JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Qara ta saki lkcn data buga kanta jikin bishiya batare data sani ba tayi baya zata Fadi Kareem dayaketa mata mgn tun dazun ya tareta ta fada hannunsa tafi minti biyar komai Yana juya mata kafin duhun ya yaye ta bude idanunta ta zubasu akansa ta janye dasauri tare da gyara riqon yarta tace “tnks” daga haka ta juya taci gaba da tafiya yabita yace “Meenah Ina gurin Aiki akacemin kinzo nazo dominki ki tsaya Mana mu gaisa” hawayenta ta dauke ta juyo ta dubesa kamar zatayi mgn sai yaga ta dago Muneefah ta miqa masa yasa hannu ya karbi yarinyar ya cillata sama yanajin muguwar qaunarta na zaga ruhinsa Wanda ya tabbatar da tasamo asali ne daga qaunar da yakewa mahaifiyarta.
Juyowar da zaiyi yaga gurin wayam Meenah har takai qofar falon gdan ya bita da sauri yana kiranta Amma ko juyowa batayi ba ta fada dakin Mom ta zube a jikin Kumbo Hami ta rushe da kuka tace “dama saboda irin wannan ranar nace abarni na rayu ni kadai bazan aure ba aka kasa fahimtata yanzu ga irinta nan Ya Rasheed yaqi saurarona tuhuma yakeyi da naci amanarsa Kumbo wlh banci amanarsa ba ki fahimtar dashi ki zai gane…..” Gabadaya hankalin Kumbo Hami ya tashi ta qufula an taba mata zuciyar cikarta daidai lkcn Kareem ya shigo suka kalleshi Meenah ta kawar dakai ya zauna Yana share gumi yace “meye ya faru Kumbo?” Qwafa tayi tace “yo Wagga sakarar yarinya damuwarta tana wucce ta Abdulrasheedu ne komai Rasheed Komai Rasheed aiga irinta nan ga wulaqancin da kika jama kanki nan da kinyi zamanki a Kanon gdan Barrister Kabir aida baisamu damar cin mutumcinki ba”

Jinjina kai Kareem yayi yace “ayi hqr Kumbo kinsan halinsa shi dama fahimtarsa ba daidai take data mutane ba ni kaina gaba yakeyi dani a gdannan akan abinda bamu Isa mu canzashi ba Kumbo ya zanyi da rabon Muneefah ne dake tsakanina da Meenah itanma da taqini take kallona a matsayin maci amanar dan’uwa ya zatayi da ita wlh na tabbata inda Mai Martaba bai hada auren nan ba ko ta wacce hanya sai Muneefah ta fita ajikina ta shiga nata Kuma saita haifamin ita tunda haka qaddarar take a rubuce”
Shiru ta ratsa ta dogon lkc Kareem ya dago ya dubi Juhud da har yanzu take kwance jikin Kumbo tanata matsar hawaye ya miqe yace “kiyi hqr komai zaizo qarshe Allah shine yasan abinda ke cikin qasa a binne” daga haka ya fice a dakin dauke da Muneefah ya nufi gidansa da ita Zahrah tana ganinsa da yarinyar ta zabura ta miqe ya dubeta ya kawar dakai itama saita waske ya shiga kitchen ya daukowa yarinyar biscuits da yourghut ya zauna Yana bata yana murmushi dadi yakeji a ransa rabonsa da ita tun tana jaririya gata har ta tafi shekara guda ji yake dama ace mahaifiyarta ce a gefensa.

Share hawayen daya tsiyayo masa yayi Zahrah na kallonsa tana kada qafa takaici yana qara kamata tace “waikai yar wace ka dauko?” Murmushi yayi yace bakisanta ba ko?” Tabe baki tayi tace “ya zaayi nasanta tunda baa cikin ahlinmu ta fito ba” sake kallon Muneefah yayi yace “qwarai kuwa baa cikin ahlinku take ba tunda kinada ikon canzata daga jinina Zahrah na dade da fahimtar Ina kika dosa koma dai meye a ranki kibi a sannu domin Aisha itace ya babba a gurina Kuma ko zaki haifi duniya bayanta zasu biyo abu na qarshe da nakeso ki sani a aurenki ma arziqin Meenah kikeci saboda haka ki taka a sannu”
Tashi yayi ya dauki yarsa ya nufi hanyar ficewa daga gdan tayi dariya tace “iska kuwa na wahal dame kayan kara wahalalle Meenah dai tafi qarfinka saidai kaganta ka hanga kayi sake dan zaki ya girma me ita ya dawo son maso wani qoshin wahala”

Bai saurareta ya tsaya bata Amsa ba ya fice ya nufi wani shop yayima yarsa siyayya ya juya ya koma gdan sarautar har sun shirya suna zaman jiran dawowarsa domin Alh Garbu yace ba kwana zasuyi ba a ranar zasu koma Kano Meenah bataso haka ba taso ta samu cikakken lkcn fahimtar da Baffa’am dinta gskyr lamari Amma batada wannan damar, tana kallonsa Yana kallonta ya dawo daga yawonsa a mota sukayi sallama da Kumbo Hami da Alh Garbu itakam ko kallo bata isheshi ba wani takaici ya cika mata zuciya abin nasa harda wulaqanci juyawa yayi yayi tafiyarsa tabisa da kallo ta girgiza kai ta shiga motar suka tafi tana waiwayensa hankalinta baimakai ga Kareem da yaketa daga mata hannu ba.
Suna tafe tana furzar da iska a haka suka Isa Kano goma na dare suna Isa gdan da suka sauka ta shige daki ta kwantar da Muneefah dake bacci ta zauna zaman karatun wasiqar jaki batada mafita ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta dawo ta kwanta bacci ya gagareta sai juyi kawai da takeyi cikin dare ta lalubi wayarta ta fara neman layinsa ta kasa jurewa Kira biyar tayi baa dagaba ta rubuta masa gajeran saqo na ban haquri, tana qara Kira taji wayar a kashe taja fasali ta kashe tata wayar ta zubawa Muneefah idanu tana sharar kwallah Tabbas duk abinda yasa Rasheed daukan wannan matakin akanta ba qarami bane, da wannan tunanin bacci ya dauketa da asuba ta tashi suka fara shirye²nsu domin tashi zuwa Dubai, Tara suka tashi itadai badon tanajin dadin komai ba donma Naila tana dauke mata hankali da dan karen surutunta.

Kumbo Hami ta fahimci abinda yake damun jikar tata koda suka isa dinma bata wani saki jiki ba har suka Isa masauki sukayi sallah sukaci abinci sukayi wanka kowa ya nemi makwanci sai dare suka fice daga masaukinsu, suka shiga gari itadai Meenah yaqe kawai takeyi lkc zuwa lkc tana gwada layin Rasheed Amma har yanzu yaqi dagawa har dole tasa ta saduda ta qyaleshi.
Sai asuba suka koma gda sukayi sallar asuba suka kwanta rayuwar taci gaba da gudana a haka baqin naci ya hana Juhud daina kiransa shikuma yaqi dagawa kamar yanda Kareem yake nacin kiranta itama tana jizgashi idan abin ya dameta saidai ta Kira Ya’isha tasa mata kuka tace ta tayata bawa Baffa’am dinta hqr saidai Ya’isha tayi murmushi tace “wlh Meenah baqin kishine yake damun Ya Rasheed Amma Ni shaida ce bai daina sonki ba” da haka take dan kwantar mata da hankali take samun nutsuwa.
Satinsu biyu suka daga zuwa Malay daga Malay sukayi India daga can sukayi Saudi sukayi Umarah daga nan sukayi Turkey daga Istanbul suka gangaro Nigeria daga Nigeria suka zarce Mali, watanni hudu suka kwashe a yawon nasu suna dawowa suka shiga bikin Naila da Hameen dake abin duka na family ne yayi armashi sosai.

Mom ita da Ya’isha da Aunty Hamida duka sunzo tunda sukazo take maqale da Mom tanata zubanta shaqwaba washegari suna gurin dinner Rasheed ya dira a qasar Basu dawo gida ba sai wajen 12:30am suna kowa baccine akansa tana shigowa tana cewa “ni Allah Mom badon kin takura ba bazanje wannan dinner ba gara na kwanta nayi chat…..” Mgnr ce ta maqale mata lkcn da idanunsu ya sarqe ana juna ya wani maze tunaninsa zatayi masa mgn ga mamakinsa sai yaga taba banza ajiyarsa ta Kara wayarta a kunne tana cewa “double sorry na shiga yanayine wayar na jakka bansa ka kiraba sai yanz….” Iyakar nan Rasheed yaji ta shige daki yaji gabansa na mugun faduwa ya dubi su Mom da suketa faman dariya ita da yan’uwanta ya miqe zuciyarsa na tafasa yace.
“Gobe da wuri zan wucce Ghana ba lallai mu samu haduwa ba” bai jira amsar Mom ba ya fita ya ishe Alh Garbu da fadawansa sunata hira gda kamar kasuwa ya lura suma dabi’ar qasar kamar basa bacci sosai da dare, daquwa Alh Garbu yayi masa yace “dan boko dan qaniyarka shine ka shige cikin mata ga qannenka da yayyaenka da iyayenka duka bazakazo cikinsu ba” yaqe kawai Rasheed yakeyi ya isa garesu ya gaishesu wasunsu da yawa yasansu qannen Mom ne wasu Kuma jikokin gdanne nan aka baje sabuwar hira Nan Alh Sulaiman babban yayan su Mom ya kaikaice yace “Alh dama tun kusan sati uku nakeson yi maka mgn wai ya mgnr yaran nan Najeeb da Ameenah…..” Tunda ya Fadi haka Rasheed ya zubansa ido duk da baisan wacce Aminan ake nufi ba Amma yaji saukar saqon faduwar gaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button