HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

Please share

 

Page 27-28

Wani murmushi budurwa tayi tace “da ka aje wannan girman kan na ka da zai fi yi ma,saboda tunda shugaba tace a kawo mata kai doli sai ka je.Dan haka ka tashi ka biyo bayan mu ta salin alan ko kuma mu tafi da kai ta ƙarfin tsiya”ɗagowa Tajdeen yayi yana kallonta tabbas murɗaɗen jikinta ya nuna ita ɗin mai ƙarfi ce amman bai yi tunanin izzarta har ta kai haka ba,toh wai shin ma wacece shugabar da take magana?Feedy kamar ta san abinda ya ke tunani tace “in mun je can idon ka ya gane maka ita,ka tashi mu tafi umarni ba shawara ba”ta faɗa ta na mai gwada mashi wata carte mai nuni tafi shi matsayi,miƙewa yayi yabi bayan su ba dan tsoro ba sai dan ƙa’idar aikin soja ne doli kayi ma na gaba da kai biyayya.
Sun yi ƴar tafiya mai nisa sannan suka ratse suka bi wata ƴar siririyar hanya kafin kuma su ɓullo ta wani tsararren wuri mai kyau mai ɗauke da shibke-shibke da furenni.Ɗaki guda ne tal wajen a nan suka tsaya tare da ƙwanƙwasawa “Come in”aka basu izini,Feedy ta buɗe ƙofar tare da yi ma Tajdeen alama ya shiga ba muso ya wuce ta rufe ƙofar suka tsaya a waje.
Wani sihirtacen ƙamshi mai cakuɗe da sanyi AC ya ratsa Tajdeen,lumshe ido yayi na ƴan sakanni kafin ya buɗe su kan wata matashiyar budurwa wace ba za ta wuce 25years ba.Murmushi ta sakar mashi tace “T.Deen ya na ga ka tsaya ba ka ƙaraso ba?”wata irin faɗuwa gaban Tajdeen yayi saboda tsananin daɗin muryata da ya ratsa kunnuwan shi,a hankali ya fara taka lalausan capet ɗin da ke shimfiɗe a tsakiyar ɗakin ba tare da ya shirya ba sai ganin shi yayi tsakiya salon.

Da idonta masu saye imanin duk ɗa namiji tayi mashi nuni da salon,zaunawa yayi yana kallon ta yana mai yi ma Allah tasbihi a zuci kuma faɗi ya ke “Allah yayi hallita nan”karo na farko da ya taɓa jin macce ta burge shi.
Cike da kuri da yanga ta miƙe ta tsiyaya lemu ta bashi,kai ya girgiza ya saita nutsuwar shi yace “a ƙoshe ni ke ki gaya min abinda ya sa kika kira ni”murmushi kawai tayi ta shiga latsa waya.An fi minti talatin tana dadanna wayar ta kafin ta buɗe baki kamar wadda aka yi ma doli tace “sunana Amrita Ƴa ɗaya tilo gun général Diore “taɓe baki Tajdeen yayi jin yadda ta ke wani taɗa kanta saboda kawai ta na ƴar shugaban su,ɗagowa tayi ta na kallon shi tace “ko ba ka ji abinda na ce ba?”yace “naji sai aka yi ya?dama kawai dan in san ke ƴa ce ga shugaban mu kika sa na bar abu mai muhimmanci?”ƙurrr tayi mashi ido jin yadda ya ke ɗaga murya a gabanta ya na nuna shi mai zafin rai ne.
“Na fara faɗa ma ne dan ka san da wa kake magana amman da alamu kamar ba ka san wanene général Diore ba”tsuki Tajdeen yayi dan tabbas ta bashi haushi yace “kin ga in ba ki da abun faɗa sai an jima kin ga tafiya ta”ya faɗa ya ne mai miƙewa tsaye.”

Tako ɗaya biyu yayi ya juya da nufin fita yaji saukar tatausan tafin hannunta ya jimƙi muscule ɗin shi,a fusace ya juyo tare tureta can gefe ya nanata da yatsa alamun kashedi kamin ya buɗe kofa ya fice ran shi suya.

Banko ƙofa yayi yana huci su Irfan duk suka miƙe suna kallon shi,cikin takaici ya dubi abokan na shi yace “wai ita taƙamar ta ɗiyar général ce,shiyasa ta wani shanya ni kamar wani garin tuwo mtws na tsani mutum mai girman kai”kafaɗar shi Irfan ya dafa yace “wannan ta wuce duk inda ka kaita,duk wani launin wulaƙanci na duniya babu wanda ba ta da shi.Mi tace maka da ka tafi ?”yadda su kayi ya kwashe ya gaya ma su,dariya Faruk yayi yace “da fatan ka san fa’idar kiran na ka da ta yi?”kai Tajdeen ya girgiza Faruk yace “to ka buɗe kunnuwan ka da kyau ba komi yasa ta kira ka ba sai dan kawai ka biya mata buƙatar ta,Amrita hatsabibiyar ƴar iska ce rabin sojawan da ke wannan compagnie ɗin duk ta lalata su, ba kai ne na farko ba da ta fara nema”buge mashi baki Tajdeen yayi ya tofar da yawu yace “Allah kiyaye ka bar ƙaƙaba min ita domin ni ba ta neme ni ba,su ma sauran da son su in ba haka ba ta yaya macce za ta lalata namiji?”murmushi Faruk yayi yace “banda cika baki malam,in tambaye ka tsakanin ka da Allah kyawun ta bai burge ka ba?”tsuki Tajdeen yayi yace”to shine mi?”Faruk yace “shine kau wani abu domin da shi take ɗana tarko dan mafi akasarin maza suna zama lusarai gaban kyakyawar macce”
“Toh ni banda ni”cewar Tajdeen”aikin banza na nawa kuma?wai an ce ma kuturu Allah ya la’ance ka,ina ce dai yanzu ka gama faɗin Allah yayi hallita nan,to bari kaji ina mai tabbatar maka ba za ka tsallake tarkon ta na gaba ba dan na san ba wai ƙyale ka za tayi ba ta soma bibiyar ka kenan har sai ta cimma haƙarta”
Da alamomin tambaya kan fuska Irfan ya kalli Faruk yace “kar dai ace kai ma ….?”kai Faruk ya jinjina yace “ƙwarai kuwa wancan zuwan da mu kayi na gamu da ita a hanyata ta dawo lokacin da na fita neman réseau ka tuna?”da sauri Tajdeen yace “kar ka gayi dan Allah in dai ba alkairi ba ne” “ina ruwan ka kai ya ke tambaya?ka faɗa min”cewar Irfan ya na hararen Tajdeen, Faruk ya cigaba da cewa “da farko da kalamanta ta fara cutata ta hanyar yabo da kyakyawa daga nan fah shikenan na shiga hannu”tabkar shi Irfan yayi yashe “shege nawa shiyasa mu ka ga ka daɗe amman da na tambaye ka sai ce min kayi katin waya ka fita nema”gira Faruk ya ɗaga yace “ta ya zan faɗa ma wannan sirrin”tsuki Tajdeen ya ja “sai kace wani sirrin ƙwarai ni kun ga tafiyata”ya faɗa ya na mai ɗaukar sac au dos ɗin shi ya goya,ba su yi wani ƙoƙarin hana shi ko tambayar shi ba suka cigaba da hira su ta ƴan duniya.

Da dadare kamar daga bisa sai ganin su Feedy su ka yi tsakiyar ɗaki”ya na ina?”shine abinda tace “ya fita ba mu san inda ya tafi ba kuma sai dai ko in yi remplacer shi”Irfan ya faɗa ya na kashe ido,ba tare ta tanka shi ba ta fice maƙarabanta suka take mata baya.

Cike da masifa Amrita tace “gidan ubanwa ya tafi?shine kuma ba ki tambaye su ba?”cikin jin haushin abinda ƙaramar yarinyar ke yi mata Feedy tace “ki yi haƙuri shugaba ai akwai wani ɗan kyakyawa zan iya kawo maki shi kafin shi T.Deen ya dawo”juya mata baya tayi tace “ok!”da sauri Feedy ta koma wajen su Faruk tace ma Irfan “ka zo…”cike da jin daɗi ya bi bayanta,ita tayi mashi jagora har ɗakin Amrita sannan ta juyo tana ta zaginta tare da Allah wadarai da halayya Amrita.

 

A ɓangaren Tajdeen kuwa mashin ya samu ya kai shi can cikin gari daga nan ya ɗauki mota mai zuwa yankin su,cike da kewar iyayen shi ya shiga gidan yana ƙwala kiran Mom .
Da sauri ta fito hannunta riƙe da plate ta na kallon ɗan na ta cike da soyayya da kuma kewa,hannuwanta ta buɗe alamun ya zo amman sai ya kasa saboda ganin rashin dacewar haka duk da ita ɗin mahaifiyar shi ce amman sanadiyar Muslunci da ya karɓa sai yaji ba zai iya yin haka ba.

Da murmushi ya ƙaraso ya duƙa ya taɓa ƙafafunta kamar yadda ƴan India ke yi,kan shi ta dafa tace “Allah shi yi maka albarka”ɗagowa yayi yana mai amsawa da “Amen”hannun shi ta ja suka shiga main falo,direct inda Père ke zaune kishingiɗe akan kujera ya tafi “Barka da zuwa jikana”Père ya faɗa yana matse yatsun Tajdeen da suke hannun shi “yauwa ɗan tsohon kakana da fatan na same ku lafiya?”Père yace “lafiya lau sai dai rigimar matar ka ta hana ni saƙat kullum tana kan ƙafafuna tana shammata ta”kalmar MATAR KA ya nanata a rai kafin yace “halan shegantaka ta ke yi ma”Père yace “sosai ma wai fah farin gashin kaina ta ke ma dariya wai kamar giginya”dariya Tajdeen ya tuntsire da ita yana gaida Dad da fitowar shi kenan.
Lokacin Sallah magrib yayi amman babu damar yi dan tuni ahalin gidan sun haɗu a table za’a cin abincin dare,a haka Tajdeen ya daure ya ke cin mulmulalen tuwon shinkafa gefe guda kuma Mari ce ke ta zuba mashi surutu,wani ya amsa wani kuma yayi dariya duk rabin hirar akan Père ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button