JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Kafin ta rufe bakinta ya Fadi kasa sumamme ta nufeshi a guje jikinta na qyarma ta fada kirjinsa ta rushe da kuka tanajin yanda zuciyarsa ke harbawa da mugun qarfi ta Kuma rushewa da kuka tana cewa don Allah kada ka mutu ka taimakeni Ya Kareem meye nayi maka da zafi haka wlh bansan ya akayi ba ba laifina bane laifin zuciyata ne……” Numfashin da taji yajane yasata janyewa da sauri ta miqe jikinta na tsuma ta zuba masa ido tana tsiyayar da qwallah itakam tana ganin bala’i a rayuwarta daga wannan sai wannan shikuma haka yake daga mgn sai Aman jini sai suma?
Wayarsa taji ta fara ruri ta fita da sauri number Saudi tagani taja ajiyar zuciya tana kokawa da wayar wajen amsa kiran ta Kara a kunnenta hamdala tayi lkcn da taji ance “bakada kirki mutumin zaka dawo baka fadamin ba ashe da amarya ka ta…..” Katseshi tayi da gunjin kukanta tace “ka taimakeni kazo mijina zai mutu….” “wht?” Ya fada da qarfi tare da cewa “ganinan” daga haka ya kashe wayar ta koma ta sake tsugunnawa tana danna qirjinsa tana share masa kumfar dake fita a bakinsa da tissue taji an taba qofar ta miqe har tana fasa yatsa da qofar bayin ta bude qofar Dr Khazeem ya shigo da sauri yana dubanta yana cewa “inane yake” bathroom din ta nuna masa ya nufa da gudu ya cicciboshi daqyar sukayi waje itama ta zura doguwar riga ko bra batasa ba ta rufansa baya.
Suna sauka a lifter ya sashi a mota suka nufi asibiti dake da ID card dinsa na aiki a cikin jami’ar nandanan suka rufar masa suka sassaqala masa na’urori don taimakon numfashinsa tare da wasu manyan Allurai, wannan Rana Juhud bata rintsaba a tsaye ta kwana tare da likitocin suna aikinsu tana binsu duk inda sukayi.

Hakana gari ya waye sunata safa da marwa daqyar da taimakon Allah suka samu ya fara numfasawa daidai ta sauke ajiyar zuciya ta zubansa ido gabadaya sai taji zuciyarta ta karye tausayinsa yana ratsa duk wata kusurwa ta jikinta a fili tace “wanne irin so kakemin Ya Kareem da kake neman rasa rayuwarka saboda ni bayan nidin na kasance ba kowa ba maras galihu? Don Allah ka rage kishina…..” Tana mgnr ne hannunta na qirjinsa taji yaja numfashi ya daga hannunsa ya dora saman nata ya matse hannun nata idanunsa a lumshe taga hawaye na fita ta gefensu ta daga dayan hannun nata takai fuskarsa ta share masa hawayen masu zafi tace.
“Zai zama azabtarwa a gareni zubar hawayenka Ya Kareem ka daina don Allah banaso” daga mata kai yayi ta sunkuyar da kanta daidai fuskarsa tace “are you sure?” Murmushi yayi mata ta dora dan qaramin bakinta a kuncinsa tace “I like you….” Bude idonsa yayi akan fuskarta ta sakar masa murmushi shima murmushin yayi ko bada gaske takeyi ba yaji dadi sosai aransa Kuma kalmar ta qara masa qarfi yaji ya fara warkewa.

Yunqurawa yayi zai tashi ta taimaka masa ya tashi zaune ta hada masa tea me kauri ta zauna tana bashi yanasha a nutse idanunsa nakanta Saida ya kawar dakai tace “ka qoshi?” Daganta kai yayi ta mirgina kai ta miqa masa cup din ta bude masa baki ya karbi cup din ya fara bata tanasha tana kallonsa duk ta sauke masa gajiya Saida taga hannunsa na rawa ta karba ta taimaka masa ya suka nufi bathroom ta hadansa ruwan wanka zata fita ya riqota duk da kunyarsa da takeji hakanan ta zage ta wankeshi tsaf ta dauki towel ta tsane masa jikinsa ta dauko mai lotion ta shafa masa a jikinsa tana shafa masa yana lumshe yanajin wani mugun feeling na bijiro masa yakai hannu ya saqalota qirjinta ya buga batason saka masa kokwanto akan kalaminta hakan yasa ta narke a jikinsa yana sunsunar jikinta Yana lumshe ido ta sanya harshenta ta kamo fatar kunnenta ta lasa yaji wani irin yanayi mai fitar da hayyaci ya ziyarceshi ya maqaleta suka miqe suka zube a tsakiyar dakin suna tsotse juna, tunawa yayi ashefa baa gida suke ba ya janye yana gwama numfashi yace “mu koma masaukinmu” kallonsa tayi da idanunta da suke saukensa kasala tace “ai baka gama warwarewa ba” turo baki yayi ya shafa kansa kamar wani dan boy yace “ni nagaji danan mu tafi kawai” batada zabi daya wucce na kiran Dr Khazeem ta fada masa abinda yace, kamar yana kusa kuwa sai gashi suka fita tabisu a baya suna tafe Dr Khazeem Yana masa fadan Sanya damuwa a ransa ya juya ya dubi Juhud yace “tunda kasanni kasanni da ciwon zuciya Dr Khazeem kaga sila nan nasan ba sanadinta na kamu dashi ba tun Ina qarami aka tabbatar da inada sign nasa Amma ko tashi baitabayi ba Saida qaddarar soyayyarta tasakoni a gaba Dr Khazeem inason Aminah sonda bantaba yiwa wani abu ba a duniya idan zan rayu da ita cikin aminci inaji a jikina duniya zata iya mantawa da Dr Kareem Mahfuz yanada matsalar ciwon zuciya domin itace zuciyar tawa”

Jinjina kai Dr Khazeem yayi yace “to ai kanwa dai ta kar tsami Dr Kareem Aminah ta zama taka fah mallakinka ce” murmushi yayi me kama da yaqe yace “zadai ta zama inasonta tanason Yayana Rasheed wlh addu’ar Allah ya bayyana Rasheed kullum da koda yaushe Amma idan na tuna munyi tarayya akan son Abu daya sai naji zuciyata ta karye musamman da yake banine abinda mukeso yakeso ba yafini power a gurin” shiru yayi Yana mayar da numfashi ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur yace “kasan me Dr Khazeem inaji a jikina duk ranar da Rasheed ya bayyana ranar numfashina ya qare a duniya……”
Dukka suka kallesa da sauri musamman Meenah da taji wani dukan zuciya yayi murmushi yace “badaga Ni bane a baya na da bansan wace ke ba nasha wahala har likkafanina an dinka saboda ke Meenah ya kike tsammani idan yanzu ne?” Ta riga kowa bude motar ta kwasa da gudu ya biyota Yana dafe qirjinsa ta rigashi shiga masaukin ta fada saman bed ta rushe da kuka me ban tausayi tabbas tana cikin tsaka me wuya Allah ne kawai yasan meye zai faru gobensu, ji tayi ya kwanto jikinta yana hura mata iska a kunnenta yace “kiyi hqr abinda nasan zai faru ne Meenah na haska miki domin ki shirya inaji a jikina Rasheed zai bayyana bada jimawa ba domin bantabaji araina ya mutu ba nikuma daga ranar da aka daura aurena dake nake qirga sauran kwanakin rayuwata…..” Rufensa baki tayi cikin kuka tace “ka daina Ya Kareem Allah bazaka mutu ba saboda ni……..”

Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…

Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..

Oum Hairan
[8/11, 4:39 PM] Oum Hairan: Muryar Dr Khazeem ne yasasu miqewa ya fita sukayi sallama ya dawo dakin ya kwanta ta miqe ta nufi kitchen din bata samu komai ba sai ragowar Naman da sukaci jiya shi ta dumama ta sake hado masa tea ta dauko ta nufo dakin ta aje masa ta cire hijjab dinta ta zauna a qasa tace “kaci abinci saika samu qwarin jikinka”
Girgiza mata kai yayi tare da daga rigarsa ya sanya hannunsa cikin wandonsa ya bude bakinsa cikin muryarsa me sanyi yace “bana tare da yunwa kinsan matsala ta Meenah ita kadai nakeson kimin maganinta” sunkuyar da kanta tayi ya sauko ya dago kannata ta lumshe ido yayi kissing na lips dinta yace “kiyi hqr dani nasan na takura miki ko?” Girgiza masa kai tayi ya janyota ta kwanta a jikinsa ya matseta duk da firgicinta tayi masa rawar gani ya samu yanda yakeso.
Rayuwa sukeyi me armashi cike da kulawa da tattali wa junansu musamman Kareem da kacokan lissafin rayuwarsa yake akan Juhud itanma fahimtara irin tasa matsalar yasa kan dolen dole ta yakicewa kanta bayyananniyar damuwa, ko tunani ta daina yarda tayi a gabansa yanzun nan saiya rikice mata rayuwarsu a qasa mai tsarki ta zame mata wata rayuwa da take bata nishadi tanajin Kareem a ranta fiye da tunani Amma har gobe takasa canza gurbin Rasheed kullum shine cikin tunaninta mafarkinta da dukkan wani motsinta hatta addu’arta ya kwashe kaso mafi rinjaye shidin bashi da tamka cikin rayuwarta bazatayi masa madadi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button