JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Zubansa idanu Alh Garbu yayi Yana nazarinsa can yayi murmushi yace “to ai lamarin Aminah ne akwai rikitarwa kaga mijinta na farko ko igiya daya bai yanke mata ba nemansa akayi aka rasa shari’a tabata damar aure ta auri qaninsa shikuma qaddara ta rabasu da saki daya to mijinta na farko din ya bayyana Kuma tanasonsa shima na shaida yanasonta wani dalili ne ya hanashi magantuwa saboda haka indai sunason juna to sunfi dacewa da juna wannan dalilin yasa nace da Najeeb ya hqr wannan abu duk na gidane dashi da Rasheed duk jikokin gdannan ne rashin zumincinsu yasa basusan juna ba”
Tunda Alh Garbu ya fara mgnr gumi ke karyowa Rasheed baqin kishinsa ya motsa ya dago idanun nan kamar gauta Yana Shirin yin mgn wayarsa tayi ring ya zaro ya duba aqogo daya na dare harta gota ganin number Ya Arman yasashi tunanin akwai dai wani abu daya faru daga wayar yayi ya Kara a kunnensa numfashi ya sauke me nauyi yace “ina Kareem din?” Huci ya furzar yace “Har matarsa aka kashe ko iya shi kadai ne?” Sake jan numfashi yayi yace “ok zan dawo gobe” daga haka ya kashe wayarsa.
Ya miqe ya nufi makwancinsa ya soma safa da marwa Yan fashi sun shiga gdan Kareem sun kasheshi shida matarsa? To akanme?” Tambayar da ya rinqa yima kansa kenan mara Amsa a hankali yaji wasu hawaye sun zubo masa ya nemi guri ya zauna Yana tuno haduwarsu ta qarshe da kalmar qarshe ta Kareem ya fada masa, “Kai dan uwana ne na jini Ya Rasheed a tunanina murna ya kamata kayi da ya kasance nine na kula maka da iyalanka a halin bakanan ba gaba yakamata kayi dani ba! Ya Kareem har gobe inason Meenah bazan taba daina sonta ba har fitar numfashina na qarshe na hqr da Meenah ne badon zuciyata ta hqr ba saidon bata damar kasancewa dakai domin kaine zabinta, dani qaddara ta rubutawa bacewa ka auri matata idan na dawo gdy zanyi maka badon bana kishinta ba aa saidon nasan ta cancanta ne shiyasa ta zama matar gado cikin ahlinmu”……….

A daren nan Rasheed bai rintsa ba kwana yayi Yana tuna abubuwa da dama da suka faru tsakaninsa da Kareem tun daga ranar farko da suka fara qullah soyayya da Meenah kawo lkcn daya aureta ta qarfi da irin wahalar da Kareem ya rinqa Sha ta ciwon zuciya duk akanta kawo yanzu yanayin da suke ciki da irin bibiyar da Kareem ya rinqa yi masa akan yayi hqr ya daina gaba dashi sosai yayi kuka da baitabayin irinsa ba a duniya tabbas ya tafka kurakurai masu wuyar gyarawa Kareem baya duniya labarinsa ya shude balle yaje ya nemi afuwarsa akan abinda yayita qoqarin ganar dashi yaqi bashi qofa.
Da asussuba kuwa ya dokawa Mom Kira itanma yanda ya kwana haka ta kwana saboda tun Daren itama aka fada mata abinda ke faruwa Meenah kam batasan meke faruwa ba Amma ranar ta kasance cikin wani yanayi domin a daren waya sukeyi da Kareem Yana mata wasu kalamai data kasa fahimtarsu can taji yace “Meenah kada ki manta wannan wlh tallahi duk duniya nafi kowa sonki ban barki don biyayya ga umarnin Addah ba nabarki ne don nasan kedin banine a zuciyarki ba Meenah in son samuna ne Muneefah ta rayu a qarqashin kulawarmu ni dake nasan hakan bazata samu ba wani abu yana gaf da faruwa dani, Ina kukan rabuwa da abubuwa biyu da nafi qauna ke Meenah da Kuma yarmu Muneefah Amma a wani sashin Ina farin cikin kasancewar zata rayu da cancanta madadina wato Rasheed Meenah ki komawa Rasheed don Allah don taimakon maraicin Aishatuna kinji……” Daga haka ya tsaya da mgnr taji wata qara can taji yace “ina zuwa zan kiraki kamar Yan fashi sun shigo unguwarmu” daga wannan tajishi shiru kalamansa sun tsayanta a rai zuciyarta ta karye tabbas lamarin Kareem akwai taqawa da tsoron Allah baitabayin Abu don jin dadin kansa ba komai zaiyi yanayine don mafitar Al’umma Kareem yakai masoyi a gurinta.
Miqewa tayi zumbur lkcn da taji Ya’isha ta rushe da kuka tana cewa Innanillahi wa Inna ilaihir raji’un Allahumma ajirni fih musibati Mom da gaske Ya Kareem sun kasheshi ya mutu shikenan bazai qara dawowa duniya ba Muneefah ta zama marainiya…..”

Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…

Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..

Oum Hairan
[8/22, 8:04 PM] Oum Hairan: Da mugun gudu cikin fitar hayyaci Juhud ta fito daga dakin da take cikin gigita ta cacumi Rasheed dake shigowa idanunsa kamar garwashi ta jijjigashi tace “da gaske ko gizo kalamin Ya’isha sukemin Ya Kareem ya mutu…..” Zubanta idanunsa yayi so yake yayi mata mgn ya kasa sai kawar dakai da yayi hawaye suna zubo masa yasa hannunsa ya janye nata, ganin yanda yake goge hawaye da tissue yasata zama a gurin dabar ta daura hannunta akanta ta rushe da kuka tana cewa Innanillahi wa Inna ilaihir raji’un” Ya Kareem kada ka mutu dom girman Allah ya kasance mafarki shudadde Wanda bazan qarayinsa ba har abada wlh na aminta da kai zan dawo gareka na qara Haifa maka qannen Muneefah nasan shin….shine burinka a duniya…..” Dagota Mom tayi tace “kiyi hqr Meenah shirya mu tafi” Babu wani shiri ta sunkuci Muneefah da taketa bacci abinta baccin asara abin tausayi mota ta debesu gabadaya harda Alh Garbu suka nufi airport dake abin na manya ne nandanan suka Isa Nigeria kamar a qasar suka kwana goma na safe suka shiga Daura lkcn an gama shirya Kareem da Zahrah zaayi musu sallah mazan suka tsaya wajen jana’izar sukuma suka shige ciki.

Addah Abulle tana ganin Juhud ta miqe ta nufeta da sauri ta karbi Muneefah ta rungume ta qara rushewa da kuka tace “shikenan ya tafi Meenah yatafi yabar Mana duniyar Babu shi din Babu Zahra wayyoh Kareem dama inada dama Dana dawo dakai duniya nabarka da zabinka da yarka daya mafi soyuwa a ranka kullum kana fadamin bakajin dadin rayuwa baka tare da Muneefah ashe ita kadaice rabonka ita zaka tafi kabarni da ita Kareem wayyoh Ni Zainabu na cuci kaina na cuceka Kareem Allah na gde maka da bakabani saa ba lkcn da malam Mati yabani magani yace nabaki kici a waina da tuni Babu Aishatu da tuni Ni da kaina na kashe bayan dana kaicona Ni Zainabu Allah ya isa Dada Hanne da Hajiya Bilki kune kukayita dorani a keken bera ashe kaini zakuyi ku baro yau na rasa Kareem ban barshi ya rayu da farin ciki ba ya tafi da jin ciwon nice silar rabashi da matarsa mafi soyuwa a duniyarsa….”
Surutai taketayi kamar wacce ta zautu hakan yasa wasu mata daga cikin danginta sukazo suka kamata suka tafi da ita daki tana kuka tana kiran Meenah Kareem shikenan Kareem ya tafi yabarmim duniyar Ina nutsuwata da hankalina yayi na kasa gane nauyin qaddararsa?” Kowa ka gani a falon kuka yakeyi mutuwar Kareem tabar tambari ba iya Daura ko Katsina kadai ba hatta arewacin Nigeria baki daya duk Wanda yaji labarin mutuwar ko baisanshi ba sai yaji alhini a jikinsa duniya tayi rashin nagartaccen mutum me hqr da kawaici kunya da kara wannan dabi’ar tasa yake soyuwa a zuciyar duk wanda yayi mu’amala dashi ta kusa kota nesa ranar anyi yinin alhini Juhud kam zazzabi ne ya rufeta sosai bana wasaba hawaye yaqi tsayawa a idanunta tayi danasanin zabar Rasheed akan Kareem ta zabi Rasheed tabar Kareem Rasheed din ya tattarata yayi watsi da ita yaqi saurarenta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button