BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 61 to 70

Yana tura ƙofan yashiga yahange ta kwance saman gado sai sharan barci take yi, wajen gadon yaƙarisa yana kafe ta da idanuwan sa
Tana kwance ta ɗaura kanta saman pilow tare da matse shi sosai a tsakankanin hannayen ta, gyalen da ɗankwalin ta gaba ɗaya sun yi hanyan su, sai ta nannaɗe ƙafafuwan ta waje ɗaya tacure kamar wata me jin sanyi
Idanu kawai yazuba ma face ɗin ta yana kallon yanda tabuɗe baki tana sharan barci, be san sanda yasaki murmushi yana jin tsananin son ta a ransa
Ya ɓata lokaci sosai yana ƙare mata kallo ko ta ina, sai da yagaji don kansa kafin yanufi sip ɗin sa yazaro ƙananan kaya yasaka, sannan yanufi gaban mirror yayi shafe-shafen sa tare da gyara yalwataccen gashin kansa yafeshe jikin sa da turaren sa masu shegen ƙamshi sannan yafice.
Ƙamshin turaren sa shine yatashe ta, lokaci ɗaya tabuɗe idanunta batare da ta motsa ba, sai da tadaɗe ahaka tana ta shaƙar daddaɗan ƙamshin sa kafin tamiƙe zaune, ɗankwalin ta taɗauka taɗaura tasauka tanufi Toilet, bata fito ba sai da tayi wanka kafin tariƙo kayan ta a hannu tana ɗaure da towel tafito, ajiye kayan tayi tanufi gaban mirror tashafa Lotions sannan tanufi wajen Trolly ɗinta tazaɓo kayan da zata saka
Doguwar riga ne na atamfa iya ƙasan gwiwan ta, sai skert pencil me tsagi ta baya, kayan sun yi mata kyau da tasaka kasancewar atamfan ja ce da ratsin blue, ɗan kwalin kawai taɗaura tafito sabida yanda take jin yunwa sosai a cikin ta
Babu kowa parlour’n sai tanufi kichen kanta tsaye, dashi tasoma cin karo yana zaune a bakin ƙofa saman kujera, hannun sa riƙe da tea Cup yana latsa wayan sa
Shigowan ta yasa yaɗago kai yana kallon ta, wanda idanuwan su suka haɗe cikin na juna, sai tayi saurin cire nata idanun tana gaishe sa
“Ina kwana?”
Be ɗauke kansa akan ta ba sabida tayi masa kyau sosai duk da kuwa babu kwalliya a fuskar ta, kuma kasancewar tana jego sai skin ɗin ta yaƙara fresh duk da kuwa ta rame a fuska, amsa mata yayi a taƙaice
Sai taƙara ce masa “Ya jiki?”
Wannan karon sai da yaja lokaci kafin ya’amsa mata wanda har ita tayi tunanin ba zai amsa ɗin ba, kuma tana tsaye a wajen taƙi jirga wa, ji kawai tayi gaba ɗaya kamar an zare mata kuzarin ta sabida yanda take jin idanuwan sa akanta, wanda ta tabbatar kallon ta yake yi shiyasa takasa gaba takasa baya
Miƙe wa yayi yanufi cikin kichen ɗin ya’ajiye Cup ɗin hannun sa sannan yafice
Fitan sa yayi daidai da sauke numfashin da tayi, dafe ƙirjin ta tayi tana jin yanda yake luguden bugawa, ta jima a tsaye bata san me zata yi ba kafin kuma taja ƙafafun ta taƙarisa ciki cike da rashin jindaɗin yanda Khalil yasauya mata tun kafin haihuwar ta, ta rasa mene tayi masa yasauya lokaci ɗaya, ada abun baya damun ta amma a yanzu sosai take jin haushi da rashin yin mata magana da baya yi
Tura baki gaba tayi tasoma neman abinda zata yi breakfast, ruwan tea ta dafa sannan tasake a Cup ɗin da yasha, sai tasoya ƙwai guda uku, sai da tagama tahaɗa Tea ɗin sannan tazauna a inda yatashi tasoma karya wa, ba ta son tafita Parlour ta tarar dashi don haka tayi zaman ta nan
Sai da tagama sannan tafito, babu shi cikin parlour’n sai tanufi ɗakin sa wanda yazama nata a yanzu, tana tura ƙofan tahange sa bakin gado, dasauri tajuya takoma parlour tazauna
Kallo takunna tayi zaman ta anan tana ta saƙe-saƙe a ranta.
Khalil be fito ba sai da yaji kiran sallan azahar, da keey ɗin mota a hannun sa yafice agidan.
Itama tashi tayi tashiga ɗaki tagyara kwanciyar ta takwanta saman gado bayan ta ɗau wayan ta da tabari akan drower, kasancewar tana jego hakan yasa bata da tsarki, wayan ta tay ta dannawa har zuwa wani lokaci, gaba ɗaya ta gaji da zaman ta haka nan har Ummi ta kira sun yi waya, daga ƙarshe sai tajawo jakan makarantan ta tasoma duba handout ɗin ta, a ranta tana tunanin dole ne gobe takoma school tunda baza tay ta zama haka nan ba koda yaushe bata da abokin hira
Da wannan shawaran tatashi tasoma gyara gidan, duk da kuwa ko ina fesfes yake jin sa, amma haka tagyara ko ina tasaka turaren ƙamshi gidan yabaɗe da ƙamshi sosai, ganin Khalil be dawo gidan ba sai tasake sakin jikin ta tana ta harkokin gaban ta, a Parlour tabaje tana ta kallo gefe ɗaya kuma ga handouts ɗin ta ta baje su tayi karatun har ta gaji
Sai da yamma tayi sosai sannan tatashi tashiga kichen tagirka musu shinkafa da miyan jajjage sannan tayi musu zoɓo tahaɗa salat, takai dainning duk ta jera tanufi ɗaki tasake yin wanka tasauya kaya.
Sai dare Khalil yadawo, lokacin tana Parlour zaune yashigo, sannu da zuwa tayi mishi ya’amsa yawuce ɗakin ta, wanka yayi yasauya kayan sa yafito Parlour
Kasancewar da yunwa yadawo yana fito wa yakalli dainning, nan yaga coololi an jera su don haka can yanufa yazauna yazuba abincin yaci
Halwa tun fitowar sa tashige ɗaki, dama zaman jiran sa take yi taga dawowar sa sabida zuciyarta haka kawai tamatsa mata da rashin jindaɗin dawowar nasa, sauya kayan ta tayi zuwa na barci riga da wando sannan tahaye gado takwanta, babu jima wa barci yay gaba da ita
Khalil be dawo ɗakin ba sai da yagama kallon sa sannan yashigo yaɗau kayan barcin sa yasaka yafice yakoma ɗakin Saleema.
Washe gari da safe Halwa tana tashi tagyara gidan tayi musu breakfast sannan taci nata takoma ɗaki tashiga wanka, tana fito wa tashirya cikin riga da skert na atamfa ruwan madara sai ratsin brown da baƙi, ɗinkin yayi mata kyau sosai ya sake haska ta matuƙa, Hijab tasaka brown Colour wanda yatsaya mata dai-dai gwiwar ta, sai taɗau HangBag ɗin ta tafito
Lokacin Khalil ya fito daga ɗaki yana shirin shiga nata don saka kaya suka ci karo
Dasauri tamatsa masa tare da gaishe sa
Kallo yabi ta dashi kafin ya’amsa mata batare da ya tashi a hanyan da yatsare mata ba, mamaki yake yi ganin ta da shiri “to ina zata je?” Yatambayi kansa gaban sa na faɗuwa jin wani sashi na zuciyar sa ta kawo masa tunanin ƙila gida zata koma
Halwa kamar tasan me yake tunani tace “Uhmm dama zan je school ne”.
Be ce komi ba yamatsa mata tawuce shi kuma yashige ciki
Tana fita tahaɗu da drever, tayi masa maganar makaranta zai kai ta
zuwa yayi yaɗauko motan tahau suka fice cikin gidan.
Khalil dake tsaye bakin window yana kallon su, sai da suka fice sannan yasauke ajiyan zuciya yaƙarisa yasaka kayan sa yafito Parlour yay zaman sa, dayike ba wai ya gama samun sauƙi bane shiyasa bazai iya koma wa bakin aiki ba, har yanzu ciwon na damun sa don baya iya yin tuƙi, jiya da yafita har ya shiga mota ya zauna ya kunna yana shirin tuƙa wa yaga bazai iya ba, shine yakira drever suka fita tare.
*****
Drever na sauke Halwa tanufi department ɗin su, yau bata saka Niƙap ba don bata da sha’awar saka wa kamar ko yaushe
A hanyan ta taci karo da wata Course mate ɗin ta Nafeesa, suna mutunci sosai da ita don haka tayi saurin kiran ta
Hakan yasa Nafeesa tajuyo don taga me kiran nata, ganin Halwa sai tafaɗaɗa fara’an ta tace