KANWATA HAUSA NOVEL

KANWATA HAUSA NOVEL

Dad ne ya shigo fara na bayi tana alwala maman fara ta fito rike da karami towo ina kika samu yaro tai dariya jikanka ne jikana kuma ya kamo hannun yaron ya sunanka sunana Hamza anman karami ake cemin a kace takwara bane yai dariya kaima karami ake cema eh amman kai vabbane kai wannan yaro da wayo kake ummi ce ta fito tana kuka ina mominta dan ita vata cuka sabiba irin yarannan ne nasu nacun uwa ah ashe yaran da yawa ya kamota tako kara tsanyara kuka fara ta futo da sauri ta dauketa to yar rigima takwantar da kai a girjinta tana saukarda ajiyar xuciya dad ya xaro idi wanake gani kamar fara nice dad yakalli mum tai masa murmushi jeka masallaci kadawo sai kaji komai.

Koda ya dawo ta fada masa yadda sukai yace ikon Allah rabon tun alokacin baxamu gana bane tace dad mai yadawo dakunan naje can kunsaida sai hawaye kuskurena ne bakomai ba haba dad mai yajawo kuka kayi hakuri in mgnta ko xuwana ya bata maka rai ko kusa basu suka batanba sai tuna abinda dan uwana yamin.

Kanwata
Na F.A.Ya’u

Tun bayan mukai mgnar auranki kika bujire tun lokacin naji tsanarki haka kawai banasan ganinki na rasa mai yasa sai bayan da akai auren yaya yaxo duk wata harkata ya shiga tsimdim dafarko komai normal dan nama manta dake yayinda a hankula inna kaka tafara canja min ko naje gunta bata shiga sabgata gai suwata ma tadena amsawa na rasa mai nai mata ahankula komai nawa ta dena karba saima ta hada kayanta ta koma gidan yaya.

Ban fiskanci komaiba saida aka gama cuta ta domin ina gida akaxo wai ansaida gidan nace kamar ya aka ban takarda naga sa hannun yaya naje nasameshi sai na taddashi a kujerata a gun aiki wai ai daman yai alkawari kuma alkawarinsa ya cika domin tun muna yara anfi sona agida komai ni shi kuma abin na masa ciwo angirma na fishi arxiki gashi har yanxu ummanmu tafison yata kan nasa shiyasa yaci burin sai ya rabani da komai dan inji bakin cikin da yakeji aduk sanda aka fifitani shiyasa yafara da rabani da diyata uwata da dukiyata aranar nai kuka nai kuka kamar mai haka yasa akamun korar kare yace jibima innaxo ansaida kamfanin itako inna kaka badamar ganinta dan yace kar abarni na shigar masa gida tsanata yasa aka sanya a xuciyarta ki yafemin komai ba lefina vane lefin asirine duda kuwa asirima na tadda hali tasa kuka dad nice xan nemi gafararka ni nakasa maka biyayya watakil danayi yaya salim ya aureni da duk hakan bata faruba.
Sai tara tabar gidan tabar musu karami dan yan biyu basa yadda da kowa sai ita sai vabansu in yan wulakancin suka motsa ko shi basa kulashi suna manne daita.

Kanwata
NaF.A.Ya’u

Washe gari fara ta aiko da mota dan su mum dinta suxo suga gidanta aiko tunda aka shawo lokon suke gwala la idanu dan kam duk lokon babu karamin gida basuga gidan da yai dai dai da farhanba ga mamakinsu gidan da yafi kowanne aka nufa dasu basu kara tsindima cikin mamakiba saida sukaga fara tsaye tana jiransu.

Dadi kasa shuru yai saida ya tambaya anya kuwa nanne fara tai dariya nanne mana das shima yajira baku isoba yace bara yaje ya dauko yara dan kugansu acan babban gida.

Basu dade da xamaba ya iso aikon farhanne saidai duk ya sauya kana kallonsa xakasan kudi sun xauna yakara kyau yai yar giba dai dai shi nan yagaidasu cike da ladabi dad yai tabashi hakuri yace aishi bai taba rike shiba.

Koda suka dawo gida cike da alkairi iri iri dad yace lallai ikon Allah sai kallo mum tace aini naga haka mutum ba’a bakin komai yakeba kedai bari naga ishara yanxu mukuma akiramu mai tace ai nikam batun yauba nadaukarma kaina alkawarin dena cin xarafin talaka yai dariya to muma cin ina kudin aimuma daya muke arxiki daga Allah kigadai yaronnan lokacin da nake cin mutuncinsa waxai ce xaiyi koda keke ne nasa segashi koda ace inada kudin vaxan kama kafa dashiba kinajifa har gwala gwalai yake da shagonsu a saudia da Dubai haka naji sudai haka sukai da danasaninsu kala kala.

Duk wani nauyi na su dad farhan keyi dan yanxu ya saimusu gida anan rijiyar xaki daman wanda suke ciki na dorayi na haya ne abubuwa sun fara komawa dai dai dan kasuwancinsa ma farhan ya sanya masa hannu ya kara masa jari ya fara far fadowa abu daya ya dameshi shine inna kanasu.

Kanwata
Na F.A.Ya’u

Shawarar da Fara ta kawo suka bi duk juma’a ana dafa abinci abaima almajirai sauka kuwa asati sai ai sau uku ko hudu addu’a ba kama hannun yaro kan Allah ya karya abinda akaima inna na farraku ita da dad.

Akace wanda ya kama addu'a baya danasani domin kuwa inna kaka yau ta tubure fada ita sai ankaita gurin danta yaya yanaji yana gani yadauketa har gidan kanin nasa dan yasan inda yake aiko anan ya sauketa ko gidan bai shigaba yajuya dan sunyi da matarsa akan yana kaita yaxo su koma gurin boka dan wani abin ita ke dorashi akai duda shima da bakar xuciyarsa.

Akan hanyarsu ta xuwa sikai hatsari nan take matar ta mace asibiti aka kira wayar hamxa bai bata lokaciba ya xo ganin halin da yayan nasa ke ciki ne ya daga masa hankali shi yai masa komai kafin yaje ya tawo da inna kaka da mum saida yaga komai normal yadauki gawar umma amarya sai gidan acan aka hadata aka kaita inka dauke yayanta ba wanda ya damu dan murnama suke sun rabu da masifa musanman ma sauran kishiyoyinta abinda kawai ya damesu kawai lpyar mai gidan.

Inna kaka na gefe yana kuka ya ruko hannunta inna ki taimaka kisa kanina ya yafemin itama tana kuka mune sanadi da tun farko muka dasa maka tsanar sa ta nuna banbanci mu muka kasa danne xuciyarmu.

Nikam tun farko ban rikeka ba lefina nadauka nagode kanina farama haka ya nemi gafarar ta tace ita tuni ta yafe masa.

Jinyarsa gaba daya inna kaka ce tai kulawa ta musanman take bashi duda tasan abune daxai gogeba tun farko sunyi kuskure na nuna ban vanci tsakanin yayan nasu.

Kanwata
Na F.A.Ya’u

Jiki kam yai sauki ansallami shi ya koma gida kullum inya xauna bashi da aiki sai rokar kanin nasa afuwa.

Kinsan me sai ka fada kasu wanci na na Malay nakesan xuwa sabida wasu abu buwa da suka taso kuma akalla xanyi watanni yakike gani tai dariya sai innemo maka yar yarinya ka aura katafi da abarka kwasha amarci yai dariya kinfiye xaulaya da gaske fa nake to ya xamuyi da yaranmu daman hutu suke suna babban gida karami yana gunsu dad se mu tafi da yan biyu sune daman dai matsala tai dariya to Allah ya nuna mn.

Duk wani shirinsu sun kammala angama komai fara taje duk tai sallama da yan uwa abinda ya vata  mamaki shine dataje babban gida kowa sai nan nan ake da ita kamar ba itaba ce wadda suka dauki karan tsana suka dorama va abinda vata saniba shine duk abinda farhan ke musu yakance injita.

Baban yara na’am inajinki yako batun masallacinnan eh an gama inaso kafin mu tafi afara sallah yawwa na gode ranar da xa’a su tafi ta tace masa nasadaukar da masallacin ga kanwarmu yai dariya Allah yasa da alkairi danshi baisan iya abinda yai sadaukarwa ga kanwarsa mai sansa ba duda kasantuwar yayansu yara ne anman sun dorasu kan insunyi sallah ko kiran sallah suka jiyo su musu addu’a suyima umma fadya abin har ya xame musu jiki dai dai da yan biyu sun iya.

Harfilin jirgi aka raka su anata daga musu hannu tana rike da ummi yayinda farhan han ke rike da abi saida sukaga dagawar jirgin sannan suka watse.

Nima anan nake cewa Allah yakaisu lpy yabar so da kauna dan banda kudin binsu balle inkawo muku rayuwarsu a Malaysia.

Alhamdulillah Allah abin godiya da ya bani ikon kammala wannan littafi fatana ya amfanar.

Wani abu da nake san agane.

Banyi dan cin mutunciba ko bata sunan wani sai dan nishadan tarwa fadakarwa.

Wani abu game da labarin da nake san a fuskanta.

Mutum baya xama mutum har sai ya girmama mutum dan uwansa duk yadda kakejin kafi wannan mutumin bakasan irin baiwarsa ba bakasan yadda xata kaya maka ba akarshen rayuwarka.

Biyayya ga iyaye dolene komai sukai maka indai harkana san cigaban farin cikinka kamar yadda fara bata samu farin ciki mai dorewaba saida iyayanta suka yafe mata.

Gareku iyaye nuna ban banci tsakanin yayanku kan jawo musu kin juna da tabarbarewar xumunci ko kafisan daya daure kabar abin aranka treat them equal.

Manta alkairi ga wanda akaima bai xamto halin dana gariba kamar yadda fara ta kasa mantawa da karamci mutuncin fadya ga rayuwarta.

Godiya

Godiya ga duk wani ko wata da yabada lokacinsa wajen karanta wannan littafi fatan duk wani kuskure da’aka gani xa’amin afuwa dan adam axijine.

Taku har’abada
Fatima Aminu Ya’u
F.A.Ya’u
09028287218

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8

Leave a Reply

Back to top button