HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

“Duk wacce ta san ta zo lati ta tashi tsaye”shine abinda malam Nur yace yana mai buɗe coffre ya ɗauko dorinar shi,Allah ya isa suka fara jama Rabi’at kafin su fara miƙewa tsaye.

“Dan Allah ki tashi ki ba mara Ɗa kunya saboda ke ne suka tuna ma malam zancen bulalar lati amman an fi sati rabon da ayi ta”cewar Samira ta na mai jimƙe hannun Nazifa , murmushi ta sakar ma ƙawarta ta kamin ta mike tsaye.

Bulala goma-goma malam Nur ya shiga zabga ma Ɗaliban har ya zo kan Nazifa,daure zuciya yayi ya shiga tsula mata bulala duk in ya shauɗa sai ta rumtse ido dan zafi har aka gama mata.

Zaunawa suka yi suna jinyar jikin su dan duk juriyar ka in malam Nur ya zane ka sai kaji jiki,karatu suka fara yi kamar kullum har lokacin shan iska yayi.

“Naziii…”shine abinda malam Nur ya faɗa ganin ta nufi ƙofar fita,dawowa tayi tana turo baki.Ajiyar zuciya ya sauke tare da furzar da huci yace “sorry”ɗagowa tayi tace “da aka yi mi fah ” “da dorina ta zane ki”baki ta sake turowa tace “ai kai ka sanya ta”da idasa maganar kamar za tayi kuka “nooo!kar kiyi kuka zan ko hukunta ta dan ba za ta sake kwana duniya ba ƙonata zan yi cikin huta tunda har ta taɓa fatar amarya Nur”dariya Nazifa tayi har da ƙyarƙyatawa nan dai su ka fara karatun litattafai kamar kullum.

Bayan an dawo daga shan iska maimakon a cigaba da karatu sai malam Nur ya ɗauki rigar rashin mutumci ya saka,nan ya shiga yi ma ɗaliban da suka sa ya ɗaki Nazifa masifa inda ya ke cewa “ku a tunanin ku har za ku iya yi ma malam Nur wani ƙulli wanda ba zai gane ba?ribar mi kuka ci da na daki Naziii?ke kuma da kika fi su fitsara sai suka turo ki ki min tuni da bulalar lati ko?”cikin son kare kai suka fara rantse-rantse shi kuma ya katse su da cewa “miyasa kwanakin baya baku tunan min ba sai na yau?duk ƙiyayar da kuke nuna mata na sani ba tun yau ba dan haka zan ba kowacen ku hutun sati guda duk wacce ta san da sa hannunta ciki ta tashi ta fita”ya na gama rufe baki munafukan duk suka fita waje.
Wannan abun da malam Nur yayi shi wanke zuciyar Nazifa da duk wani ƙunci har ta mance da maganar wata Sappa.

 

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka zo yau saura kwana biyu biki,duk ɓangaren uku shirye-shirye kawai su ke Sappa ta koma gidan su tun tuni mahaifiyar ta sai ƙara gyara ɗiyar ta take.Inna ma ba albarta a baya ba sosai ta ke kula da Nazifa wanda hakan ya sa ta ƙara haske tayi wani freshe sai ƙyalli take da santsi.
Darul Mar’a malam Nur ya biya kuɗi tun daga gyaran jiki,farce,gashi da lalle,sosai tayi kyau ka na ganinta ka ga cikakkiyar amarya ƙawayenta sai ɗaukar ta hoto su ke.

Ranar ɗaurin aure duban jama’a suka shaida auren Nuradeen Ali Ɗan Masani da Nazifa Sa’id Lawan da kuma Sappa Hamisu Kabeer,mutane da dama sai mamaki su ke jin mutum guda ya auri mata biyu duk ɗaya rana.Ɗalhat da shi ya bayar da auren ƙaunar tashi sosai ya girgiza jin ba ita ɗaya ba ce,a zuci ya ke tunani “ƙila shiyasa Inna tace min zan ji wani a wajen ɗaurin auren amman kar na tada hankali na,to ko shine abinda malam Nur ya zo ya gaya ma Inna a jiya”ganin dai bai dai amsar tambayar ya ƙarasa wajen baƙin shi su ka nufi gida kasancewar ɗaurin auren masallaci ne.

Sosai Nazifa ke kuka wanda ta rasa na miye na farin ciki ko akasin haka,yau dai ta zama NazNur…….

 

Please share

Jikar Rabo ce????
[24/07 à 10:56] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)

Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????

*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM

Dedicated to *Amana Writers Associations*????????

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________________________________________________

“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????

*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

Page 11-12

Danƙareren gida ne na musamman mai part biyu,ko wace ciki uku da falo ne aka yi mata.
Nazifa banda kuka babu abinda ta ke ta wani riƙe Samira tace babu inda za ta,a na haka sai ga sallamar ango da malam Jabeer.
“Yauwa ga angon ki nan ai yanzu sai ki sake ni”cewar Samira ta na kallon na ta sahibin,sallama suka yi masu da fatan alkairi na farin ciki mai ɗorewa kafin su wuce.

Murmushi mai ɗan sauti malam Nur yayi wanda har sai da taji cikin ƙahon zuciyarta,mayafin da luluɓe ya ɗan ɗage nan kyakyawar fuskarta ta bayyana wacce tayi shaɓe-shaɓe da hawaye,wani murmushin ya ƙara tare da cewa “amincin Allah ya tabbata ga Shalele ƴar gatan malam Nur, Mama su Ayman da Laila”Nazifa dai tun da ya fara magana ba ta ɗago ba sai da ya zo ƙarshen maganai ne tayi saurin rufe fuska tana dariya.

“Tashi ki yi alwala ki rama sallah da ba kiyi ba,ina zuwa”ya faɗa tare da fita ita kuma ta miƙe ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah magrib da isha’i wanda ba ta samu tayi ba saboda cawaniya biki.

Malam Nur ledodin da suka bari a falo ya ɗauki biyu ya fita zuwa ɓangaren Sappa wacce ta cika tayi pam kamar za ta fashe dan tun lokacin da suka shigo shi da malam Jabeer akan idonta.

Tura ƙofa yayi tare da yin sallama,can tsakiyar gado ya tsinkayota ta sha kwalliya kamar wata aljana.Ido cikin ido su ke kallon juna,babu abinda malam Nur ya tsana irin wannan kwalliyar mai sauya ma mutum kamanni,baki ta turo ganin yayi tsaye bakin ƙofa bai zo gun ta ba.
“Wa’aleykum salam”ta faɗa cikin jin haushi taɓe baki malam Nur yayi kafin ya ajiye mata ledar gasasar kaza da ta fruits da jus,yace “sai da safe in Allah ya tashe mu ki zo ki ƙulle ƙofa”wani irin dirowa Sappa tayi daga kan gado ta na mai cewa “kai kuma ina za ka je?”banza yayi da ita ya fice.
Zuciyarta na zafi taje ta rufe ƙafo ta dawo ta haɗe kai da gwiwa tana rusar kuka.

 

Malam Nur sai da yayi wanka a ɗakin shi tare da alwala sannan ya tafi gun amarya,a zaune ya tarar da ita tana ƙare ma ɗakin kallo ba laifi Inna ta fidda kuɗi an yi mata meubles masu kyau daidai ƙarfin su.Gyaran murya yayi ta juyo ta na kallon shi sai kuma ta maida kai ƙasa tana wasa da zoben hannunta,”amar su a tashi mu yi sallah godiya ko?”ya faɗa lokacin da ya zo dab da ita,miƙewa tayi ta shimfiɗa wani tapis daga gaban nata malam Nur ya hau ya ja su sallah suna gamawa su kayi ƴan ciye-ciye kafin su gabatar da sunnah Manzon Rahaman.

 

Asubah farin Nazifa ta farka,cike da jarumta ta miƙe ta faɗa toilet ta haɗa ruwan ɗumi tayi wanka game da alwala.
Har sai da ta gama raka’atil fajir sannan malam Nur ya farka,shi ya canza zanen gado ya wanke a injin wanki sannan yayi wanka ya zura jallabiya zuwa masjid.

Sai da rana ta fito wantsar sannan malam Nur ya dawo gida dan wannan sabon shi ne duk bayan sallah asubah masallaci ya ke zaunawa yayi ta azkar.Har zai shiga ɗaki sai kuma ya ji motsin ta a kitchen,a hankali ya ɗaga ƙafar shi zuwa can kitchen ɗin ya jingina da bango ya na kallonta ta na zuba ruwan zafi a Flask,ba ta san da zuwan shi ba sai ji tayi yayi huging na ta yana murmushi mai sauti “bonjour !”ta faɗa a kunyace lokacin da ya juyota suna facing juna, hanci ta ya ja kafin yace “bonjour qui ?haka ake gaishe da miji ko ɗan sunan nan na masoya ba za’a saka ba”malam Nur ya faɗa yana mai zuba mata ido,turo baki tayi tace “to ka sake ni sai na faɗa”waro ido yayi yace “au!sai na sake ki zaki faɗa?to bari ki gani”dariya tayi jin ya sungumeta kamar wata baby,kan bed ya direta ya luluɓeta da blanket “yi kwana kwanta ki huta”ya faɗa yana mai dadaɓata tare da hura mata iska a fuska,lumshe ido tayi tana jin soyayyar mijinta na ratsata kafin wani lokaci har barci ya ɗauke ta.Murmushi malam Nur yayi ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin wata rantsatsiya gizner H color,zaman hullar kan shi ya gyara ya ɗaura agogo a tsintsiyar hannun shi na dama tare da fesa turare ya nufi part ɗin Sappa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button