NOVELSUncategorized

INA TARE DA ITA BANSAN ITA BACE 125-END

INA TARE DA ITA!
????????????????????????????????
(bansan ita bace)
????????????????????????????????
Story & written by
mmn fareesa
????125&126
THE END
“” Doctor yace eh hjy ko batada aurene?”
da sauri Ummi ta ce ah ah da auren ta mana!kallan inna kuluwa tayi tace muje ,yyinda Jidda tayi shiru kamar ruwa yacita…


Suna tafiya inna kuluwa tace wa Jidda keeeeee! dan ubanki ina kikasamo ciki? ta fad’a cikin zare ido “
Ummi ta ce dan ALLAH ki rabu da ita ,muje gd tukum.
shiru ta yi ,yayinda Jidda tayi k’asa da kai “suna zuwa gun motar ,tun kafin su shiga yah Muhammad ke tambayar Ummi meke damun jiddan?” Kallon data masane yasakashi yin shiru ,yaja motar bayan sun shiga.
Sai dai aransa yana tunanin toko Jidda tace musune yana kusantarta ne dan tunda yalura ta fara period yafara kusantarta ,yaita mata dad’in baki har taruka aminta dashi.
Tsit sukayi bbu mai mgn a motar,dan Ummi abin yafara bata tsoro akan rashin kunyar yaran gdn ,dan inbata mantaba jiya ta kama yah Usman yana kissing d’in Fatima…Ashe yau kuma zataga mai kankat,dan tasan tabbas cikin Jidda na Muhammad ne.
Ajiyar zuciya tayi data tuna amasu auren kaf shine k’araminsu ,dudu shekararsa 23 yanxun shine har yaba Jidda ciki,lallai gara da aka yimasa aure ….dama abinda abbu ya ankarar dasu kenan lokacin da suke cewa wai Muhammad yyi k’aranta da aure….parking din da yyine yasakata dawowa tunaninta.

Bayan sun fito,tayiwa inna sallama had’e da fatan samun lfy ga Jidda tayi part d’in mommy dan kai mata labarin abinda Muhammad yyi…yayinda su Jidda suka nufi part d’in su ,yah Muhammad namata alamar ta tsaya ta masa banxa tayi tafiyarta dan ta lura da kallon da inna ke mata.,,,,,,
Suna isowa a waiting parlour suka sami atine zaune ,ko gaisawa basuyiba, inna kuluwa ta sakarma Jidda wani gigitaccen mari mai rai da lfy, had’e da cewa dan uwarki ina kikasamo ciki?”
Innalillahi wa inna ilaihir raju in,baba atine tace had’e da Jan yo Jidda jikinta datake shirin fad’uwa sbd zafin Marin”ahankali ta maimaita ina tasamo ciki kuma inna kuluwa?” aikema kinsani tunda da auren ta ,sai a godewa ALLAH…… Inna ta katseta da cewa kinada tabbas ne akan hakan?”dan ubanki bazakiyi mgn ba……da sauri Jidda dake kuka ga kuma zafin marin tace umm…umm dama…damah ai ance duk abinda yamun karna fad’a ,shine kullum innaje gyaramasa daki sai yyimun….da sauri atine tace ya isa tashi kishiga ciki kici wani abu kisha magani…sum sum tabar parlourn…
“bayan fitarta atine tayi ajiyar zuciya afili tace oh ikon ALLAH ” toko gsky dole su tare Ai bata haihu ananba….inna datayi mutuwar zaune ,cike da al’ajabi tace to badoleba atine abin da kunga ,ni yanxun mezancewa mlm?” Duk da Dai matarsace ,amma ai da kunya….atine tace ai sai agodewa ALLAH da yasa da aure tsakaninsu, amma da ak’auye ne hakan tafaru.. wai! da anyayatamu wlh…inna tace ALLAH ya kyauta…
************
da dare su abbune da daddy, Abba sai mlm ,zaune a parlourn baki suna mgn kasan Cewar Ummi ta sanar da abbu komai game da Jidda d Muhammad, itama mommy ta sanar da daddy ,inna ma haka..
Abbu yyi gyaran murya had’e da kallon mlm yace to wlh mlm kaji abinda ta gayamun.
Yaran zamani kenan bbu kunya atare dasu,dan ALLAH mlm kayi hkuri ba laifin jiddan bane ,laifin yana ga marar kunyar taron nan….murmushi mlm yyi had’e da cewa ni bana laofinsuba su duka sbd matarsace halal d’in sa a addinance basuyi wani laifi ko rashin kunyaba,sai dai a al’adance ake ganin sunyi rashin kunya..
Iyayen suka ce hakane”
Mlm yace to inaga in bbu damuwa kawai su duka wad’and’a basu tarenba su tare inga zaifi kyau gsky ,afin abun yafi haka…daddy yakarbe da cewa hakane dan inbamuyi d gskeba to wataran ca za’ayi wata ta haihu acikin su…murmushi sukayi baki daya.,,,,,
Abbu yace eh insha ALLAH nan da sati 3 zasu tare duka sbd Suleiman yasayi wani fili babba abayan gidan nan zai turo shi cikin gdn to zaa yiwa kowa b’angarensa dan gsky banaso subar gdn nan nafiso muzama tsintsiya mad’aurinki daya “
gaba daya sukace hakane ,nan sukayi addua kowa yyi part d’in sa…
Yah Muhammad ne yyi sallama a waiting parlour na mommy….aciki ta amsa masa….fuska daure tace kai zo nan dama inason ganinka.
“ganin bbu wasa a fuskarta yasa yad’uk’a gabanta” batare data kallesaba tace Ashe ba kada mutunci ba kada kunya kota miyan bacci ko?”
da sauri yace mommy me kuma nayi?”
dakk’uwa tamasa ,had’e d cewa uwarka kayi,sunkuyadda kansa yyi k’asa “mommy tace wato dan ba kada kunya Ashe kunsantar yarinyar nan kake?” har gashi tasamu ciki…..zumbur ya mik’e baki washe yyi ihu had’e da tsalle yace yeeeeeeee! Nima zan zama daddy wlh gobe akwai party…..kuna ina yan uwana? ,kuji nasamu k’aruwa….d gudu yafice dg parlourn yana murna bebi ,takan mommy ba.
“Ita kuwa baki bude take kallon sa” byn yafita ta girgiza kai had’e da cewa oh ALLAH yashiryaka Muhammad, wato rashin kunya ajininka take…
*******
bayan 4weeks duk samarin sun tare ,bbu abinda suke sai soyewa ,Muhammad na like da jiddo ana shan love kuma
yana kula da ita sosai sbd cikin jikinta..gefen guda kuma zubaida cikinta ya tsufa ,yyinda ifti Manya ta yaye Khalil hartasamu wani cikin..
Iftihal ce zaune ,tana jiran dawowar yah Suleiman suci abincin rana,amma shiru”
Wayar ta ta fito ta kirasa,Amma be d’agaba,saida takira sau3 ,sannan aka d’aga…bbu mgn.
Ifti tace hellow!kawai saitaji muryar mace na cewa hellow wake mgn?
Wani mugun Sarawa ifti taji kanta yyi,da mummunan fad’uwar gaba, afusace ifti tace uwarkice! dallah kibawa mai waya ,wayarsa…d’it taji ankashe….
Wani irin tashin hankali iftihal ta Shiga ,tuni ta fara zufa ,sai hawaye afili take cewa ni yaya zai ciwa amana! dama ance nmj bashida tabbas.
Tafi minti 10 zaune zuciyar ta natafasa ta na kuna had’e da jin kanta na sarawa….Khalil yashigo parlourn yasha gayunsa ,da fara soyayya a hannun sa yanufo ifti yana cewa Anty gashi inji mommy…… azuciye ta hankad’asa ya fad’i kansa ya kurme ,yasaki ihun azaba….adedenan yah Suleiman yashigo d gudu yanufo gun Khalil….ifti cikin zafin rai tace kada ka koma zuwa guna ! basaonka dakaida mahaifinka…
Arazane yah Suleiman yakalleta ,yyinda yake rurrugar Khalil sbd gurin har yyi ja….cikin bacin rai yace me kike nufin iftihal me Muka mik?
Wani kallo ta watsa masa,hade d cewa banasonka ! maciyin amana ,na kiraka shine kki dagawa sbd kana tare d mace …wlh saika sakeni ,kuma zan kashe Khalil nakashe kaina,kai kuma ka dauwama da yar iskar Budurwar taka….
Tana fad’in hakan ta jawo wukar dake kan dining area zata cakawa kanta….yah Suleiman ya dunga bata hkri yana cewa ta tsaya ta saurareshi.
Wayar ta ta yi ringing kuma ringing din datasawa yah Suleiman ne ,ta ga number sa ,ta dauka batayi mgn ba ,matar tace nasan kece matar matar me wayarce ,kiyi hkuri nima tsintar nayi….sbd rud’u d kunya ifti takashe wayar ta zube kasa tana kuka.
Yah Suleiman yyi saurin kwantar da Khalil kan kujera ganin yyi baccin dole ,yanufi ifti.
Rungumeta yyi had’e da cewa angel kin ga illar zargi ko wlh wayar fad’uwa tayi gurin daurin auren cpt salim da sumy….cikin kuka tahau basa bahuri ,yashare mata hawayenta yace bbu komai….kafin tayi mgn anyi sallama …wata matace ayan Kwane tashigo sai wari take tana hawaye ,ta zube gabansu .
Tace Sunana Laure ,nice wacce Muka had’a kai d zulai Muka batar da iftihal dan ALLAH kugafarceni ,wlh na tuba naga darasi na rayuwa dan ALLAH kutaimaka min….. Yah Suleiman ya yatsine fuska had’e da cewa zaki iya tafiya, ganinkima yasa mungane kin saduda “ALLAH yashiryi masu irin halinku…..iftihal tace ameen kije munyaffe danmu munyi gaba …
Bayan shekara 5
Su ifti anxama manyan mata ,yaransu 4 ,3 ke gunsu ,Khalil yah Yusuf ya karbe sa.
Yyinda su duka samarin kowa yanada yaransa…baba atinema tanada yara2 mace d nmj.
Zaune suke acikin farinciki da k’aunar juna ,yanxun haka yah Suleiman yacanxa ginin gdn sbd yanxun Yakoma general Suleiman ammasa k’arin girma ,arzikinsa na bunkasa ….yazama babban matashi maiji da kansa kuma dan gatan matarsa……
Tamat bi hamdilillahi anan nakawo karshen wannan novel ,kuskuren danayi ALLAH ka yafemin ,kabani ladar abinda nayi dai dai.
Ina mik’a godiya ta ga d’in bin masoyana ,nagode nagode nagode!!!
Sosai ina muku fatan alkhairi sai mun had’e asabon novel dina insha ALLAH.
Nasadaukar da wannan novel ga dukkan masoyana…
ALHMDLLH
by
Mmn fareesa
????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button