JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL
Jinjina kai Muntaz yayi yace “Ya Kareem din ne ya saki Meenah Kumbo….” Daquwa ta watsa masa tace “aa tatsunniya nakeyi maka ja’irin yaro zo ka kaini cikin gari akwai wata yar qasarmu mu kwana acan da safe saimu tafi” yasan rikicin Kumbo Hami idan ta fusata hakanan ya debesu da Meenah da taketa matsar hawaye batasan dalili ba sai taji abin yanayi mata yawo a kwanya ta tambayi kanta yafi sau goma ashe Kareem zai iya rabuwa da ita ashe dama duk abinda yake fada mata na ta rayu dashi forever itane zuciyarsa itane rayuwarsa qarya yakeyi mata?
Sosai takejin qunci a zuciyarta batasan zafin saki haka yake da qona zuciya ba hawaye ta rinqa daukewa lkc zuwa lkc har suka Isa unguwar da Kumbo tace akaisu dake tayima matar waya aka taresu gdane babba na masu hali suka shiga bayan Muntaz ya tafi komai ya nutsa Kumbo take fadawa qawar tata abinda ya faru sun jima suna jinjina lamarin Meenah binsu kawai takeyi da ido wani bangare na zuciyarta na ayyana mata lallai dole ta canza takunta lkc yayi da zata tsayawa rayuwarta.
Kuyi hqr da wannan naso yi muku typing me tsayi wani uzuri ya katseni ma hadu gobe.
Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…
Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..
Oum Hairan
[8/18, 2:25 PM] Oum Hairan: Batasan ya akayi ba da safe Kumbo Hami ta tasheta suka duma zuwa Kano kwanansu biyu a Kano ta Kira Muntaz tace ya kawo mata passport din Meenah ta bashi address na inda suke ranar ta kama kwanan yarinyar bakwai a duniya hakanan Muntaz ya taho ya kawo musu passport din ya nan yake fadawa Meenah Kareem bashida lfy Amma fita dashi waje.
Fatan sauqi tayi masa da rangwame gurin me ikon bada sauqin ya dauko kudinsa Dubu dari yabawa Kumbo Hami yace “wai Addah ce ta bayar tace a siya rago ayima yarinyar hakika” murmushi tayi ta debi kudin ta watsar tace “kace mata mu harkar arziqi mukeyi bama ta tsiya saboda haka ragon dubu dari yayi kadan a hakikar jinin mu tabarshi ta rage zafi” da wadannan kalamai ya dauki hanyar Katsina sukuma sukaci gaba da abubuwan da zasuyi na tafiyarsu Mali domin taci alwashin Meenah ta gama zaman wannan gda da can a baya ma don bata da ikone da shi kansa Rasheed saita rabasu don sama mata salama da yancin rayuwa.
Sun qara kwana uku kullum suna waya da Mom suka dauki hanyar qasar Mali nan Meenah ta Raina kanta gdan kakanta mahaifin Mamanta ya rikita lissafinta yasata jin sabuwar izza ba gdan sarauta bane Amma barorin gdan sunfi dari ko Ina sukabi zubewa akeyi ana gaishesu har kawo suka isa asalin harabar gdan inda zata sadasu da asalin cikin gdan Hajja Kharimatu tayi tsalle ta rungume Juhud tana dariya tace “wayyoh dadi ga yata ga jikata. Narkewa tayi a jikinta tana murmushi suka zube a falon kafin kace wane wannan falon ya cika maqil da yan uwan mahaifiyarta kowa ta kalla fuskar Innatu take gani a fuskarsa ta share hawaye tace “na yarda na dawo cikin gatana cikin ahlina
Wani dattijo dake shigowa yace “kuma bazaki qara barin ahlinki ba har gaban abada Qanwa inayi miki barka da dawowa cikin zuri’armu bayan wahala da mukasha ta dogon lkc akan neman inda zamu samoki”
Kumbo Hami ce ta nuna matashi tace “tashi kije ga kakanki Meenah yayi kukan boye yayi na fili saboda rashinki ke kadai duk jikokinnan da suka kewayeshi” miqewa tayi da sassarfa ta Isa garesa ya rungumeta yana shafa bayanta tana kuka Yana hawaye yace “tsarki ya tabbata ga ubangijin daya rayani har naga Aminatuh na a raye cikin aminci” janta yayi suka zauna yace “naji quncin watsi da nayi da mahaifiyarki hakan ya jawo tabarbarewar komai naso na gana da Aishatu kodon na nemi gafararta ita da mahaifiyarta ubangiji bai nufa ba saiya kawomin ke madadinta ajiyar numfashi tayi shima ya aje numfashi nan sukayita hidima da ita da Muneefanta har dare sannan aka kaita makwancinta sashine guda da yasha kyau da gyara sosai part din ya qayatar da ita Saida Kumbo Hami ta dafanta ruwan zafi ta gasanta jiki sannan ta qyaleta ta kwanta bacci kuwa me dadin da ta dade batayi irinsa ba ranar shi tayi.
Haka rayuwarta a Mali taci gaba da kasancewa cikin annashuwa dangin mahaifiyarta daga mazan har matan da yayayensu sunata nannan da ita sai janta sukeyi da nuna mata gata ta kuwa saki jikinta sosai duk da zuciyarta bata nutse guri daya, kaso mafi rinjaye na sinadarin tunaninta yana ga Rasheed Wanda kullum saita Kira wayar Mom taji lfyrsa Abu daya take fada mata jiki ana samun sauqi itakam tanason sanin wanne irin sauqi ake samu gashi Kumbo Hami ta kasa ta tsare ta hanata wani motsi koda tasamu Baffa Garbu kakanta da mgnr tanason zuwa Nigeria don ta gano jikin Rasheed hanata yayi gashi shima Kareem yaqi lfy an fada mata ma Addah ta dawo masa da Zahra Amma don masifa yaqi qyaleta batasan inda yasamu number data sake ba kusan kullum sai ya kirata da farko Yana bata tausayi idan yana fada mata halin da yake ciki so batason yasa mata kokwanto akan qudurinta ta qudurce ko zatasha wuya zata rayu da Baffa’am dinta shi kadai a mind dinta domin yafi kowa cancanta da ragamar zuciyarta.
Bata cikason takura ba hakan yasa sometimes tana ganin kiransa takeqin dagawa musamman data fahimci sosai Kumbo Hami ke fushi da ita duk ranar data fahimci sunyi waya da Kareem, Muneefah nata girmanta kwanci tashi har taci wata biyar da haihuwa lkcn tuni Juhud ta hada iddarta hankalinta ya kwanta tayi wani matsiyacin kyau mai rikita isassun mazaje duk inda ta juya ido akanta yake a daidai lkcn ne Kuma kawai Baffa Garbu ya shirya musu tafiya shaqatawa qasashe biyar don sangarta harda wani bata zabi su hudu zasuyi tafiyar shi Kumbo Hami Naila daya cikin jikokinsa sai ita Meenah da yarta Muneefah.
Yanayin yanda suka tsara tafiyar ne yasasu dole Saida suka bi ta Nigeria Kuma ma ba yini zasuyi su tashi ba sai sun kwana biyu qusqus taji sunayi wai zasu barsu a masauki suje Katsina su duba Rasheed daya dawo gida shekaran jiya, ai tanajin haka ta tubure musu kuka baji ba gani dole don basusan bacin ranta suka aminta suka shirya tafiyar da ita tanata murna zataje taganshi tare da addu’ar Allah yasa ya warke sosai tunda suka shigo gdan a mota taji gabanta na faduwa sunayin parking ta daga kanta ta ganshi tsaye saman benen part dinsa corridor din daya zame masa tamkar gurin shaqatawa yanajin nishadin tsayawa a wannan guri musamman idan wani abu na damun zuciyarsa.
Suna tsayawa ta zame batare da ta jira sun fito ba ta saba Muneefah a kafadarta ta nufi hanyar shiga part din nasa cikin saa a bude yake ta shiga ta nufi inda zai sadata da corridor din ta haura da sauri fadi takeyi “Baffa’am wayyoh Baffa’am dina miss you too…..” Tsayawa tayi a bayansa ta dafa kafadarsa tace “ayyah dai ubana yafi na kowa alfaharina a duniya bama haka dakai fah” juyowa yayi ya kafeta da idanunsa dake cikin glass baqi ya cije lebensa har Saida suka fashi ya kama hannunta ya cire daga kafadarsa ya furzar da iska ya juya yabar gurin, binsa tayi cikin muguwar kidima tana Kiran sunansa baiko juyo ba Saida ya dangana da dakinsa
[8/21, 8:19 PM] Oum Hairan: Yana shiga tabisa dakin ya tsaya idanunsa na kanta yace “kije kawai banson hayaniya” dubansa takeyi da yanayin rashin fahimta tace “Ya Rasheed nice fah Meenanka” sake daure fuska yayi ya zura hannunsa cikin aljihun wandonsa yayi murmushinsa na isa da indai yayishi tasan ya shiryawa rashin mutunci yace “eh na ganeki fah Juhud Meenah Aminatuh Mom Sarki junior kinsan nasanki nasan wace ke fiye da sanin da kikayiwa kanki? Koda yake ba abin mamaki bane canzawar mutum cikin qaramin taqi Meenah kiyiwa Allah ki ficemin a daki kada kisa ruwa na ya hau wlh banson ganinki….”
Idanunta sosai ya ciko da hawaye ya fara tsiyaya a fili tace “meye nayi maka?” Zaburowa yayi kamar Wanda ta bugawa wani abu yace “zanc….” Sai Kuma yayi shiru jikinsa na Bari yace “ki fice nace da gaske ban qaunar ganinki Meenah kinci amanata kin ha’inceni kin yaudareni kin nunamin Babu wanda kikeso samana ashe qarya kikeyi dama ce kika kasa samu lkcn da kikaga Babu idona kika dauko zabinki kika maye gurbina dashi Abu mafi ciwo wai qanina Meenah Ina raye ki auri Kareem Kuma ki dawo ki fadamin me nace meye zaki fadamin…..”
Ya qarasa mgnr da ihu ta dago idanunta da tun kafin ya fara mgnr suke tsiyayar da hawaye tace “wlh ba laif…..” Dauketa yayi da Mari yace “idan na qara cewa ki fita kikaqi Tabbas gangar jikinki zata riga Rana faduwa Meenah a yanda nakejin tsanarki tsaf ko zaa kasheni zan iya kasheki” juyawa tayi jikinta a mace bata taba tunanin haka daga gareshi ba tayi tunanin kamar yanda take a baya yafi kowa fahimtarta da bata lkc yaji damuwarta ashe yanzun ta canza zani ba haka abin yake ba “to kodai bai gama warkewa ba?” Abinda ta tambayi kanta kenan lkcn da take tafe kamar mahaukaciya zuciyarta na tafasa gabadaya duhu take gani a idanunta batasan inda take jefa qafarta ba.