin akai” dagowa yayi idanunsa cike da qwallah yace “bayin kaina bane Mom zuciyata tana fadamin bazan taba iya hada soyayyar life dina da wata ya mace ba a duniya saboda haka yasa na yanke wannan hukuncin da azo ayi abun da zaa rinqa wlh tallahi gara tun farko kada a fara”

Yana fadin haka ya juya zai fita Mai Martaba yace “nasan abinda yake rudarka ka zabi mace sama da ni dana haifeka na dauki dawainiyarka har zuwa lkcn da ka girma ka zama mutum ka tsintota a daji ka mayar da ita mutum tsayin lkc kana tare da ita duk wani motsinka da nufaqarka akan Juhud na fahimceshi daga ranar daka kawota gdannan kawo lkcn da dauketa ka lalata mata rayuwa ka massheta mata a gurinka ta hanyar zuwa a dauranka aure da ita batare da neman izininta ko yardarta ba, duk kallonka nake har zuwa lkcn data samu ciki suka fita domin zubarwa da binsun da kayi ka saceta ka boyeta dukka Ina kallon irin naka wayon ne Rasheed ban hanaka cigaba da rayuwa da Aminatuh ba Amma kayi sani na rantse da ubangiji daya Mara abokin tarayya mun sanya qafar wando daya dakai muddin nine ubanda ya haifeka kamar yanda ka furtawa Hidaya saki uku itama Meenah saika saketa daidai da hakan idan kaqi Kuma ka nunawa duniya ta hanyar cemin bazaka iyaba”
Kalaman na Mai Martaba sunyi mugum dukan zuciyoyin duk wadanda ke gurin Amma Banda Rasheed da yake latsa wayarsa Captain Salman yayansa ya matso gabansa ya daukeshi da wani gigitaccen mari daya sanyashi lumshe idonsa ya budesu akansa maimakon yanayi na damuwa saima juyawa da yayi ya fice Mom da Addah Abulle da Dr Arman yayansa suna kiransa tare da biyo bayansa Mai Martaba ya daga murya yace “duk Wanda ya fita to karya dawo shima na cireshi cikin yayana……”

Wani mugun tashin hankali Juhud ta shiga Wanda rabon data risketa a cikinsa tun lkcn mutuwar Innatu tace “Innanillahi Wa Inna ilaihir raji’un Ya’isha don Allah da gaske kikeyi meye yake damun Baffa’am ne komansa daban dana mutane meye yake nufi da fitowa ya baro gdan batare da lamuncewar Iyayensa ba…..” Numfashi Ya’isha ta sauke tace “tabbas kekam kina ruwa gaban breaker yasaki cikin wani yanayi domin tunda ya sakai ya fice a gdannan Mai Martaba yake saba da marwa babban abinda yafi komai dagawa kowa hankali yanda yaje aka daura muku aure batare da kowa yasani ba Mai martaba yace “wato shi bai dauki kowa da muhimmaci ba cikin rayuwarsa kawai abinda zuciya ta saqa masa shi yakeyi kiyi bakin qoqari wajen ganin kin saitashi tunda qaddara ta hadaki dashi babban tashin hankalin ma dazun nan fah mukayi baqin wasu Fulani sunce abinda ya raboki da rugarku Moddibon rugar kika kama kika cinye shine yan’uwansa suka sanyawa bukkar da mahaifiyarki take jinya wuta ke Kuma suka biyoki zasu kasheki Kuma fah kowa ya amince da wannan labarin harma Mai Martaba yayi rantsuwar babushi babu Ya Rasheed muddin be sakeki kin qara gaba ba Addah Abulle ce me cewa ita Allah ya rabata da qaya da tuni danta da takejin dadi dashi ya zama sorry, Mom kam har yanzu ta kasa cewa komai sai hawaye da taketayi na tambayeta meye dalili tacemin “Ya’isha sharrin maita yanada ciwo anyima qanwar babana sharrin maita ta mutu da wannan baqin cikin anyiwa yayata sharrin maita tun daga cikin gdanmu Ayshatu ta tashi da wannan ciwon a ranta ta sake samun dangin mijin da basa qaunarta aurenmu na Fulani suka hanata shiga dangi bata zuwa Mali kawai saboda sunce danginta mayune wannan dalilin yasa ta bata a dangi bamu santa ba tun tana qarama dama uwarta tabar gidan babanmu da ita tun suna Senegal Saida ta Isa aure aka aurawa wani bafullace ita ya tafi da ita daga nan bamu sakejin duriyarta ba har kawo yanzun. Ya’isha idan Juhud ta kasance yanda ake tunani to tabbas tana cikin hadari idan Kuma ta kasance akasin haka to tafi shiga hadari domin kuwa duniya zatayi mata qunci zata rasa tudun dafawa ga maraici ga qiyayyar dangin miji nikam banso Rasheed ya auri yarinyar nan a haka ba naso yayi aure me yanci da ita wlh inasonta a cikin jinina Kuma Ina tausayinta”

Tunda Ya’isha ta fara mgnr Meenah ke wani irin kuka me ciwo tanajin tausayi da tsanar kanta a hankali ta zame cikin kuka tace “inasu Baffa Ribado sukasan inda nake har sukazo suka lalatamin tarihina……” Qwace wayar taji anyi ta dago tana kallonsa tana hawaye, yaja fasali yace “ba laifinsu bane nine naje na nemesu domin su dauramin aure dake, ko ki kasance mayya ko ki kasance akasin haka niba damuwata bace damuwata kawai ki kula da kanki ki kiyayeni nima na kiyayeki. Ke Kuma munafuka da kike kwashe komai kike sanar da ita zanyi maganinki duk ranar dana shigo Katsina…..”
Da sauri Ya’isha ta kashe wayar ya jefata a aljihunsa ya zauna kusa da ita ya riqo hannunta yace “idan ya kasance nine mijinki Kuma na yarda da komai akanki Meenah na yarda na mutu saboda ke to meye Kuma saura dazai dami rayuwarki?” Sosai kalamansa suka shiga jikinta ta fada jikinsa ta ruqunqumeshi tace “zanyi farin ciki da samun masoyin gsky me qaunata domin Allah Mai sona da aibina Amma bazanso ya kasance nice silar lalacewar alaqarsa da danginsa ba musamman iyaye Baffa’am kada ka zabeni saman mahaifanka don Allah kabarni da qaddarata……” Bakinsa yasa ya rufe nata a hankali suka zube a qasa Yana hura mata iska ya zare bakin nasa yasa saman hawayenta Yana lashewa Saida ya tsotsesu tsaf sannan yace “zan tayaki jigila da qaddararki bakin rai bakin fama yanzu ne wasan zai fara Meenah ko kowa zai gujeki Ni zan rayu dake” hannu yasa a aljihunsa ya zaro wata baqar leda ya kunce ta zubansa ido ya tasheta zaune ya zaro abin wuyan dake ciki sai walwali yakeyi ya dubeta itama shi take kallo tace “lahh Baffa’am Ina kasamu wadannan?” Murmushi yayi yace “tun ranar farko dana tsinceki na cire miki shi a qugunki na adana maki su ke Ina kika sameshi?” Sunkuyar da kanta tayi tace “Innatu tacemin na kakata ne da Babanta yabata lkcn aurenta shine data rasu baffana yaci gado shikuma yaketa ajiyarsu gareni har zuwa lkcn da ajalinsa ya riskesa ya samqawa Innatu itama ana gobe zata rasu tabani su Ni nama manta dasu badan yanzun ba”……………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button