KALLABI 58
BABI NA HAMSIN DA TAKWAS
Kurawa juna ido suka yi, kafin Lamido ya janye yana me shafa kan shi, abu daya zuwa biyu suka tsirga mishi, na farko bakin cikin yadda Ammyn tayi ta kuka akan Mutumin gaban shi, na biyu kuma wani mahaukacin soyayyar mutumin da yake huda duk wani sassa na cikin jikin shi, cikin wani ɗan uban sauri zuciyar shi take bugawa kamar zata dirko daga kirjin shi, Tausayin kan shi da kuma yadda yake kallon mahaifin nashi, yasa shi takawa gaban shi tare da rike hannun Baffa’m ya kai fuskar shi.
“Me yasa?” Ya tambaye shi hawaye na sauka daga idanun shi.
“Me yasa ranar ka ki amsar uzurin ta? Me yasa ka juya bayan ka bayan kasan dud duniya bata da wanda ta yarda da shi sama da kai? Meye ya faru wancan lokacin! Ina son sanin me ya faru! Domin idan na d’aga takobina sai na karar da duk wani makiyin Ammyna”
“Yaki dan zamba ne, idan har kanq son sanin me ya faru wannan ranar sai ka shirya sai ka shirya sai ka ajiye zafin ran nan sai ka shiga cikin gidan sarautar sai ka binciko me ya faru da wannan zan iya ce maka Allah ya baka sa’a, na hakura da kome ne domin ita na ki amsar ku ne domin rayuwar ku da a can aka haife ku baka isa ka rayu cikin salama da aminci ba, a yadda naso ganin ka haka na ganka, amma bana son ka kuma tambaya na me ya faru, amsar ka yana can a can zaka same shi”
Kakarin amai suka ji Anum tana yi, kallon kofar yayi sannan ya mai da hankalin shi wurin mahaifin shi da ya mike shida galadima, suka shiga cikin dakin.
Kokarin amai take amma ta kasa, sai mika take tana rike cikin ta.
“Galadima babu wani abun da za a mata ne?”
Kallon kofar yayi sannan ya ce mishi.
“Bana jin ina da maganin da zan iya bata, duba bayan ta an dake ta da wani irin guba ne shi yake sakata haka.”
Jikin Baffa’m yana rawa ya fito waje ya same shi zaune yana kallon kasa, yayinda yake zana kasa da karan dawa, zana da’iran Masarautar yayi sannan yayi ta fitar da wasu irin kofofin da ya fahimci suna cikin masarautan, tsayawa Baffa’m yayi akan shi.
“Gidado ne ya baka labarin yadda masarautan yake?” D’ago kai yayi sannan ya mai da kasa, yana kara cire wasu kofofin da suke jikin masarautan.
Wannan hali na Lamido da ban mamaki yake dafa kafadar shi Baffa’m yayi sannan ya bude baki zai kuma tambayar shi, taran numfashin sa yayi yana faɗin.
“Wata mata ce ta dauki wancan mahaukaciyar na shiga na daukota”
Daga haka ya tsuke bakin shi, yana cigaba da zana kome.
“Yahanasu Bingel ce ta mata wannan aikin? Subhanallahi toh ya zamu yi da ita guba ne a jikin ta fa?”
Nan ma shiru yayi yana kokarin fitar da wani abu ya ce.
“Idan akwai danyen madara a bata da garin sabara”
Ya cigaba da aikin shi, fita yayi ya dauko kayan shi a jikin dokin shi yq shiga rubutu babu ji babu gani, zuwa yanzun Baffa’m ya fara gano halin Lamido Hassan, tab ya fada a ran shi yana kara jin kaunar shi. Akan uwar shi ya tsawaita magana, akan kowa kuwa maganar takaitaccen ne.
Fita Sarkin gida yayi ya nimo danyen madara ya kawo aka hada aka bata,.da tayi ta sheka amai sai da tayi wani irin haske.
Fitowa Galadima yayi sannan ya zauna kusa da Lamido.
“Lamido tun kafin kazo dan uwanka gidado ya sanar mana, sai dai bamu tsammaci ganin haka ba. Akwai abubuwa dayawa wanda nake son mu yi magana a kai, tashi muje ga daki can”
Mikewa yayi ya bi bayan galadima, har cikin dakin, sannan ya amshi kayan shi ya ajiye mishi a saman wani gadon kara, zama suka yi sannan ya kalli Galadima.
“Yanzu ka huta daga gobe zamu fara aikin da zai zame mana maudu’in nasara”
Gyada mishi kai yayi, ya cigaba da abinda yake. Abin mamaki kallon shi yake cikin wani irin yanayi, mulkin da yakw kewaye da shi, kasaita da miskilanci, nutsuwa da mai da hankali akan abinda yake.
“Baffa akwai wani abu ne.?”
“Allah ya baka nasara mai martaba! Babu wani abu umarnin ka nake jira na fita” lumshe idanun shi yayi na wasu dakikai, kafin ya ware su akan kofar dakin.
“Allah ya baka nasara a huta lafiya” ya fito yana kakkabe rigar shi.
Haduwa suka yi su uku suna kallon kofar dakin shi.
Kallon kofar Baffa’m yayi a karo na babu adadi ya ce.
“Daga ni har uwa shi babu wanda ya daurawa kan shi mulki da alamu dai mune muka.damu da mulkin shi kuma mulkin ce ta dame shi.”
Hango shi suka yi ya goya hannu a baya yana kai gwauro ya mai mari, fitowa yayi sannan ya ce.
“A cikin masarautan yan majalisar sarki nawa ne? Ina son sunayen su kafin faduwar rana, sannan ina son sanin halayyar su domin cimma abinda ya kawo ni”
“An gama ranka shi dade!”
Inji Sarkin gida, a take suka dauko tawada da alkalami domin Baffa’m baya rabuwa da su. Kafin sallah azahar an gama rubuta mishi kome, sannan suka mika mishi bayan ya ja su sallah, fita yayi wajen gari ya nimo abinda zasu ci, a hanyar shi ta tafiya yaji ana bada labarin abinda ya faru a masarautan Gobir jiya.
Bai wani ji ko dar ba, asalima kamewa yayi ya nufi farautar shi bayan ya gama ya dawo, da kan shi ta fede barewar ya gasa musu, sannan ya koma gefe yana kallon waje, shigowar Sarkin gida amatukar rikice yana yarfe zufa.
“An saka lada domin kamo wanda ya balla kofar birnin” kallon shi Baffa’m yayi ya ga ya kauda kan shi.
Cikin sand’a ta fito zata fice, Baffa’m ya ce mata.
“Ya jikin naki?”
“Da sauki” ta fada muryan ta na rawa.
“Anum karki fita domin an saka a kamo ki a mace ko a raye?”
“Wayyo Allah na, toh meye nayi kuma?” Ya tambaya tana jin Kwaila na cika mata Idanu.
Share ta suka yi kowa ya kama gaban shi.
Bayan sallah Isha suna zaune ta dama musu fura da Sarkin Gida ya sayo a rugar su.
A hankali Galadima yake mika mishi wasu bayanai.
“Ina ga kamar ka fara ta kan Chiroma!”
“Ka gaya min labarin abinda ya faru ta nan zan iya kamo bakin zaren.”
Mikewa Baffa’m yayi domin zasu fama mishi ciwon da yake ran shi ne, a hankali galadima ya shiga bashi labarin abinda ya faru. Har zuwa inda ake zargin Aaminatu da cikin su.
“Mutumin da ya aikata haka a ranar da aka shirya kashe shi ta gudu, sannan Bello yaki amsa mata ne Sabida yana amsa mata zasu iya kashe dayan su,.matukar ya amince cikin na shi ne. Wallahi bai ki Aminatu dan abinda aka fada ba,.sai dai matukar tana raye a cikin masarautan ba zai iya kare ya ba”
Anum da bata da kwarin zuciya sai kuka take tana kallon lamido da ya bata tausayi kamar me, amma fir babu alamar fushi bacin rai ko damuwa akan fuskar shi mai hatta idanun shi basu nuna tashin hankalin shi ba, kallon shi take da dukkan zuciyar ta, tana jin yana mata wani irin bugawa a duk lokacin da ta kalli fuskar shi, wani irin abu yana yawo akan ta, Tausayin shi da kuma na iyayen shi suna kara samun daraja da matsuguni a zuciyar ta.
D’ago kai yayi, idanun su suka sarkafe da juna, tsuke fuska yayi alamar bai son wannan kallon. Sunkuyar da kai tayi kasa, sannan ta mike tsaki yaja.
Tun da ta shiga dakin ta kasa barci, tana leken shi. Sun jima suna hira, da Galadima kafin suka yi sallama ya wuce dakin shi. Fitowa yayi ya ganta zaune tana.kallon kofar shi tayi nisa cikin tunani, alola yayi ya barta a wurin. Wa shi gari suka tashi da wuri shi da galadima, suka nufi kasar sokkoto, bayan gari ya waye ta fito tana kallon kofar dakin shi. Cikin sand’a ta leka kofar.
“Kina niman shi ne?”
Da sauri ta juya tana kallon Sarkin gida.
“Baba sarki kawai ina mamakin taurin zuciyar shine jiya kaga dai yadda Baffa’m ya mike yana jin babu dad’i amma shi ko a jikin shi ”
“Waye ya gaya miki bai ji ciwon abinda aka gaya mishi ba?”
“Ina fa, kawai ni zan baka labarin abinda na gani. Bai da imani zuciyar shi bai tausayi, zuciyar shi tana buɗe ne domin kai hari ko kare kai akan Idanuna yayi ta sare mutane yana karya su, dube hannuna? Karya ni yayi shi yasa ma.kasa barci ina mamakin da kuma hasashen mutanen da suka yiwa Ammyn mu rashin mutunci, wallahi kareraya musu katarya zai yi!”
Baffa’m da yake daki fitowa yayi yan kallon ta kafin ya ce mata.
“Me ya faru a ina kuka hadu?”
“Baffa’m ban san a inda muka hadu ba, sai dai na farka naga ya kai ni tantin shi, daga nan kuma wasu suka kawo min hari ya kare ni, sai lokacin da Gwaggo Bingel ta saka aka kama ni jiya aka kai ni cikin masarautan ya shiga ya dauko ni bayan ya kar-karya musu hannaye da kafa, Akan Idanuna ya rike hannun arnen daji Baffa’m sai da suka gudu dakan su.”
Shiru suka yi itama kamar wacce aka matse bakin ta take ta zuba.
“Kenan yanzu haka an san fuskar Lamido?”
“A’a Baffa’m ai yaki sakewa suga fuska shi, na rantse duk a rufe yayi ta yakin nan kawai Baffa’m karka ce mishi ni na gaya maka wallahi karya min kafa zai yi nan gaba.”
Cikin zolaya sarkin gida ya ce mata.
“Ai tunda kika bada labarin nan kamar a kunnen shi, domin ko bamu gaya mishi ba dole zai sani”
“Baba sarki taya zai sani bayan ba a gaya mishi ba? Ni dai zan tafi!”
“Toh ai zai biyo ki har gidan ku” da gaske ta razana kawai ta fashe da kuka tana faɗin.
“Don Allah karka gaya mishi wallahi ban san me yasa na gaya muku”
“Jeki Anum tunda kina tsoron shi”
Fita tayi kamar munafika tana ajiyar zuciya, da tasan za ayi haka wallahi da bata tada fada ba.
**
Har gari yawaye ana jin kara da saurin algaitu, abinda ya saka dayawan mazauna birnin tsorata kenan, suka ki fitowa daga gidajen su domin ba a tab’a jin haka ba, a baya bayan nan amma wani tsoho ta tabbatar kimanin shekaru dari hudu da suka gabata kafin shigowar musulunci anyi haka akan sarkin da aka yi gardama akan shi, har aka kori ahalin shi. Lokacin da Sarkin ya dawo masarautar haka ce ta faru daga nan aka fara samun matsala da Sarkin da yake mulki, sannan ya kara da tarihi zai mai-maita kan shi, fatar su daya shine kar a zubda jini akan sabon Sarki domin haka zai iya sakawa mulkin ya zama ta jinsi biyu ne domin akwai masu bukatar haka.
Shiru kowa yayi kafin suka ce mishi.
“Idan har sabon Sarki ya hau ba azubda jini ba haka yana nufin an samu adalci kenan”
“Eh haka ne amma dole a fara amfani da niman agaji domin kare shigar su cikin mulkin”
—
“Wayyo Allah!” Ya farka yana ido tare da rike kunnen shi da yake mishi kamar an raba shi da dodon kunnen shi.
“Innah! Wallahi ba zan tab’a kyale shi ba sai na dauko Anum na aure ta”
“Aikin banza kayi min shiru sa’an ka idan ma baka girme mishi ba, yazo ya mangare ka, shine ka fadi kamar wanda aka sare kan shi wawa Lusari da ana cewa kai Lusari ne ban yarda ba, sai yanzun sakarai tunda ta hudu da wannan Tsinannen da ya sani yin dunguren masa sau biyu, ka sani babu kai babu ita domin kowani lokaci zata iya sanadin da zamu bar cikin masarautan nan wawa kawai”
“Taya? Idan Anum ce zan saka Haima ta dauko min ita nan da jibi kawai kwantar da hankalinki”
Yanzun ta kara tabbatar da cewa kande ta haifa sakarai shashasha barekata Lusari mara amfani kullum dakikiyar ƙwaƙwalwar shi bata ja cikin takaici ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana ji kamar ta kefe dan banza da kari.
“Allah wadaran naka ya lalace….
You Bingel me kike nufi Baby Barkindon ne ake mishi wannan cin zarafin?
Yau yan team Barkindo hankalin su zai tashi.
Team Lamido
Nasan sarai fatar nasara zasu mishi.
Team Anum kuma fa?
Ina team Haima?
Ina Team Dijah da Gidado…
#Mai_Dambu..
<p>The post KALLABI 58 first appeared on 2gNovels.com.ng.</p>