NOVELSUncategorized

NAJEEB 30

Ibtisam bayan ta tashi dialing din number din kabir tayi wanda yake ta ringing ba’a d’auka ba 

Kabir kam tunda ya kira batai picking ba ya ajiye wayar ya shiga toilet domin yayi wanka, koda ya fito shima ganin misscall din ibtisam yayi da sauri ya kirata ringing d’aya ta d’auka tare da sawa a kunnenta


Kuka ta saki tare da fad’in mai yasa ka kashe wayarka? Mai yasa kayi nesa dani? Kasan irin halinda na shiga kuwa Mai…..  Kuka yaci karfinta Sosai wanda hakan yasa ta kasa k’arasa abunda tayi niyan fad’a 

Kabir kiran sunanta yayi da ibti 

Cikin kuka tace uhm 

Yace plz ki daina kuka Ina son ki bani dama inyi miki bayanin abunda ya faru 
Pls ku rika mana click koda say daya ne Arana Akan ads, shike bamu Karfin gwuiwaDan shuru tayi domin tana son ta saurareshi 

Yace ibti ranan da nazo gidanku ranan daurin aurenmu bayan na dawo naji abunda ya faru, Naje hospital anyi min test inda daka nan nazo gidanku wajan Abba na nuna mishi k’arya ne sharri akamun yace inje zai nemeni, a hanyata ta komawa nayi accident wanda har saida aka fitar dani waje, ina sauka Kena Fara nema 

Ibtisam kuka take tana fad’in dama jikina ya bani akwai wani abu daya faru dakai, wlh jikina ya bani, Ina fatan kana lafiya yanzu 

Yace ibti lafiya? Sai dai na musulunci….  Canza maganan yayi da fad’in ina asibiti a America naga wata kaman ke…. 

Tace America a wani hspt? 

Nan ya fad’a Mata, tace Wlh nice nice dama kaima nan aka kaika?? 

Kabir yace eh, Mai kikaje yi a can?? 

Tace KABIR an kaini wajan NAJEEB….  Sai kuma tayi shuru tare da saka kuka can taci gaba da fad’in KABIR Ina cikin wani hali dan Allah kazo ka d’aukeni mu gudu, wlh bazan iya zama da kowa ba inba kaiba dan Allah kazo mu gudu muje muyi aure na ro’keka 

Kabir shuru yayi wanda sai yanzu ya tabbatar daya rasa ibtisam domin tunda tace an kaita wajan NAJEEB, lallai ya rasata kenan, wani irin hawaye ne ya zubo mishi Mai zafi tare da fad’in ibtisam Ina son kiyi hakuri ki rungumi aurenki hannu bibbiyu domin yanzu ke matar wani ce 

Ina miki fatan Sa’a a rayuwa, sai dai Ina son ki sani zuciya ta Kece a ciki har abada, Indai na cireki a ciki toh daka ranan nabar duniya…. Yana fad’in haka ya kashe wayar domin yanda yake jin zafi cikin ranshi lallai yasan abune Mai wuya ya iya cire ibtisam a cikin ranshi, amma koh Waye ya mishi wannan Sharrin ya gama dashi 

Ibtisam kam jin ya kashe wayar yasa ta k’ara fashewa da kuka tare da fad’in Wlh KABIR Nima bazan Barka ba, lallai dole NAJEEB ya sakeni, bazan iya rayuwa ba tare dakai ba…. 

Zarah da tun d’azu ta shigo d’akin ta tsaya bakin kofa domin jin ibtisam na kiran sunan KABIR, shigowa tayi tare da kiran sunan ibtisam 

Ibtisam bata d’ago ba balle ta amsa mata kiran da tayi mata 

Zarah hakan bai dameta ba, ta Fara magana da fad’in ina son kiji tsoran Allah, karki manta ke matar aurece bai kamata ki dinga magana da kabir b…. 

Ibtisam ta taso cikin zafin rai tare da fad’in nayi magana dashi din, sai me? Wlh bazan daina magana dashi ba, sannan karki k’ara kirana inada aure domin da wannan auren gwara babu, Abu d’aya zakiyi shine kisa yayanki ya sakeni 

Zarah kallonta ta tsaya yi cikin mamaki, lokaci d’aya kuma tayi murmushi irin na takaici tare da fad’in ibtisam Nasan ranki a bace yake, musamman na rabaki da Wanda kike so, wanda bada gangan akai miki hakan ba, kowa ya soki da kabir amma Allah yasa bashi bane mijinki, duk da anyi mishi kazafi ne, so ina son ki amshi kaddara kiyi hakuri ki amshi abunda Allah ya baki d….. 

Ibtisam cikin kuka tace ai dole kice haka, tunda dan uwanki ne, dole ki dinga bin bayanshi, wlh Zarah koda zaki kwana kina wannan maganan naki, baji zanyi ba domin bazan taba son NAJEEB ba har abada, so d’aya ne, naba ma kabir dan haka kibar bata bakinki wajan Kare Dan uwanki da bai San hakkin Dan Adam ba 

Zarah ganin yanda ibtisam tayi zafi Sosai yasa tace Allah ya baki hakuri ibtisam ni bana goyan bayan NAJEEB hasali ma ke nake goyan baya, wlh bance kiso NAJEEB ba, haka bazan tursasaki ki soshi ba, but abunda na Sani Kema y’ar uwarshi ce kaman yanda n…. 

Ibtisam tace Allah ya kyauta, wlh ba dan uwana bane, kima daina had’ani dashi 

Zarah tace nidai ina baki shawara kiji tsoran Allah kina da aure, ki daina waya da kabir domin karki bata lahirarki Ina fad’a miki hakan ne badan Ina son NAJEEB bane dake ko d’aya sai dan kiji tsoran Allah ki kuma tuna kina da aure 

Ibtisam juya mata baya tayi taci gaba da kukanta, ba komai ke mata yawo a Kai ba sai irin yanda KABIR yake fad’a mata Idan ya rasata bai San wani hali zai shiga ba, da irin kalaman soyayya da yake fad’a mata, tuna ranan da yayi kissing d’inta yayi da sauri ta tashi Tana fad’in NAJEEB ka cuceni sai kuma ta fashe da wani sabon kuka mai sauti….. 

Zarah janyota tayi jikinta tana fad’in haba ibtisam, Ina iliminki yake? Ina saninki yake? Duk ina kika kaisu? So yana son ki kasa yarda da kaddaran da Allah ya baki cikin rayuwarki? Ibtisam ko kin manta kowa da irin tashi jarabawan? Mai yasa kika kasa yarda da wannan jarabawan? Ko kin San Allah yana jaraba bayinsa domin yaga imaninsu….. 

Ibtisam cikin kuka tace hakane Zarah, wlh Ina son kabir, baki ji yanda nake ji bane, inda Kece a matsayina da zaki fahimci irin halin dana shiga, wlh Zarah son kabir yamin yawa, bana son kabir bazan iya bashi girman da mace zata iya Bama miji ba, zarah miye amfanin zamana da NAJEEB? Bayan baya sona nima bana sonshi? Wlh na tabbata in naci gaba da zama dashi zanyi ta jefa kaina cikin halaka, domin bazan iya bashi girman da mata ya kamata taba miji ba, gaba d’aya ko ganin fuskan NAJEEB bana sonyi inna tuna da abunda yayi min sai inji kaman in kashe kaina dan ba’kin ciki,.

Zarah ki duba yanda mace ke ririta kanta domin takai mutuncinta gidan miji, danta samu daraja, ki duba yanda nake ta kame kaina, amma at the end ki duba yanda akai dis virging d’ina a wulakance, bama tare da saninshi ba, inda Nasan haka zan rasa budurcina da tuni na barar a titi da…. 

Baki Zarah ta toshe ma ibtisam tare da fad’in ya isa haka Idan rai ya baci bai kamata hankali ya gushe ba, ina so kiyi hakuri Kibi komai a hankali insha Allah zaki samu sauk’i 

Ibtisam tace sau’ki d’aya shine NAJEEB ya sakeni 

Zarah dai rarrashinta tai tayi tare da bata baki, akan ta daina waya da kabir har sai NAJEEB din ya saketa 

Ibtisam dai batace komai ba sai shurun da tayi tana sauke ajiyan zuciya 

Yau watan ibtisam biyu da dawowa daka America, ibtisam gaba d’aya komai nata ya canza kirjinta sun ciko sai ta k’ara haske Sosai, ga yawan ciwon kai, dacin abinci kaman hauka, yau ta fito daka lecture kallo d’aya zaka mata kasan sauri take, ibtisam sauri take domin taje taci abinci dan wani irin yunwa takeji, tafiya take tana fad’in dole insha maganin macijin ciki, Nasan shine yake sani irin wannan cin abincin kaman hauka 

Tana shiga daki ta iske Zarah nacin abinci zama tayi tare dasa hannu ta faraci 

Zarah tace wai ibtisam wannan wani irin ci kike kwanan nan haka?

Ibtisam tace uhm macijin ciki ke damuna, zansha magani shike sani wannan mugun cin Wlh, ga ciwon kai, saifa naci abinci ciwon kan yake lafawa, anjima kad’an kuma sai ciwon kai din ya tashi inna k’ara cin abinci saiya lafa haka yake min… 

Zarah tace toh anya kuwa? 

Ibtisam tace anya kuwa me?? 

Zarah tace gaskiya kije asibiti a dubaki, ban taba jin irin wannan Abun ba 

Ibtisam tace zani 

Zarah tace Allah ya kyauta 

Ibtisam tashi tayi tare da tube kayan jikinta tasa wata riga mara nauyi tasa sannan ta kwanta tare da lumshe ido, ba komai take tunani ba sai KABIR daya daina d’aukar wayarta tunda ta kira wata rana ya dauka yace tayi hakuri ta daina kiranshi tunda ita matar wani ce, yana fad’in haka ya kashe wayar tun daka ranan bai K’ara d’aukan wayarta ba, itama ganin haka saita daina kiranshi tare da burin suyi hutu ayi Mai yihuwa NAJEEB ya saketa,.

Tunda tazo NAJEEB bai kirata ba, balle yaji ya take ba, itama hakan bai dameta ba, dan tasan dama za’ayi hakan, Toh Mai ma zaice Mata inya kira din?? 

Ibtisam kasa bacci tayi sai juyi take tayi, ganin haka yasa ta tashi tare da d’aukan hijab tasa tace Zarah Bari inje waje insha iska Wlh wani iri nakeji gaba d’aya jikina babu dad’i, ni gashi ba ciwo ba, amma jikina wani iri 

Tashi Zarah tayi tare da fad’in muje tare musha iska din 

Fita sukayi inda suna nan zaune suna fira saiga Salees yazo ya zauna ta gefen ibtisam sunata fira ana dariya, Zarah tashi tayi tare da fad’in kai na manta inada lecture 5 wai assignment zamu bashi bari inje in dauko. 

Bayan Zarah ta tashi Salees yace Wai nikam ibtisam kodai kin Fara shafa Mai ne?? 

Tace maika gani?… 

Yace naga yanda kike wani walkiya, kinyi haske gashi kin k’ara kyau Sosai Kai ibtisam nifa gaskiya wannan guy din ya kwafsa min 

Dariya ibtisam tayi tana fad’in bleaching Rufamin asiri ina ni Ina bleaching…..

Yace Wlh Kinga yanda kike walkiya kuwa…… 

Tun daka nesa ya hangosu a zaune, fuskanshi ne ya canza 

Bayan driver ya faka wanda dai dai lokacin aka kira Salees a waya ya tashi tare da fad’in ina zuwa 

NAJEEB cikin zafin rai ya fito ibtisam kawai ganin mutum tayi a gabanta ya tsaya, fuska d’aure 

Gabanta taji ya fad’i Sosai gaba d’aya abunda ya mata ya fara dawo mata, hannunta ya kama tare dayin gaba da ita ya bud’e motar ya Jefata sannan shima ya shiga ciki yace driver ya tada motar suje 

Ibtisam ganin haka ta Fara k’okarin bud’e motar….. 

NAJEEB janyota yayi da karfi tare da ri’ke mata hannu 

Shidai driver tuk’i yake 

Koda suka fita daka cikin school din driver ya tambayi NAJEEB Ina zasu? 

NAJEEB yace ya kaisu best hotel dake ZARIA 

Driver ya amsa da OK 

Koda suka k’arasa NAJEEB yaba driver ATM d’inshi tare da fad’a mishi pin din yace yaje ya Kama musu d’aki Biyu a cire kud’in a ciki 

Ibtisam ganin driver din ya fita yasa ta kalli NAJEEB daya ri’ke mata hannu tace ka sakemin hannu 

Wani irin kallo ya watsa mata Kai Kama da ni sa’anki ne 

Ganin haka yasa ta Kame bakinta tayi shuru tare da k’okarin taja hannunta daka nashi, amma ta kasa 

Har driver din ya dawo, yace an Kama d’akin sir 

Najeeb bud’e kofar yayi tare da janyota suka fita, hannunta na ri’ke da nashi suka shiga ciki har d’akin inda ma’aikatan hotel din suka kaisu 

Suna shiga ya jefar da ita tare da rufe kofar 

Kallonta yayi idonshi wanda ya canza launi alaman bacin rai, yace keda uban wa kike magana a skul??  Kenan abunda kikeyi kenan koh? Shuru yayi yana kallonta alaman yana tunanin maima ya kamata yayi mata ne lokaci d’aya ya d’aura hannunshi akanshi tare da lumshe ido 

Ibtisam kam ganin haka yasa ta tashi a k’asa daya jefar da ita, tare da tsayawa a tsaye

Najeeb bud’e idonshi yayi wanda ya sauka akan na ibtisam din yace am asking you keda uban Waye kike zaune??? 

Shuru tayi amma gabanta faduwa yake saboda tsoro 

Ganin yana nufota yasa tayi saurin fad’in class mate d’ina ne…. 

Najeeb karasawa ya farayi inda take harya ganin haka yasa ta Fara matsawa baya, harta had’e da jikin bango inda ya k’araso inda take tare da janyo mata hijab lokaci d’aya ya cire mata hijab din, rigan jikinta irin Mai budaddan kirjin nanne nononta ana ganin Sun fito waje amma ba duka ba  

Idon NAJEEB ne ya sauka akan nononta wanda suke a tsaye kuma a ciki, domin Sun k’ara wani girma, ganin ya kura mata ido yasa ta kalli inda yake kallo da sauri tasa hannu ta janyo rigan tare da rufewa amma still ana ganin nonon 

Da yake NAJEEB Dan duniya ne saiya basar tare da fad’in your class mate? Kin manta da aurena a kanki??.. 

Ko kin d’auka ni Wawan namiji ne wanda ban San abunda nake ba? Am talking you tare da daka mata tsawa 

Ta tsorata da Tsawan daya daka mata, wanda harta furta Kalman kayi hakuri ba tare data sani ba 

Jin haka yasa ya k’ara mata ido yana kallon fuskanta da idonta ke rufe, gaba d’aya yaga yanda ta tsorata, domin yanda tayi da jikinta 

K’are ma fuskanta ido yayi inda idonshi ya sauka akan bakinta mai laushi domin yaune rana ta farko daya k’are ma ibtisam kallo 

Najeeb gaba d’aya ya kasa mata abunda yayi niya lokaci d’aya yaji ranshi ya fara sanyi, domin yayi niyan Idan yazo ya mata abunda sai tayi dana sanin kula wani namiji amma duk da hakan zai d’auki mataki 

Ibtisam a hankali ta bud’e idonta ta ganshi akan gadon d’akin daka shi sai boxer da singlet 

Da sauri ta kawar da idonta gefe, gabanta ya buga da karfi tare da tunanin mai zai Mata? Gaba d’aya abunda ya mata ya dawo mata lokaci d’aya kuma ta fara hawaye, domin tana tunanin abunda yayi mata rannan shine zai K’ara mata yau 

Ibtisam cikin kuka tace dan Allah ka barni in koma skul, kayi hakuri ka barni in wuce dan Allah…..

Yace will you keep quiet and stop that crying 

Ibtisam shuru tayi amma tana hawaye, ga kanta ya fara ciwo alaman tana jin yunwa, ganin tana jin ciwon kai din bazata iya zuciya ta daure ba yasa ta saki ihu tana kuka, lallai dole inje hspt wannan wani irin jaraba ne ya kamani….

Najeeb yace if I hear your voice again I will teach you a lesson nonsense 

Ibtisam shuru tayi, lokaci d’aya taji har jiri jiri take ji, da sauri ta nufi fridge din d’akin ta bud’e taga harda Hollandia aiko d’auka tayi ta kafe Kai ta Fara sha kaman mayya 

Idon najeeb na kanta yanda yaga Tana sha tsaki yaja tare da k’ara sanyin AC din d’akin ta remote, domin yana bukatar ya kwanta kafin yasan hukuncin da zai yanke mata 

Ibtisam bayan ta gama sha taji dan dama dama, lokaci d’aya kuma taji yunwar har yanzu nufa wajan gadon tayi inda ta dauki wata takarda akan side drower din, inda y’ar wayar telephone ke wajan inda zaka kira masu hotel din in kana bukatar Abu 

Duba takardan tayi taga irin abincin da suke dashi, sannan ta danna wayar ta Fara magana 

Najeeb harya Fara bacci yaji muryanta kaman tana waya wanda hakan yasa ya farka ile kam wayar takeyi, da sauri ya amshi wayar tare da sawa a kunne dai dai lokacin ana tambayarta room number din 

Najeeb fad’a mishi yayi tare da fad’in mai zaka mata?? 

Yace sir abinci za’a kawo mata 

Yace OK tare da ajiye wayar ya janyota tare da rungumota ta kwanta ta gabanshi

Tana k’okarin tashi yace ki nutsu kona zaneki 

Ibtisam jin haka yasa tace plz ka sakeni in tashi bana jin bacci 

Najeeb yace an so what, I don’t care kina ji ko bakya ji, I need silent, so don’t disturb me 

Ibtisam tace OK allow me to go 

Bai bata amsa ba sai hannunshi daya saka tare da toshe mata baki da karfi 

Ibtisam ta Fara shure shure Da k’afa alaman ya saketa, amma NAJEEB ya’ki gashi dakyar take nishi, NAJEEB har hawaye yaji yana taba mishi hannu amma ya’ki sakinta….. Bacci ne a idonshi Sosai,….  Jin nocking din da akeyi yasa ya saketa tare dayin tsaki ya tashi 

Kofar ya bud’e tare da amsan abincin, Kun San hotel in aka kawo maka abinci zaka bada kudi ganin ya tsaya yasa NAJEEB fad’in am coming 

Shiga yayi ya ajiye abincin tare da kallonta yanda take kuka yace kawo kud’in in bashi 

Wani irin kallo ta watsa mishi tare da fad’in ai bani nace ka d’auko niba, kaida ka dauko ni saika biya 

Najeeb kallonta yayi yanda take maganan cikin tsoro amma dole sai tayi rashin kunya.

Yace banda kud’i a wajena 

Ibtisam Banza dashi tayi tare da tashi ta dauki abincin ta faraci kaman wata mayya 

Yanda take cin abincin abun yaba NAJEEB mamaki cikin ranshi yace sai kace wacce bata taba cin abinci ba 

Najeeb d’aukan wayarshi yayi ya kira driver da shima yake d’ayan dakin da aka Kama, yace yazo d’akinshi.. 

Ba’a dad’e ba driver din ya k’araso, najeeb yace suje a cire kud’in abincin ta POS sannan yace ma driver din shima yaci abinci tare da fad’in inya gama ya ciro Mai kud’i domin yana bukatar kud’i a hannunsa kud’in Nigeria,

Driver ya amsa da OK sir tare dayin gaba shida wanda ya kawo abincin 

Najeeb wani irin kallo ya watsa ma ibtisam sannan ya koma ya kwanta 

Ita kam ibtisam ci take hankali kwance, abincin ya mata dad’i sai dai Naman ne data Fara ci taji kaman zatai amai dan haka ta barshi, zuciyarta taji Tana tashi Wanda yasa da gudu tayi toilet tana kwarara amai kaman hanjinta zai fita 

Najeeb jin kaman nishinta yasa ya tashi jin Tana toilet Tana amai yasa ya tashi ya nufi toilet din duk da baya son ibtisam ta dan bashi tausayi harda yi mata sannu tare da rukota yana buga mata baya kad’an k’adan 

Ita kam idonta duk ya firfito yayi ja Dan azaba 

Kamota yayi Bayan ta dauraye bakinta ya fito da ita tare da ajiyeta akan gadon d’akin yana fad’in ba dole kiyi amai ba, kinsha Hollandia and now kalli yanda kike cin abinci kaman wata witch 

Ibtisam kallonshi take tana mamaki yanzu ya nuna kaman ta bashi tausayi harda sannu, amma jiba kuma yanda yake mata fad’a kaman wata y’arshi 

Najeeb tsaki yaja tare da fad’in komai mutum ya samu yaci, may be Kinje kinci food poison 

Kwanciya yayi tare da fad’in I need to sleep so don’t disturb me plz 

Ibtisam Hararanshi tayi cikin ranta tace kaji dashi Wlh ka tashi kaban takarda na domin kabir na jirana mugu kawai……..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button