JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Inuwarsa da taga ta lullubeta yasata dago kanta kafin ta gama sauke idanunta akansa fitsari ya fara qwace mata hakan yayi daidai da lkcn daya daka mata wata uwar tsawa yace “meye hakadin banason shashanci sanyi kikeji da zaki rinqq wata tsumar jiki?” Kafin ya rufe bakinsa ta saki kuka me gunji cikin kukan take cewa “ni dama nasani mutuwar Innatu bazata taba zamemin Alkhairi ba wlh gara na mutu na hutt…..” Ko kadan bai daukan shirme da raini hakan yasashi shaqota ya miqar da ita ta rintse idonta lkcn da shikuma yayi saurin sakinta saboda qarnin manshanun daya shaqa a hancinsa daya sanyashi jin amai ya yunquro masa da sauri ya nufi bathroom din ya fara kelaya aman ta miqe zaune tana jan zuciya har yanzu jikinta rawa yakeyi. Fitowa yayi daga bathroom din yana qwafa baiko tsaya a dakin ba ya fice ya jima da fita kafin ya dawo dauke da wata jaka a hannunsa ya cilla mata yace “kije kiyi wanka ki cire abinda yake qarni a jikinki bana zama inuwa daya da qazami”
Dagansa kai tayi cikin yanayin tsoro ya sake ajiye gongonayen Madara da Milo da nescafe ya fita can saiga wata Christy ta shigo dauke da flast na ruwan zafi da wata kula a hanunta ta aje ta juyo ta watsawa Juhud wani dan iskan kallo ta tabe baki tace “gashinan yace ki tashi kiyi break kafin ya dawo” ko kallon tsiya bata samu gurin Juhud ba balle na arziqi bama tasan tanayi ba ta lula duniyar tunanin rayuwarta ta baya hakan yabata damar qare mata kallo taja tsaki a ranta tace “dubeta kamar aljana” a fili Kuma waya ta dauka ta Kara a kunnenta tayi turancinta Juhud ta juyo da sauri ta kalleta sai taji ta burgeta tanason mutumin da ya iya turanci a rayuwarta a fili tace “lah gwaggo kin iya turanci nima zaki koyamin?”
Dariya abin ya bata ta Harareta tace “saboda yar iskance niba me zai hana na tsaya koyawa bakin da bai iya ko A ba turanci qazama dake” bataji haushi ba domin ko dukanta zatayi indai akan turanci ne to zata jure “qwalqwal tayi da ido tanason yin mgn ya turo qofar gabanta ya Fadi tayi saurin zubansa ido sai yanzu ta ganeshi tace “lahhhh Kado dama kaine ashe kaine wanda ka siyemin nono na ranar da su Baffa Ribado suka qonemin Innatu na….” Shiba ma’abocin dariya bane hakan yasashi shafa sumarsa yace “dan uwarki waye Kadon?” Nandanan ta nutsu ganin ya nufota yace “wato ke dama da ganinki zakiyi raini nace kiyi wanka shine saboda kin quna kamar yanda aka qone Innatu kikaqi yi salon ki qara sani amai jibi babu abinda yake tashi sai qarnin manshanu a dakin nan”
Kallon Christy tayi idanunta sun ciko da qwallah da sauri Christy ta dauke idonta tace “baby kace qanwarka ne Kuma naji tana mgnr tallar nono ya haka?” Harara ya maka mata ya juya ga fast din tea din ya dauki cup ya hada mata ya miqa mata da biredi sai soyayyen qwai da dankali, tea din ta karba hannunta na rawa dama yunwa takeji sai bread din ta soma turawa yanda takecin abincin a yunwace yasashi zama ya zuba mata ido ta cinye bread din ya sake yaga ya bata ta Kuma cinyewa tama manta da shayin Saida taji ta qoshi sannan ta kora da shayin ta ajiye kofin tayi gyatsa ta rinqa kallon qwan tana girgiza kai.
“Ya sunanki?” Abinda taji ya fada kenan ta juyo da sauri tace girogal….. Da mamaki da takaici ya dubeta yace “sunanki kenan girogal?” Dagansa kai tayi tace “ayyah Kado tausayinta nakeji yanzu shikenan kun cinye mata qwanta da kinbar mata da ta haihi yaranta ta rinqa jansu suna tahiya kiwo” wata muguwar dariya ce ta qwacewa Christy lkcn da taga ya dafe kai ya juya ya galla mata harara ta gimtse dariyar kawai taga yakai hannunsa ga wandonsa ya fara zaro belt dinsa nandanan ta nutsu ta saita hanya tasan dukansa sai tayi wata guda tana jinya Juhud nacan tana sharar kwallah tana cewa Allah sarki girogal Allah shine zai saka miki kamar yanda zai sakamin nima…..” Qara ta saki lkcn daya zumbuda mata belt din tayo qasa ta fadi aikuwa ta shige qarqashinsa tana ihu ya qwace qafarsa yace “ina tambayarki kina yimin hauka” da sauri tace “Aminatuh Juhud Baffa Haro Innatu Indo…..” Jefar da belt din yayi ya dafe kansa ya fice daga dakin ya nufi gidansa yana shiga ya zube a kujera yace “Rasheed ka daukowa kanka da shegen kwashe²nka fitowa Christy tayi daga daki kasancewar ta rigashi shigowa ta zauna tana matsa masa qafa tace “baby anya yar qauyen nan qanwarka ce?” Cikin hassala yace “bansani ba kada ki Kuma tambayata game da ita meye damuwarki da sanin wacece itan?” Jan bakinta tayi ta tsuke yaja tsaki ya miqe ya shiga dakin da baya amfani dashi a gdan ya soma gyarawa kasancewar shima kamar dakinsa yake da katifa da wardrobe da TV na bango sai bathroom,
Gyara yayi masa na sosai sannan yayi wanka ya fito ya fice daga gdan cikin gari ya shiga ya nufi wani Mall ya siyowa Juhud kaya bazai iya tantance tsayinta ba Amma ya qissimata da Ya’isha qanwarsa duk kayan daya diba mata qananu ne sai hijjaban sallah ya koma gda ya tarar da Christy a kitchen tayi masa sannu ya Amsa Yana shigewa dakin daya gama gyarawa ya zuba kayan a wardrobe ya dauki mukulli ya fito Christy ta tareshi da cewa “ga abincin petiant din nan am naji kamar tace sunanta Aminatu ko?” Warmer din kawai ya karba ya fita ya nufi asibitin lkcn ta shiga wankan da Nurse Karima ta takura mata tayi kasancewar an kwance bandejin saura dinkin ta Nina mata yanda zatayi wankan sannan ta barta koda ta gama wankan ta dauki riqarta ta mayar ta fito riqe da towel din da Nurse Karima ta bata domin daurowa.
Da sauri tayi baya jikinta ya kama tsuma tana ganinsa ta tuna da dukan da yayi mata dazun ya kuwa daure fuska yace “kici abinci na kaiki gda na gaji da yawon asibitin nan ba Mai martaba ne babu lfy ba ba Mom ba” ajiyar zuciya tayi ta rinqa takowa da sanda dariya kecin Karima babu halin yi, a haka harta iso ta karbi doguwar riga ta rinqa juyata a hannunta tana kallon duwatsun jikinta sai ta ajiye ta Kuma daukar wata taga har tafi ta farko kyau a haka Saida ta gama qarewa kayan kallo duk ta ajiye ta dauki rigarta ta Fulani zata mayar Karima tayi saurin riqewa tace “meyesa bazaki Sanya wadannan ba?”
Turo baki tayi tace “dagawa da almubazzaranci niba yar kowa ba haka kawai nasa kayan sarakai salon asani a wutar jahannama …….. Kallon da ta dago taga yanayi matane yasata rufe bakinta da hannunta yayi Alama da yatsansa Karima ta dauki wata milk ta miqa mata ya kafeta da idanu babu yanda ta iya hakansn ta karba tasa tana qunquni tana hawaye ita a dole anyi mata laifi ansata almubazzaranci.????
Flat ya dauka ya zuba mata tuwon shinkafar da miyar agusi da tantaqwashi da qashin rago ya aje mata a qasa ta ya sake kafeta da idanunsa tayi qasa da nata tare da zama a qasan ta Sanya hannu tana jajjagula tuwon tana gutsurar gaya tanaci idan ta dauki saita goge miyar sannan takai bakinta, Karima ce taga abin yayi yawa tace “meyesa bakicin miyar” kamar me jiran kadan kuwa ta fashe tace “bayan mun fada muku kudaina cinye kaza da shanuwa da tumaki Amma kunqi ku Kadawan nan bakuda Imani nikam bazanci nama ba idan naci sai Allah yayi Mana hisabi”
Ba Karima ba shi kansa Saida ya murmusa ya zubanta ido yanda take tsakurar abincin take karkade miyar abin yaso bashi dariya saidai bazaiyi ba ta samu fuskar rainashi haka ya tsaya akanta Saida ta cinye tuwon sannan ya zauna yana karkada qafa yace “uhum maza cinye naman ki shanye miyar….” Yanda ta zaro ido yaso yasa dariya ta kubce masa ya maze yace “idan kinqi” hannu yasa Yana qoqarin zare belt dinsa tayi saurin daukar kwanon ta kafa baki ta shanye miyar tas sannan ta rinqa yagar naman kamar tana yagar jikinta har Saida ta cinye ya miqe ya dubi Nurse din yace “tayata fito da kayan nan zata koma gda ta rinqa zuwa ganin likitan kafin ta qarasa warkewa” ficewa yayi Karima ta debi kayan ta fita ta miqe tabita da sauri ai tana zuwa jikin motar ta cake taqi gaba taqi baya tsoro ya kamata ta janye ta koma gefe ta rakube bayan sun gama zuba kayan ya juyo ya kalleta tayi wani kalar tausayi ta sakeyin raurau da fuska yar fara’ar da yakeyi ya daina yace “kizo ki shiga mu wucce malama” girgiza masa kai tayi ya cije lebe a fili yace “ciwon kai wannan yarinyar zatayi taurin kan tsiya” itadai bataji me take cewa ba Kuma bata bar inda take ba Saida ya daka mata tsawa tayi saurin nufar motar tana zuwa gabansa ta zube cikin in…Ina tace “ka rantse bazaka saidani ba Baffa’am yace masu sulluwa suke sace mutane suna kaiwa burnin Kano da Lagus suna saidawa anayin fate²nsu………….