JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Batasan lkcn da bacci ya dauketa ba a sama ta rinqajin ana taba qofar ta miqe tana miqa tare da yin salati tace “wayene?” Cikin sanyin yanayinsa na dabi’a yace “kinyi sallah ne?” Bata bashi Amsa ba ta nufi bathroom ta watsa ruwa ta dauro alwala ta fito ta sanya doguwar riga ta tayar da sallar bayan ta idar tayi azkhar ta sake zubewa a gurin duk da ba wata hidima tayi a bikin ba tanajin gajiya a jikinta sosai, bacci ne ya sake dauketa bata farka ba sai 10:30pm shima din wayarta ce taji tana ring baqon layine ta Kara a kunnenta yace “barka da safiya ki fito kinyi baqi”
Miqewa tayi tasa rigarta ta bude qofar ta fito Sarki ya rugo da mugun gudu ya rungumeta ta dagashi daqyar tana dariya yaron yace “Mom jiya nayita kuka daban ganki ba ashe gdan Uncle kika dawo nima na dawo nan” murmushi tayi tace “surutu dai kazo ka dameni ko” tsuke fuska yayi zaiyi kuka Kareem ya matso ya karbeshi yace “ba tun jiyan nace kazo mu taho ba kace kai bazaka tafi kabar Mom dinka ba to yanzun fah zaka taho ko shima aa?” Da sauri ya daga kai yace “eh” Mom dake tsaye tayi dariya tace “aikam baka isaba yaro muna tare aurena dakai mutu ka raba” kuka ya saka Yana cewa “nin…Ni Mom banasonki kinmin tsufa ni gurin Mom dina da uncle zan dawo”

Dariya sukayi dukkansu ta nemi guri ta zauna Hamida tace “jikin yayi sauqi kenan tunda na tafi nakasa sukuni dake na kwana a raina” sunkuyar dakai tayi ya miqe yace Mom me zaa kawo muku gdan namu bai gama tsaruwa ba Hajiyan sai yanzu ta fito” kiransa Mom tayi tace “kazo kayi zamanka bama buqatar komai tun jiya da sukaje suka sanar dani halin da ake ciki na kasa sukuni shiyasa nazo naganku yanayin Alhmdllh komai zai wucce insha Allahu Meenah hqr zakiyi da abinda Allah ya hukunta, Aminatuh nice na haifi Rasheed Amma bazanyi shaidarsa kamar yanda zanbada shaida akan Kareem ba kin samu miji na nunawa saa daya tamkar da dubu idan kin kwantar da hankalinki insha Allahu komai zaizo qarshe ita rayuwa kowa da irin tasa jarrabawar Babu me taya wani dakon kayan da ubangiji ya qulla masa dole shine zaiyi dakon kayansa rabon dake tsakaninku me qarfine Allah ne kawai yasan adadinsa saboda haka kuyi hqr da jarrabawarku”
Kallon kallo sukeyi kowa da abinda keyi masa yawo a ransa Mom ta miqe tace “Inason mgn dake Meenah miqewa tayi tabita suka haura saman dakin baccinta suka shiga Mom ta zauna a gefen gadon ta kama kunnenta tace “ki kiyayi shiga haqqin Kareem kawaicinsa da kararsa ta game kowa zai iya zubanki ido akan duk abinda yaga baki da raayi koda kuwa shi zai cutu hqrnsa abin jinjinawa ne shiyasa yake wahala idan ciwo ya ganshi don Allah kada ki zama silar wargatsa masa rayuwa kinji”

Kwantar da kanta tayi a cinyar Mom tana shassheqar kuka ta dauko wasu turaruka masu qamshin gaske na humra da na wuta tace muje a jerasu a show glass din fita sukayi suka jera ta fito da wani garin magani ta dauko danyen nonon raqumi ta barbada a ciki ta miqa mata tace “shine yayi saura da jiya kikaqi sha duk yanda kike tunanin fitinar Rasheed Kareem yafisa saboda akan hakan har so akayi a raba aurensa da Zahrah kwanakinsa bai qare ba yanzu Kuma gashi zaki zauna ke daya da sunyi hqr ma sun barta ta dawo da kin samu sauqin wani abun don Allah banda rowa Meenah shidai abinnan in kin hanashi ma ba ado zakiyi dashi ba Kuma ba kwanaki zaa qara masa ba idan wa’adinki yayi shima nasa yayi please a kula don Allah” sosai Mom ta rinqa bata shawari a fakaice saida taga ta dan sake sannan sukayi musu sallama suka tafi shima ya fice a gdan ta shiga bathroom tana wanka ta jiyo wayarta tana ring batabi takanta ba Saida ta gama shirinta tsaf sannan ta dauka number Ya’isha ce tabi suka gaisa tace “ya amarci jiya tsohuwar zuma ta motsa Ya Kareem an kwana ana zikiri” dariya mgnr tabata tace “waiku don Allah meye yasa kuka bawa abinnan muhimmaci ne haka”
Dariya Ya’isha tayi tace “mahadin rayuwa kenan gulma nazo yi miki” gyara zama tayi tace “aike dama indai anga kiranki to gulma ke cinki meye zaki fadamin” gwauron numfashi ta sauke tace “wato bantaba sanin Addah Abulle jahila bace sai jiya iliminta baya mata jagora kamar yanda yakeyiwa danta jiya Mai Martaba Yana zagaye bayan an taho kawoki ya nufi bayan gda ya isheta ita da Dada Hanne suna qusqus Dada Hanne nabata shawarar kawai tunda duk bugunsu yaqi tasiri akanki to su dora miki jinya yanda shi Kareem din zai gaji ya koreki sannan su sanyawa kowa qiyayyar ki a zuciyarsa ta yanda ko kin dawo gdannan Babu me karbarki Ina kaiki sun gama tattaunawar nan suna daga ido sukaga Mai Martaba da Ya Muntaz shine Mai Martaba yayi musu wani warning mai kama da daukar rai har yana fada musu daganan zuwa shekara goma idan kikayi ciwon kai saiya hanasu kwanciyar hankali ke sosai fah akayi rikici qarshe dai Addah Abulle tace da Mai Martaba tunda har ya nuna mata ita ba kowa bace akan danta to saidai ya zaba ko ita ko ke shikuma yace ya zabi zabin dansa aikuwa tace saiya saketa anso hanashi yaqi ji qarshe yayi mata daya me kyau sannan yace da Kareem yabashi damar rabuwa da Zahrah tunda abin nasu iskanci ne aikuwa tuni ya yankawa Zahrah ticket itama Kinga sai tafi samun sukunin zaman gida”

Zuciyar Imani ta Meenah duk sai jikinta yayi sanyi tace “Innanillahi wa Inna ilaihir raji’un Ya’isha wannan ba labarin badawa bane Allah fa shine ya halatta saki Amma bayasonsa nikam banji dadi ba idan Addah bataci arziqin komai ba yakamata taci na yayanta wlh wannan sakin bala’i Mai Martaba ya qara jefani sannan ita Zahrah meye laifinta a ciki najifa ance iyayenta ne suka dauketa bataso tanason mijinta Kuma ko jiya da yazo dakina naga ta kikkirashi bai dagaba haba don girman Allah wannan ba adalci bane bai kamata ba”
Tabe baki Ya’isha tayi tace “saiki fada mawa Mai Martaban tunda kinfishi hangen nesa nikam naji dadin hakan ko banza sayi hankali susan ba ko Ina ake shimfida a zauna ba” kashe wayar tayi ta zabga tagumi wannan wacce irin masifa ce daga wannan sai wannan?
Bataji tsayuwar motarsa ba saiji tayi ya zare hannunta a kuncinta ya tsugunna a gabanta ya shafa habarta ya dago kanta taja numfashi tace “Hasbunallahu wa ni’imal wakil” Babu alamun bacin rai a tattare dashi yace “meye kuma?” Kafin ya rufe bakinsa yaga ta balle da kuka tayo qasa ta dora hannunta a cinyarsa gwiwarta na gugar nasa tace “kayimin wannan alfarmar ko ita daya ce a rayuwa don Allah Ya Kareem” da rashin fahimta ya dubeta tayi qasa da kanta tace “ka dawo da matarka dakinta domin Allah.

Miqewa yayi yace “ok kinyi sallar Isha?” Girgiza masa kai tayi yace “ki dafamin coffee ki kawomin dakina” ficewa yayi daga dakin ta bishi da kallo wani takaici ya tokareta waishi miji gashi babu damar yin musu yau izzar yakeji sosai batada zabi sai nufar kitchen din da tayi ta fara hada masa coffee din ta gama ta nufi dakinta tayi wanka ta Sanya kayan baccinta ta zura hijjab ta nufi dakin nasa ta qwanqwasa yabata izinin shiga ta bude ta shiga gabanta na faduwa ta kawar dakai tunda take bata taba ganinsa a tube ba sai yau cikar zatinsa kawai abin ka tsaya ka nazarta ne qirarsa ta hutun gaske fatarsa lufluf su ta lura kamar sign na Fam dinsu ne gargasar jiki daga mazansu har matansu.
Sunkuyawa tayi ta aje masa ta miqe zata fice ya Kira sunanta ya nuna mata guri ta zauna Saida ya gama abinda yakeyi sannan ya miqe ya nufi wardrobe ya dauki riga yasa yajasu sukayi sallar ya dauki coffee din yanasha Yana kallonta ita Kuma na kallon qasa ganin yanda duk ta takura yasashi cewa “jeki Saida safe” kamar me jiran umarni ta miqe tayi zuruf ta fice ya girgiza kai yana murmushi yace “Meenah kenan”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button