Labarai

Kare Ya ciji Al’aurar Uban Gidan Sa Ya Dauka Nama Ne A Jahar Calabar

Wani magidanci mai shekaru 60 a Calabar, jihar Cross Rivers, Ani Ikoneto, ya mutu bayan da karensa ya cije masa al’aurarsa.

A cewar makwabtan da suka zanta da Vanguard, Ikoneto wanda ke zaune a lamba 12, Titin Jebbs a Calabar ta Kudu, ya tafi shaye-shaye a jajibirin Kirsimeti ya dawo gida buguwa.

“Lokacin da ya dawo, mun kwanta amma wasu suna waje. Dakinsa ya shiga ya kwana ba tare da ya rufe kofa ba, shaye-shaye ya yi yawa ya fita da kanshi.

Karen nasa da ke waje ya shiga cikin dakin sai karen ya ciji al’aurarsa a tunanin sa nama ne ko kuma wani bangare ne na hatsaniya,” inji Itoro makwabcinsa.

A cewarsa, mutumin ya buga ihu ne dalilin da ya sa makwabta suka garzaya zuwa gidansa suka gano abin da ya faru.

“Lokacin da muka ji yana ihu sai muka yi zaton ‘yan iska ne suka kai masa hari amma da muka isa wurin sai muka ga baya tare al’aurarsa kuma karensa na da jini a bakinsa Inji makwabcin.

Itoro ya ce ba za a iya garzaya da mutumin asibiti ba saboda jinin da ya rufe jikinsa, don haka sai an fara wanke shi.

Ta kara da cewa a lokacin da muka gama tsaftace shi, yana zubar da jini sosai kuma a kan hanyar zuwa asibiti ya mutu”

Mutumin yana zaune shi kadai yayin da aka aurar da ‘ya’yansa mata kuma suka zauna nesa da shi. Tuni aka kai shi kauyensu domin yi masa jana’iza.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button