Rayuwar Mace

RAYUWAR MACE 7

RM
         7

****Kayan ta hau tattarewa tana kuka sosai, duk da dama ta san akwai kalubale a gabanta amma bata taba hasashe ko tunanin rashin mutuncin Adam din ya kai haka ba, ranar da aka kawo ta? Ai ko jaka aka kawo masa a wannan ranar dai ya kamata yayi treating dinta da sauki.
   Bata san in da zata fara neman iron ba, haka ta dinga dubawa guri guri har lokacin tana kuka, sai da k’yar ta gano shi a dakin da take da yakinin nasa ne don yadda yake dauke da tarkacen kayan sa, zama tayi dirshan tana cigaba da kukan ta hau goge kayan daya bayan daya wanda duk da gugar su ya hargitsa su kawai dan ya wahalar da ita , bakar gajiya da  yunwa su suka fi damun ta, batun bacci kuwa babu shi dan ko jin sa batayi. Tana cikin gugar aka dauke wutar, duhu ya mamaye ko ina, tsoro ya kamata ta yunkura da sauri zata tashi, ta manta shaf da iron din sai ji tayi kafarta a jikin iron din,tayi kara da karfi zafin na shigar ta sosai. Jan kafar tayi ta dinga laluben hanya da k’yar ta fad’a dakin, ta hau laluben wayar ta amma bata samu ba, durkushewa tayi a wajen ta dinga kuka tamkar ranta zai fita,da dade sosai a wajen sai da taji kafar ta rage zugi ta sake lalubawa ta samu gadon ta haye ta kwanta cikin jin tausayin kanta da rayuwar da ta samu kanta a ciki.
  Bata san karfe nawa ba, bata san adadin dadewar da tayi a kwance ba tana kuka, ta nemi bacci ta rasa amma kuma idon ta kamar zai cire tsabar zafin da yake mata, haske ne ya gauraye dakin, a daidai lokacin ya turo kofar ya shigo. Tsayawa yayi yana kallon ta kwance a kan gadon sa, itama shi take kallo ya sauya kayan jikin sa zuwa gajeren wandon 3quater, da wata rigar daban da ta dazun, tashi tayi zaune ta hau kokarin sakkowa daga gadon, ya rigata ya hawo ya dora mata karfin sa gaba daya, ya danne ta ya hanata motsi, kafarta da ya kama mata ta dinga kokarin nuna masa tana kukan amma ko gezau be ba, kamar ma baya cikin hankalin sa. Kayan jikinta ya hau kokarin raba ta dasu, yana fincike su da karfin gaske! Bata da karfin da zata hana shi, sai dai kuma tana tsoron abinda zai je ya dawo, tana tsoron kar yayi kokarin take dokar Allah, dan taga alamun so yake da gaske sai ya raba da  martabar ta,wanda ko da babu period ba zata taba bari ya kusance ta a yanayin da yake ba, bata san matsayar ta ba, taba san wanne irin aure yayi da ita ba.
Gadan-gadan taga yana neman wuce gona da iri, bata san sanda ta samu hannun sa ta go gantsara masa cizo ba, hakan ya saka shi sakin ta da sauri gami da sakin gara, da sauri sauri ta tashi ta fice daga dakin, ta fad’a dayan dakin ta sakawa kofar key, sannan ta zame a wajen ta fashe da kuka. Wannan wacce iriyar masifa ce?
Tsawon daren bata runtsa ba, ya dade yana buga kofar ta kamar zai balla saboda bacin rai, ya gaji dan kansa ya tafi amma ta san dole haduwar su ba zatayi kyau ba, zatayi iyakar kokarin ta wajen ganin ta gujewa haduwa dashi din ko da zata mutu tayi mushe a dakin.
Da k’yar ta tashi lokacin da hasken rana ya hudo dakin sosai,ta shiga toilet ta gyara jikinta ta fito, ta chanja kayan jikinta ta hau gado ta kwanta tana fatan ta samu ta runtsa ko yaya ne.
Cikin baccin taji kamar ana taba kofa, ta tashi zumbur tana kallon kofar a tsorace. Sake bugawa akayi sai dai bugun na hankali ne,

“Waye?” Tace cikin muryar ta da ta dashe saboda kuka

“Nadeeya ce.”

Sakkowa tayi ta bud’e kofar tana kallon bayan ta ko tare suke, dan kallon ta tayi ganin yadda ta fige kamar wadda tayi rashin lafiya me tsawo,

“Ina kwana?” Ta gaishe ta ganin yadda take kallon ta.

“Lafiya lou, breakfast ne Mama tace a kawo muku, yarinyar tayi ta sallama shiru shine Mama tace nazo na gani.”

“Wallahi bacci ne ya dauke ni.”

“Ba damuwa, ki koma ki kwanta ai akwai gajiya,ga breakfast din nan a kitchen.”

“Mun gode.” Tace ta juya ita kuma ta sauka k’asa tana ayyana ramar da Asma’un tayi a dare daya kachal.

Kasa komawa baccin tayi kuma ta dinga juyi tana jin duk motsin sa tsakanin daki da falon saman, baya minti biyar sai ya amsa waya wanda yawancin mata ne sai tsirarin abokan sa. Bata dai jiyo me yake cewa amma tana jin sautin muryar sa, tayi tunanin zai zo ya buga mata sai kuma taji shiru, daga baya ma sai taji fitar motar sa daga gidan. Da sauri ta sauko, ta bud’e kofar ta sauka k’asa zuwa kitchen din da ta nemo shi da sauri sauri, ta dauraye plate ta zuba abincin da sauri ta sake hayewa saman ta saka key cike da tsoron kar ya dawo. Har ta gama ci bata ji ya dawo ba, ta tabbatar ya yi nisa ko kuma yana gidan Hajiya Maman, wanda tayi tunanin yi dan dazu bata iya wankan ba tana tunanin zai iya balla kofar ya shigo, a gurguje tayi wankan ta shirya ta dan gyara dakin sannan ta fito wajen da ta bar kayan sa na jiya, babu ko daya duk an kwashe sai ta koma ta rufe dakin ta kwanta ta fad’a kogin tunanin da ya zame mata aboki a yanzu.
Karar bud’e gate din gidan taji, ta leka ta window ta hango su Hidaya da Abbati da Rauda sai yaran gidan da jikoki na shigowa bayan me gadin ya bud’e musu, da sauri ta tashi farin ciki na mamaye ta, ta bud’e kofar ta sauka k’asa a dai-dai lokacin sun karaso balcony din, ta bud’e musu gami da rungume Rauda da take a gaba, dariya suka saka dukka Abbati na tsokanar su, suka shiga ciki suka zauna. Zuwan su ya saka ta manta tashin hankalin da take ciki, ta sake sosai suka dinga hira suna bata labari tana jin su, ta kwaso musu kayan abincin dazun suka cinye tas, sannan sukayi mata wanke wanke da dan gyaran gidan. Bayan nan sai ga yan biki daga gidan Hajiya Mama na ta shigowa ganin gidan amarya, hakan ya sakata sake shagala da abinda yake gabanta dan ko tuno shi batayi, sai yamma likis sannan suka tafi, su Ya Hadiza zasu zo gobe su kuma su kawo gara dangin su alkaki da su dublan, banda garar abincin saboda Hajiya Mama tace wa Abba ba sai anyi komai ba, duk daya ne shiyasa tun kafin bikin ma an dankare komai na abinci a gidan babu ce kawai babu.
Bayan tafiyar su sai gidan ya koma kamar yadda yake kafin su zo, saurin kau da komai take na falon ta koma daki chan sama kar yazo ya tarar da ita sai ga aiken Hajiya Mama tana kiran ta, wasu yan mata ne su biyu aka aiko, su tafi da ita, sama ta koma ta chanja kaya ta fesa turare sannan ta sakko suka tafi, bayan ta cire key din da ke jikin kofar ta rik’e a hannun ta.
Gidan na nan kamar ba’a gama bikin ba, dankare da mutane duk sai kunya ta kamata ta dinga sunnewa tana gaishe su har suka dangana da falon Hajiya Maman in da suke dukkan su a zaune, shi ta fara cin karo dashi yana kallon kofa, ya mike kafafun sa a tsakiyar falon suna hira da Maman yana ta dariya tamkar ba shi ba, tsoro taji ganin irin kallon da yayi mata, ta sauke kanta k’asa ta karasa da k’yar tana harharde kafafu kamar zata fadi. Sai da ta zauna sannan ta gaida Maman ta amsa a sake tana nuna mata gefenta.

“Dawo nan Asma’u.”

Da jan jiki ta matsa ba dan ta so ba, suka sa Maman a tsakiya shi da ita, ta shiga yi musu nasiha cikin sigar lallashi, wanda gaba daya a kaikaice da Asma’un take, duk nasihar akan yadda zata kula da adam din ne, da dukkan al’amuran sa, tana jin ta har ta gama sannan tace ta taso su je daki akwai sirrin da zasuyi, su Nadeeya suka fashe da dariya suna tsokanar Maman ta ja hannun Asma’un suka shiga ciki,suna shiga ta kalle ta tace

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button