JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL
Gabadaya hankalin gdan sarautar Babu na kwance wannan baqon alkaba’i daya fado musu Babu zato ya girgiza zuciyar kowa a gdan daga yara har manya hatta wadanda ke nuna adawarsu irinsu Hajiya Bilki a zahiri suna nuna alhininsu tare da jefar da maganganu na zargi a fakaice suna alaqanta batan nasa da Juhud da take kwance cikin halin jinya bata kwana uku da lfy saboda tashin hankalin da take ciki duk ta qare sai qasusuwa gashi kullum lkc qara tafiya yake babu wani amon labari tun daga sama ga manyan sojojin da suka baza idanunsu a kowanne lungu na Africa domin ganoshi zuwa gwamnati da itama take hobbasa wajen ganin an samo bakin zaren saidai kullum labarin daya ne baya canzawa daga inda yake.
Malamai kuwa da suke aiki da addu’ar Allah ya fito dashi sunfi dari suma kullum amsar daya ce a qara hqr lamarin daya Sanya Juhud a wani hali ga shayarwa gashi ko abincin bata iyaci dole tasa sarki yanada shekara daya da wata hudu Mom tayi masa yayen dole aka dorashi akan abinci aka qyaleta da damuwa daya gabadaya ta quntata kanta kullum bata da aiki daga sallah karatun qur’ani sai kuka
Mai Martaba da yayansa maza musamman Kareem daya dawo daga Saudia ya gama karatunsa kullum basa Kano basa Abuja basa Lagos Basu kotono Basu Togo Basu Burkinafaso tafiya kullum qara miqawa takeyi Abu ya tafi shekara guda, watarana suna falo suna zaune Meenah na rungume da Sarki junior Amrah da Fadila suka shigo suka zauna aka gaisa suka jajantawa juna Dada Hanne dake zaune ta rafsa tagumi ta dago tana kallon Juhud tace “lamarin nan da ban mamaki Mahfuz batan Abdulrasheed kamar batan toka a ruwa gsky abinnan da lauje cikin nadi Anya ba mutuwa yaronnan yayi ba”
Duk Wanda ke falon Saida ya dago karma Juhud taji labari da kaduwa tasata zamewa daga kujerar ta sauko qasa tayi dabar tana kallon Dada Hanne. Harara ta watsa mata tace “eh Mana biri yayi kama da mutum to nidai tunda abinnan ya faru nake biyar malamai da yan bori idan suka hau bori suka jirge sai suce ai saqale kurwarsa akayi akayi bandarsa” gabadaya hankalin kowa sai ya dawo kan Juhud da itama take jujjuya mgnr a kwakwalwarta Dada Hanne tace “kuma fah cewa sukeyi makusancinsa ne yayi masa wannan abin kawai saboda yanason cin gado to nidai naga kaidai Mahfuz bazakayi wannan abu ba itama Mom din yara bazatayi ba saura da me dama Kuma ku hudune magadan nasa…..”
Miqewa Kareem yayi yace “don Allah dakata Dada kada kizo Mana da surkullen hauka cikin wannan lamari ke Ina kika taba ganin anyi bandar mutum banda sakarcinku na mata? Kuma ma meye Rasheed ya Tara da har zaayi tunanin kasheshi don gadonsa haba dallah ku rinqa auna mgn kafin kuyita Mana” Yana fadin haka ya miqe zumbur ya dubi Addansa daketa harararsa ya dubi Mai Martaba da Mom yace “wlh daukan alhakin Meenah zakuyi indai kuka zargeta yarinyar nan batada wani abu da ta sani game da batan mijinta haba ai abinda zai yuwu ma dagaji ansanshi” ficewa yayi daga gdan idanunsa nakan Meenah da keta jan zuciya tunda mijin nata ya bata take cikin masifa komai Yana neman koma mata baya gdan an qara tsangwamarta da Mom kawai takejin dadi sai Kareem daya mayewa Sarki junior madadin bsbansa komai ya tarkato Sarki.
Ana haka Mai Martaba yaga zaman ya fara tsayi Abu ya tafi shekara biyu ya Sanya Kareem ya nema mata admission bayan sun biya mata an zana mats jamb lkcn da sukayi mata mgnr karatun fir qi tayi tace ita bataso daqyar Mom da Kareem sukasha kanta ta yarda ta fara zuwa Alqalam University Katsina bata jima da fara zuwa ba abubuwa suka fara canzawa Dada Hanne da Alh Aminu suna zuga Mai Martaba baiyi furuci ba Amma gabadaya ya janyewa Meenah tallafi babu Wanda yasan dalili Mom ce taci gaba da dawainiya da karatun nata ita da Kareem.
A hakadai da dadi babu dadi take gurgura karatun cike da samatsi da qalubalen rayuwa kullum addu’a takeyi Allah ya bayyana mijinta itama ko ta samu hasken zuciya. Yau da gobe ce tasa Kareem bawa Mom shawarar kama mata hostel saboda karatun nata na Law yanajan kudi sosai hakan kuwa akayi suka kama mata hostel ta koma can da zama Sarki junior na gurin Mom yanata girmansa inda a lkcn Ya’isha ta ta haihu Zahran Kareem ma ta haihu taso zuwa daidai lkcn suna exam hakanan ta hqr sai bayan Exam akayi hutu ta shirya domin zuwa tayi barkar ta nufi Daura cike da kewar gudan jininta da sallamarta ta shiga falon Sarki ya taso da gudu ya rungumeta ta dagashi tana juyashi suna dariya tayi kissing nasa tace “miss you love inata kewarku”
Lakace mata hanci yaran me shekaru hudu yayi yace “yaushe zaki dawo?” Narkar dakei tayi tace “saura semester guda Son ka matsu na dawo ne?” Turo baki yayi yace “Addah Fadila ce tacemin na daina zuwar mata gidanta kada na cinye mata su Jabir Momy wai tace kece kika cinye Dad Ina ya bata…..” Gwabe bakinsa Mom tayi tace “ba nace maka idan na qarajin mgnr nan a bakinka saina yankaka ba” riqe bakinsa yayi alamun yayi shiru ta daukeshi jikinta a mace ta nemi guri ta zauna suka gaisa da Mom ta miqe tace “zanje nagano babyn Ya’isha” miqewa itama tayi tace “nima abinda ya kawoni kenan hutunmu na sati daya ne Kuma tun shekaran jiya akayi” dungumawa sukayi suka fita suna fitowa Muntaz na shigowa Mom tace “yawwa zo ka kaimu gdan Ya’isha”
Babu musu yaja suka tafi suna taba yar hirarsu tace “Jiya Hafeez abokin aikin Baffa’am yakaimin ziyara” murmushi Mom tayi tace “nan ms yazo gurin Mai Martaba yazo ne da wani shirme wai qa’ida shekara hudu ne idan mijin mace ya bata alqali zai bata damar tayi aure ke anbaki dama ne? Tsaki taja me zafi tace “shege sai naci kutumar ubansa ni ce masa akayi mijina bazai dawo bane nifa Mom bantabaji a Raina Baffa’am ya mutu ba Yana raye kawai dai Allah ne be gama ganawa ba” numfashi Mom taja tace “nima haka nakeji so naga Mai Martaba ya saduda shiyasa nima na fidda rai da tsammani” shiru ce ta dan gifta suka Isa gdan Kareem ta jinjina haduwar gdan karo ns farko data sanya qafarta a gdan tun aurensa da Zahrah kasancewar Zahra mugum baqin kishi takeyi da ita to itama shiyasa taja jikinta.
Da sallama suka shiga aka Amsa musu Dada Hanne na dagowa taga Juhud tayi maza ta dauke jaririn tasa a bayanta suka gaisa tayima Zahrah barka tana amsawa a yatsine ta aje kayan data siyowa bebin tana satar kallonsa a bayan Dada tanason jariri a rayuwarta bata samu arziqin daukan jaririn ba Kareem ya sauko tunda ya fito idonsa na kan Juhud dake wasa da yatsunta yace “aa Meenah Ina cewa zanzo na daukoki ashe kina hanya” murmushi tayi masa tace “wlh na matsu nazo naga baby’s din da muka samu shiyasa na biyo motan haya” shafa kansa yayi yace “insha Allahu cikin satinnan motarki zatazo haihuwar nan cema ta dan takemin birki” gdy tayi ta miqe saboda bata cikason zaqewa a lamarinsa ba ganin haksn yasa Mom miqewa sukayi sallama ya biyosu har jikin motarsu yanajan Sarki da wasa suks shiga suka tafi shikuma ya juya suka nufi gdan Ya’isha………
Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…
Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..