JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Bata ko kallesa ba taci gaba da wasa da yatsunta yaja numfashi ya fice a dakin suka hade da Mom a reception ya tsaya Yana dubanta da jajayen idanunsa da damuwa biyu tasa suka kada tace “yanzu ake fadamin Zainab ta rasu ya kamata kazo ka tafi kaima tunda jikin nata da sauqi” girgiza kai yayi yace “ban yarda da hankalin Meenah ba Mom zata iyayin komai Ina tsoron kada na tafi tayi tunanin guduwa tabarni wlh mutuwa zanyi a wannan karon Mom ke shaida ce na wahala a karon farko dana rasata don Allah ki tausheta ta soni koda kwatan Wanda nakeyi matane ni basai yakai rabi ba inasonta a haka”

Murmushi Mom tayi me dauke da hawaye ta dafa kansa tace “Abdulkareem to Banda abinka Meenah yanzu ai taka ce kasan dai ba cikakkiyar lfy gareka ba don Allah ka rage damuwa da duk abinda zatayi zai hucce kasan kaima dole zaa fuskanci wannan qalubalen tunda ba ita taga damar auren nan ba Ni kaina Meenah fushi takeyi dani ban damuwa domin nasan gata Mai Martaba yayi mata kaidin dama kaine ka dace da ita Hukuncin Allah ne yabawa Rasheed da Kuma rabon Sarki junior Kuma ma ai tanasonka tun a baya kawai yanayin da take cikine yasa zakaga kamar batasonka”
Murmushi yayi yace “hakane Mom na gde am Dr yace zamu iya tafiya gda nikam zanfi samun nutsuwa tana tare dani” batason jayayya dashi shiyasa ta aminta su tafi din ta shiga dakin ta fara hada musu kayansu Meenah na kallonta harta gama ta dubeta tace “mu tafi mijinki ya matsa saidai mu tafi gabadaya” daqyar Mom tasha kanta ta miqe suka tafi baya ta shiga yana kallonta yayi murmushi sai Mom ce ta shiga gaba suka nufi Katsina da suka isa Daura ta samu ta fita a mota tayi wuf ta shige dakin da take ta fada gado ta rushe da sabon kuka tana tuna wai yau ita ce matar Kareem bata Rasheed ba meyesa qaddararta kullum ita baibai ce a fili tace “lkc yayi da zan nemawa kaina gata dole na nemi su Baffa Ribado ko zasu kasheni su fitomin da dangin mahaifiyata”

Qwanqwasa qofar taji anayi ta miqe ta bude qofar ganin Kareem ne tayi saurin mayarwa ta datse yaja baya da sauri tare da cije lebe ya juya a kasalce ya fice daga gdan ya nufi gdansa babu kowa kamar yanda ya tsammata yayi murmushi ya nufi gdansu Zahrah acan ya tarar da yan karbar gaisuwar bai wani zauna ya dade ba ya nufi gidansa ya kwanta a gado Yana saqawa da warwarewa akwai aiki a gabansa.
Meenah batashi takeyi ba baya a lissafinta ga Addah Abulle ta takura masa da Kira har takai baya daga wayarta saboda yariga yasan mgnrta bata wucce akan qiyayyar aurensa da Meenah tana qara tuna masa tun tana budurwa an hanashi sai yanzu data zama saura ragowa sannan ga rashin asali kalma daya yake fada mata Babu komai Addah inasonta a haka ba meenah ce ta qini ba a farko fin qarfinta akayi saboda hska nima bazan qita ba” idan ya Fadi haka Adda ji takeyi kamar ta kasheshi shima gashi Mai Martaba yaqi sauraronta balle yaji kokenta hasali ma fushi yakeyi da ita wannan tasa ta zare hannunta daga lamarin Kareem din ta zubansa ido tare da cin alwashin indai itace ta haifeshi to Meenah ta gama kwanciyar hankali a duniyarta saisun takurata sun azabtar da ita ita da yan’uwanta babban abinda yake daganta hankali Zahrah yar wanta ce ta nemawa Kareem aurenta don huce haushi yanzun Kuma ya samu abinda ransa yakeso bayama ta ita tunkan tafiyar tayi nisa.

Wadannan dalilan suka hadu sukayiwa zuciyar Kareem yawa abinka da mara isasshiyar lfy nandanan zazzabi ya rufeshi shi kadai a gda yayita murqususun ciwo yana dafe qirjinsa wayarsa ma ya kasa dauka ya kira wani, baa Ankara ba Saida ya kwana shidda yana fama da ciwo shi kadai a gda sannan ubangiji ya kawo masa sassauci a galabaice ya lalubi wayarsa ya Kira layin Zahrah bugu yafi biyar tana gani taqi dagawa ya hqr ya Kira na Meenah itanma yayi mata misscall yafi goma tana kallon wayar taqi ta daga qarshe ma ta kasheta gabadaya ya jinjina kai cikin azabar ciwo ya Kira layin Mom dan yasan idan ya Kira na Addah ma itanma kamar yanda matansa Basu saurareshi ba itama ba saurararsa zatayi ba.
Bugu daya Mom ta daga tace “dan halak kaqi ambato Ina ka shigene inata nemanka bana samunka…..” Nishin da taji yanayi ya fadar mata da gaba tace “ya salam kardai bakada lfy ciwon ne ya tashi Kareem…..” Cikin rawar murya yace “Mom….ki….ki taimaka ki kawomin Aminatuh don Allah kada ta zamo silar ajalina sonta zai kasheni….”
A gigice tace “o…. Ok ganinan don Allah kada ka mutu Kareem mukam mun shiga uku da wannan masifa” kashe wayar tayi ta zari mayafinta ta fice a kidime ta nufi dakin Meenah tana zaune tana koyawa Sarki Homework ta dago ta dubi Mom tace “Lfy Mom?” Sharce gumi tayi tace ”taso ki rakani unguwa”

Babu musu ta miqe ta dauki mayafin doguwar rigarta ta sanya ta kama hannun Sarki suka fito ita kejan motar Mom na fada mata inda zasu tana fahimtar gidan Kareem suka nufa hasken fuskarta ya dauke ta hade rai donma Mom tafi qarfin musu ne a gurinta shiyasa tayi shiru har suka isa gdan suka Mai gadi ya bude musu sukayi parking Mom ta fito itakam gyara zamanta tayi Mom ta dakanta tsawa tace “bafa nason sakarci Meenah ki fito mu shiga nace”
Tana qunquni ta fito suka shiga cikin tun daga falon taji gabanta na faduwa komai a hargitse tabi falon da kallo taja tsaki Mom ta haura saman tabi bayanta tana kallon tsarin gdan bude wata qofa Mom ta Kuma yi qofofi ne guda biyu suna kallon juna ga mamakinta nan dinma falo ne sai wasu qofofin biyu tsayawa Mom tayi tana tunanin wacce zata bude Sarki yace “Mom ga dakin Uncle nan” Yana mgnr Yana murda qofar suka shiga a tare itakam guri ta samu ta zauna a falon tana hura hanci.
Yanayin da Mom ta isheshi yayi mugun tada mata da hankali ta saki wani kuka tace “innanillahi wa Inna ilaihir raji’un Abdulkareem meye hakan kashe kanka zakayi a gda kai kadai” gaban Meenah ya sake faduwa lkcn da Mom ta qwala mata Kira ta miqe a razane ta shiga dakin tare da zaro ido Yana kwance a qasa magashiyan cikin wani mawuyacin yanayi ya bude idonsa ya saukesu akan Juhud tare da sauke ajiyar zuciya ya fara yunqurin miqewa Yana cewa “Am…. Ami…na…tuh zo… matso gareni please….” Janyewa tayi tayi baya idanunta na kansa Mom ta tura ta fada jikinsa ya lumshe idonsa tare da sanya hannunsa ya zagayeta yaja wata ajiyar zuciya me qarfi tana qoqarin qwacewa ya bude bakinsa yace “na…na gode Mom ke kadai kike tausayina a duniya Mom Meenah bata sona….” Juyawa Mom tayi ta fice saboda yanda taga Yana qara matse matarsa a jikinsa abin yabata tausayi da kunya ta lura da Rasheed da Kareem tafiyarsu daya Basu da kunya akan abinda sukeso…….

Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…

Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..

Oum Hairan

[8/7, 7:18 PM] Oum Hairan: 0031 Da qyar ta samu ta janye daga jikinsa idanunsa suna lumshe hawaye yake zubarwa ya riqe hannunta yace “Nayi tunanin kedin me yarda da qaddara ce da hukuncin ubangiji Meenah ashe ba haka bane Meenah ko bazakiji tausayina ki daina azabtar da ruhina don na cancanta ba ya kamata kiji qaina don qaunar da nakeyi miki inasonki ne Meenah da jinina da rayuwata” Yana mgnr numfashinsa ba kakkatsewa hakanan taji bazata iya jure cigaba da kallonsa a wannan yanayin ba ta miqe zata fice ya Kira sunanta ta tsaya ya dauki wayarsa ya miqa mata yace “idan tafiya zakiyi ki kiramin Amrah ko Urwat ko Muntaz wani cikinsu yazo ya zauna dani Ina cikin yanayin da komai zai iya faruwa dani”
Harararsa tayi ta fice a ranta tana cewa “badai ni ka zaba ba wlh saidai ka mutu yanda uwarka da yan’uwanka ke qina haka nima nakeji game daku ban shirya zama da wannan ahlin ba abarni na rayu da zabina koda baya tare dani nasan Ina kwance a zuciyarsa” sauka tayi qasan ta tarar da Mom da Dr Razaq suka dubeta tare sukace “ya me jikin” a gajarce tace “yana ciki” ta juya ta fice ta shige mota shiru dogon lkc ya wucce basu fito ba can taga mota ta shigo Mai Martaba ne da Arman suka shiga suka daukoshi suka fito dashi. A mota suka sanyashi suka fice Mom ta shiga mota Juhud taja suka fita sosai ta qular da Mom da halin ko in kula din data nuna akan mijin nata bata taba tunanin zuciyarta tayi soyewar haka ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button