HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

 

Please share

 

Page 19-20

Duƙewa Nazifa tayi tana jin mararta na ƙullewa ga wani azababen ciwo da ya dirar mata lokaci guda,zaunawa tayi dirshen ba tare da ta shirya hakan ba.Zufa ce ta karye mata,banda sunan Allah babu abinda take ambata jin ciwon sai gaba ya ke ƙugunta ma ya ɗauka.Tana nan zaune sai ga Balkis kamar an jefo ta,da sauri ta nufi Nazifa tana cewa “anty Nazifa lafiya kika yi zaune da ƙasa ai sai ki ɓata kayan jikin ki”shiru Nazifa ta kasa cewa komi sai sac ɗin ta da ta miƙa ma Balkis “kira Nurrr” ta faɗa kamar ranta zai fita,wayar ta ciro daga jakka bugu biyu ya ɗauka “anty Nazifa ce lafiya ka tawo”shine abinda Balkis ta faɗa ba tare da ta ko amsa sallamar malam Nur ba.

Su na nan zauna Balkis sai faman jera mata sannu take sai ga malam Nur,ba tare da ya tsaya tambayar ta mi ke faruwa ba ya ja ta zuwa mota.
Gidan baya ya saka ta Balkis ita ma ta zagaya ta shiga ta ɗaya ɓangaren.
Su na zuwa asibiti aka tabbatar masu da haihuwa ce,gida malam Nur ya koma sai ga shi sun dawo shi da Maman kamin daga bisani ya kira Inna ya shaida mata.

Su na nan zaman jira sai ga yayar Inna,sama-sama suka gaisa da Maman bayan malam Nur ya gaisheta “Allah dai ya sauke ta lafiya”cewar Lami yayar Inna da “Amen “dukan su suka amsa.Sai da Nazifa ta kwashe wajen awa uku sannan Allah ya sauke ta lafiya,ta haifo kyakyawar ƴarta mace mai kama da ubanta.Cike da murna nurs ɗin ta fito ta shaida masu Nazifa ta haihu da sauri malam Nur ya tambayi abinda aka samu nurs ɗin tace “mace”a take fara’ar fuskar malam Nur ta ɗauke dan shi a tsarin shi ya fi son ya samu namiji daga farko.

Balkis kuwa har da tsalle jin sun samu baby girl,rashin jin daɗi malam Nur ya nuna ƙarara wanda har Maman ta lura da hakan.
Ganin hakan yasa ita ma taji sam ba ta son mace namiji take so dan burinta bai wuce a maido sunan Ali duniya ba wato marigayi mijinta.Lami kuwa ta na can inda nurs ke duba lafiyar baby,bayan sun gama bincike suka naɗota a zane suka ba ta.

Jiki sukuku Lami ta nufi su Maman dan ba ta san yadda za su ɗauki al’amarin da likitoci suka shaida mata ba,da sauri Balkis ta nufi Lami tana kallon babyn wadda kallo guda za kayi mata ka hango zallar kamarta da malam Nur.
Karɓar ta Maman tayi tana kallon yarinyar kuma sai Allah ya jarabce ta da jin mugun sonta,kallon idon yarinya ta fara yi uwanda su ke farare tass sai ɗan boule ɗin su wanda ya ke kamar h color dan bai da baƙi sosai.
Murya na rawa Lami tace “ta ta *ƘADDARA* kenan haka Allah ya nufa ta kasance a *makauniya* ,sai mu yi fatan Allah sa makantarta ta ita ce alheri gare….”da sauri malam Nur ya katse yace “Makauniya?kamar yaya?”kafin ya karɓi babyn daga hannun Maman ya ƙura mata ido, tabbas idonta sun nuna ko a kallo za ka gane.A razane malam Nur ya ɗago ya kalli Maman ya na cewa “Maman dagaske fah Makauniya ta haifa mani”ba Maman ba hatta likitocin da ke tsaye kusa da su sai da suka yi mamakin furucin malam Nur,ita kuwa Balkis fashewa tayi da kuka tana girgiza ma ɗan uwan nata kai tace “sam ban tsammaci haka ba daga gare ka yaya Nur,ina imanin ka ya tafi har kake faɗin haka?kar ka manta kai Malami ne ka san yadda Allah ya so ya ke yi ba wai neman shawara ba”masu kararra zuciya irin su Lami sai da suka goge ƙwalla jin bayanin ƙaramar yarinyar da ba tafi 18ans ba amman babba mai hankali kuma malami ya kasa gane *ƘADDARA* Ubangij zuwa ta ke ba tare da an shirya ba.

Maman ya miƙa ma babyn yana jin zuciyar shi na zafi,sam ya kasa ɗaukar lamarin ta yaya ɗiyar shi ta farin za ta kasance Makauniya?laifin mi yayi ma Ubangijin shi? Da wannan tunanin ya nufi ɗakin da ya ga an kai Nazifa ciki.A kwance ya tarar da ita hannun sanye da ƙarin ruwa sai numfashi ta ke saukewa akai-akai,ka na ganin ta ka san ta sha wuya ba ƴar kaɗan ba.
Ido ya zuba mata yana jin zuciyar shi na bugawa yayinda ƙaunarta ke linkuwa a ciki,ƙarasawa yayi ya tsaya ku san kanta yana kallon lumshashin idonta da suke zubar da hawaye.Kamar daga bisa yaji tace “ba kayi murna ba saboda na haifi mace ko?duk lokacin da kace min namiji kake so ina samun kaina da tsinkewar zuciya dan ban san abinda Allah za…”da sauri ya rufe mata baki ya shiga share mata hawayen tare da kwantar mata da hankali,bai bar wurin ba sai da ya tabbatar ta saki ranta.

Maman da Lami ne suka shigo,tashi tayi ta karɓi yarinya da ta fara kuka Lami na gwada mata yadda za ta shayar da ita.Cike da kunya ta ke bata abincin ta, Balkis kuwa na gefenta ta kasa ta tsare sai kallon babyn take “amsar ta ai ta ƙoshi”cewar Nazifa tana mai miƙa ma Balkis bbyn,amsar ta tayi tana dariya ta dawo ƙasa inda su Maman ke zaune bisa tabarma.

Malam Nur ne ya shigo bakin shi ɗauke da sallama, ledodin hannun shi ya ajiye ya na tambayar Nazifa jikinta,gefe ya zauna yana latsa waya sai shating ya ke hankalin shi kwance kafin kuma ya miƙe ya fita.Sosai Nazifa tayi mamakin rashin ɗaukar baby amman sai ta bar shi akan ƙila bai iya ɗaukar jarirai ba.

 

Kwana Nazifa ɗaya a asibiti aka sallamota,amman ko take Sappa ba ta zo ba.Ƴan uwa na nesa da na kusa kuwa suna ta tururuwa zuwa wajen barka,Samira dai ango Jabeer ya hana yace sai ranar biki zai kawo ta.

Sha tara ta arziki Maman ta haɗa ma Nazifa ita da ɗiyarta,kayan jarirai kala-kala wasu ma sai ta shekara ba ta sa su ba.Wannan bajintar ba ƙaramin daɗi tayi ma Nazifa ba dan ko ba komi hakan ya nuna ana son ɗiyarta.

Ranar suna yarinya ta ci sunan *Laila* ,malam Nur da Nazifa anko su kayi na blue gizner.
Nazifa na tsaka da cin biki sai ga Sappa kamar wadda aka yi ma doli ta shigo ɗakin,kwalin sabulu da kayan jarirai ta miƙa Samira ita ce kusa hakan yasa ta karɓa ta na godiya Nazifa kuwa cike da mamaki take kallon Sappa dan har ta mance da ita.
Juyar da kai tayi gefe sai cika ta ke tana batsewa wanda ba komi ne ya jawo hakan ba sai kyautar gida sukutum da Maman ta bayar ga jikanyar ta.

Malam Nur angon jego shi ma ya na can waje shi da abokan shi suna taya shi murna,amsawa kawai ya ke dan babu yadda zai yi amman har ga Allah bai son yarinyar.
Kafin bayan sallah magrib kowa ya watse ya rage ƴan gidan,wanka Nazifa tayi ta fito ta na shafa mai sai ga malam Nur.
Gaishe shi tayi ya amsa kafin ya fara bincike cikin tiroir “mi kake nema?”Nazifa ta tambaya shiru yayi bai tankata ba sai cigaba yayi da abinda ya ke.

Cike da jin haushin share ta ɗin da yayi ta fito falo inda Lami ke yi ma baby Laila wanka sai ƙara take ta na kuka.Ka sa jurewa Nazifa tayi tace “Inna Lami a barta haka nan tunda ba wata dauɗa gare ta ba”dariya Inna Lami tayi tace “oh!Ni yaran yanzu babu ta ido ƙiri-ƙiri kuke nuna son ɗiya” “ba haka ba ne Inna Lami kawai na ga sai kuka ta ke ne ya kamata kuma a barta haka”cewar Nazifa ta na mai ɗauko ƙaramin towel wanda za a naɗe Laila,”ba wani son ɗiya ne mana,mu lokacin mu yaro ko huta muka ga zai taɓa ba zamu janye shi ba saboda kunya amman ku da ya ke yaran zamani ne wankan ruwan zafi ma ba ku haƙuri ayi ma yaren ku”kai Nazifa ta sosa alamun jin kunya kafin ta ce “ruwan ne da zafi ko sirkawa bakwa yi”aza mata baby Laila tayi kan towel ɗin da ta riƙe tun ɗazu tace “ke kike ganin zafin su amman ita daɗin su ta ke ji saboda yanayin jikinta da ya ke da taushi balle ma yau da ta sha ɗauka jikinta yayi yami doli a gasa ta”Nazifa dai ba ta ce komi ba sai gashin Laila da ya kwanta luf ta ke shafawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button