NOVELSUncategorized
KARUWAR GIDA 2

TSOKACI
wannan labarin bai shafi wata ko wani ba,na rubuta shine domin ganin yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamani duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zukatan ku,ba nayi ne dan son yad’a bad’ala ba zanyi ne saboda na zak’ulo wasu halaye da suka shiga gidan aure.Duk wanda yaga abinda bai masa ba yana da kyau ya bude shafin zagina k’ofa a bude take domin karbar hakan daka ko waye zagi d’an zagawa ne nasan baya tabo????♂azagi kowa normal ne????
????2⃣
Amsawa ZAINAB tayi da toh, ta sami d’aya daga cikin kujerun da suke gurin ta zauna hadi da rungume ANAS,” ita kuwa Hajiya Rukaiyya pharmacy dake cikin asibitin ta nufa kai tsaye domin sayo magungunan da aka rubuta musu,” tafiyarta kadan ZAINAB ta fada duniyar tunanin baya yadda rayuwar ta kasance tsakaninta da mijinta uban ‘ya’yanta wanda take kallon a matsayi sanyin idon ta a wancan lkc ba yanxu ba,tunawa tayi da irin soyayyar da ta nuna mishi had’i da bashi kulawa haka shima daga nashi 6angaren sam baya son abinda zai bata mata zuciya,rayuwa ce mai ban sha’awa mai cike da kaunar juna tunda ZAINAB ta auri RABI’U bata taba kai k’ararshi ba haka shima bai taba kai tata k’arar ba sai lkc da ta sami cikin MARIYA ne aka fara samun matsala domin kuwa cikin yazo mata da wani irin yanayin laulayi mai daga hankali komai taci sai ta amayar dashi,aman yakan zo matane a ko wanne yanayi babu dare babu rana,wannan ce tasa RABI’U ya fara tsanarta da hantarar ZAINAB a ko wanne lkc hakan ce tasa duk abinda ZAINAB ta ta6a RABI’U baya iya amfani dashi ga k’yara da hantara a duk lkc da ta fara amaye_amayenta haka zai tsallake ya barta babu tausayawa ya fita , tun abin baya damunta, har ta fara tsangwamar kanta da cewar ko RABI’U ya daina sonta ne? take ta k’aryata zuciyar ta akan abin da take zargi” duk abinda ZAINAB tace tana marmari a matsayinta na mai ciki bazata samu daga gareshi ba, tun tana iya tashi tayi komai da kanta har hakan ta gagara wannan hujjar ce tasa ZAINAB ta nemi izinin RABI’U da ya barta ta tafi gida tayi jinya acan” Katseta yayi da wani wawan mari hadi da daka mata tsawa na cewar ai daman ba d’aureki nayi ba ko an gaya miki cewar zamanki anan yana da wani muhimmanci a gareni ne?” Dafe kumatu ZAINAB tayi hadi da kallonshi cikin mamaki duba da irin yadda ya rufe ido yake ta faman masifa kamar bai san da wacce yakeyi ba ya fice ya barta anan tsugunne kan gwaiwuyinta ,can kuma sai ta tuna ai dole zaiyi masifa duba da yadda ta saba masa da mi’ka mishi jikinta a koda yaushe, kamin cikin ya samu, tayi iya yinta itama wajan taga tana iya jure masa a duk lkc da yaso hakan amman abin yak’i domin kuwa duk lkc da RABI’U yazo kwanciya da ita ji take yana mata wani irin wari wannan ce take k’ara sa ambaliyar amai da zarar ya nemata” shi kuwa sai yake ganin ai ta raina shine hadi da wulak’anci shi yasa ko tausaya mata baya yi a duk lkc da yaganta a irin wannan halin. tashi tayi da k’yar Ta mike ta goge hawaye da yake fuskarta ko wanka batayi ba ta sake kaya ta dauki kudin mota ta nufi gidansu,”tun daga sallamarta mahaifiyar ta tabbatar ba lfy ba, duba da yadda taga ZAINAB cikin tashin hankali hakan ne yabata damar tambayar ZAINAB ko lfy?” Asmwa ZAINAB tayi jiki a san yaye da cewar lfy qlu MAMA, ta tsuke bakinta daga haka ta k’arasa dakinsu inda k’anneta suke, duk suka tashi da murnar ganin yayar tasu”ta amsa fuska babu walwala ta nemi gefen gado ta kwanta ba tare da ta kara cewa kowa komai ba a haka bacci yayi awan gaba da ita.” Sanin halin mahaifin ZAINAB da mahaifiyar tata tayi ne yasa ko bin ta kanta bata k’arayi ba domin ba nisa yayi ba tasan da zarar yazo ya sameta tare da ZAINAB din zaice tana kitsa mata wani abune na rashin arziki tunda tun farko sai da ta nuna bata son ZAINAB ta auri RABI’U amman ZAINAB ta k’ek’ashe idonta da cewar shine za6in zuciyar ta.” ZAINAB bata fi minti talatin da kwanciyar ba mahaifinta ya shigo inda mahaifiyarta ta sanar masa cewar ZAINAB tazo”da kanshi ya k’arasa har kofar d’akin da take kwance yayi sallama yasa d’aya daga cikin k’anneta su taso ta,a firgice ZAINAB ta tashi domin tasan mahifinta mutune mai a k’idar gaske baya daukar raini, fitowa tayi da sauri wanda yayi dai2 da tashin zuciyarta nan fa ta dinga amai babu k’auk’autawa ganin haka shine ya hana mahaifinta yin fad’an daya saba. Ya koma dakinshi kai tsaye da cewar idan ta natsa yana jiranta ta sameshi can” kai kawai ZAINAB ta daga alamar toh ta cigaba da yin aman a inda ya barta. Mahaifiyarta yi tayi kamar bazata kawowa ZAINAB dauki ba, sai da taga abin ya ta’azarra sanna ta baro inda take zaune take aiki ta zo kanta domin tallafa mata” a hankali ta janyeta daga inda take ta samo ruwa da tsumma ta gyara wajan sanna ta sake komawa ta hada ruwan wanka takai mata band’aki, a sanyayye ZAINAB, ta mik’e tayi wanka,ita kuwa mahaifiyar tata dakin yaran ta koma ta kara gyrawa sannan ta koma kan aikin da takeyi, ta fahinci halin da ZAINAB take ciki watau na samun cikin nata ko daga yanayin sauyawar walwalarta da kuma daukewar da jikinta yayi ga uwa uba amai da takeyi,” wannan ne ya tabbatar mata cewar yar tata ciki gareta., Ba wani 6ata lkc ZAINAB tayi ba wajan wanka ta fito ta koma dakin k’annen nata ta takure, kunun tsamiya mahaifiyar ta damo mata ta shigo ta bata tace tasha”ba qaramin dadi kunun yayiwa ZAINAB duba da yadda ta kasance cikin rashin jin dadin bakinta, a hankali ta ringa shan kunun sai gashi ta shanye shi kamar wasa ga mamakinta kuma batayi amai ba, ganin ta sami natsuwa ne yasa mahaifiyar ta, shigowa ta sanar mata da cewar taje mahaifinta na jiranta” amsawa ZAINAB tayi da toh ta tashi ta nemi hijab dinta ta saka ta bi bayan mahaifiyar tata dakin mahaifinta ,tayi sallama suka amsa mata” zaune ta sameshi mahaifin nata yana duba littafin addini, ya taso akan son yawan karatu k’ananun littafai na addini, sai da yakai k’arshen karutunshi ya dago ya kalli ZAINAB da cewar na tamabayi mahaifiyarki ko lfy kika zo gida? Tace min bata san dalili ba shine nace kizo naji daga gareki” amsawa ZAINAB tayi cikin rawar baki da cewar daman banida lfy ne shine na taho” kallonta ya k’arayi cikin ido da cewar uhumm?” Tai shiru a karo na biyu” Ko RABI’U ne yace kizo gidan? Ta girgaza kai”, ya k’ara da cewar toh mekike nufi? Tayi shiru nan fa ya ringa yi mata fad’a kamar zai doketa hadi da cewar shi gidanshi ba’a isa a ce anyo yaji har an zauna ba” dan haka ta tashi ta shirya ta koma dakinta, ganin yadda mahaifin ZAINAB yake ta fada babu sauki ko daga k’afa hakan ne yasa mahaifiyarta bata saka baki a maganar ZAINAB ba.” Hakan ce tasa ZAINAB dole ta sake kamo hanyar dawowa gidan RABI’U gwaiwa babu kwari ta dawo,ko data dawo haka rayuwa ta cigaba da tafiya a tsakaninta da mijinta yau da dadi gobe babu, gashi tana tsoran taje gida ta Sanar a haka dai har cikin ZAINAB ya isa haihuwa bata tsinke da al’amarin RABI’U ba sai a wannan daren da zata haihu da ta rok’eshi da magiyar yaje ya sanar da mahaifanta halin da take ciki” ya amsa, fita yayi ya nemi mai mashin ya daukeshi yaje gidan su ZAINAB yayi sallama a lokacin yayi sa’ar mahaifinta ya dawo daga masllaci ya sanar masa da cewar ZAINAB tana gida tana nak’uda aje kanta, da sauri malam AUDU watau mahaifin ZAINAB ya koma ya sanarwa da mahaifiyarta halin da ZAINAB take ciki hadi da yi mata umarnin ta shirya taje gareta,” toh kawai tace a hanxarce ta koma dakinta, ta dauki hijab, ” bai tsaya jin ta bakin matarshi ba yasake dawowa kofar gida domin neman shawarar sirikin nashi kan yadda za’ayi da ZAINAB ga mamaki yana fitowa baiga dan mashin da yakawo RABI’U gidansu ba bare RABI’UN mamaki ne ya rufeshi amman sai ya kawo ko firgicine hakan tasa ya koma cikin gidan domin kara SA mahaifiyar ZAINAB tayo hanzari su tafi tare, A soron gidan yayi kaci6us da mahaifiyar ZAINAB din yace mata yawwa kin taho?” Ta amsa da cewar eh” yace hanzarta muje na rakaki mamakine ya kama mahaifiyar ZAINAB ganin yadda MALAM AUDU ya keta rawar jiki, batayi tsammanin hakan daga gareshi ba tunda tasan mutum ne mai tsatsauran ra’ayi” tafiya suka cigaba da yi har suka k’ arasa titi motar ta ratsa ta tsakiyar unguwar tasu, suka yi sa’ar samu mai texi din da zai kaisu unguwar da ZAINAB take, a hanya ne MALAM AUDU ya roki mai motar ya taimaka ya kaisu har kofar gida yar tasu da sanar mishi halin da suke cikin ya tausaya musu matuk’a driver, sanna ya karfafa musu gwaiwar zai taimakesu zuwa gidan yar tasu.” ita kuwa mahaifiyar ZAINAB jinsu kawai takeyi amman bata fashintar maganar da malam yakeyi da driver sabida hankalinta baya tare da ita, har suka k’araso kofar gidan yar tasu,” koda sukazo a bude suka sami kofar gidan ZAINAB kamar yadda sukayi tsammani, kaitsaye mahaifiyar ta kutsakai cikin gidan bata tsaya jiran umarnin mai gidan na taba, sallama tayi tun daga tsayar gidan amman shiru har ta kusa k’arasawa d’akin Sai taji ZAINAB ta amsa da k’yar hakan ne yasa ta k’arasawa cikin dakin da saurin inda ta sami ZAINAB kwance cikin jini kware_kaware a gigice ta dagota tana yi mata sannu,kai kawai ZAINAB ta d’agawa mahaifiyarta, da sauri ta jinginar da ita jikin gado takoma waje wajan MALAM AUDU domin ta sanar mishi halin da ZAINAB take ciki” tana fita ta sanar mishi, tambayarta ya farayi da ina sirikinshi?”amsawa mahaifiyar ZAINAB tayi da cewar ai babu kowa a gidan sai ita kad’e mamaki ne ya kama MALAM AUDU amman sai kuma yayi tunanin RABI’U ko yaje kiran likitane” duk abinda akeyi driver taxi din nan yana tsaye bai tafi ba, yana jiransu ya ji idan asibitin zai kai su toh ya jirasu” nuni MALAM AUDU yayiwa matarshi da cewar ta koma ciki gashi nan zuwa”komawa mahafiyar ZAINAB tayi ba tare da tacewa mijin nata komai ba’ tana shiga sai ga mai gidan nata ya shigo shima ya shigo har tsakiyar d’akin ZAINAB din bai jira wata_wata ba ya kalli matar tashi da cewar HALIMA mai zamu jira garinyi?” Ai kawai kamomin ita muje asibiti tunda naga alamar tana jin jiki”toh kawai mahaifiyar ZAINAB tace domin ta dade bataji mai gidan nata ya ambaci sunana ta, sabida tsabar kawaici” daukanta sukayi chas har mota suka sakata,sanna mahaifiyar tata ta dawo ta gidan nata ta dauki zannuwa ZAINAB ta janyo d’akin nata ta fito ta fad’a mota,shigar su mota ke da wuya sai ga RABI’U ya dawo da sauri MALAM AUDU ya fito ya tareshi da cewar munzo gidan ne tunda nazo bamu ganka ba,gashi ZAINAB tana buqatar taimakon gaggawa shine zamu kaita asibiti” yak’e RABI’U yayiwa MALAM AUDU hadi da juya yar bak’ar ledar hannushi da cewar babu damuwa, kuje kawai zan biyo bayanku, bari na shiga na ajje ledar hannuna daman magani naje sayo mata”toh kawai MALAM AUDU yace ya koma mota a tunaninshi abinda RABI’U ya fada gaskiya ne,suka ja mota suka tafi amman ko lek’awa baiyi yace wa ZAINAB y jiki ba” haka suka nufi asibiti suka kai yar tasu babu RABI’U babu dalilinshi bare bare wani nashi duk da dare ne” a haka har Allah yasa ZAINAB ta haihu lfy ta sami santaleliyar budurwa duk da tsammaninsu ko RABI’U bai sami abin hawan da zai hayo ba tunda dare ya shura, MALAM AUDU ya buga wayar RABI’U arufe daga baya ya yanke shawarar bari ya jira gari ya k’arasa wayewa ya kira ta mahifin RABI’U ya sanar mishi, haka Kuwa akayi domin MALAM AUDU yana fitowa daga masallacin asibitin ya latsa lambar mahaifin Yayi sa’ar mahaifin na RABI’U wayarshi na bude yayi sallama a ka amsa daga can 6angaren ,bayan sun gama gaisawa ne cikin girmamawa sannan ya sanarwa da mahifin sirikin nashi cewar ZAINAB ta haihu tun daren jiya ta sami mace amman suna asibiti tare da ita,yayi murnar matuk’a shima mahaifin RABI’U sanna ya k’ara da cewar basuda labarin rashin lfy tata, domin kuwa d’an nasu bai sanar musu ba,koda mahaifin RABI’U yazo kan wannan maganar sai MALAM AUDU ya nuna mishi babu komai hadi da sanar mishi da sunan asibitin da suke watau SAUDAT clinic wanda yake bayan katangar B.U.K a nan unguwar kabuga Jan bulo daman nan ZAINAB ta sanar musu tana zuwa awon ciki, anan k’awarta RuKAIYYA SHITU ta sami aiki shine har ta bude mata file anan,” basu wani bata lkc ba suma iyayen RABI’U suka hallaci asibitin da kayan baby kaca_kaca nan fa dangin suka shiga yiwa juna murnar haihuwar da ZAINAB tayi, amman har a wannan lkc gogan naku baizo asbitin ba bare yazo yaji halin da ake ciki, duk gwaje_gwajen da za’ayiwa ZAINAB da baby anyi sanna aka sallamesu daga asibitin kai tsaye ZAINAB gidatan aka mayar da ita ta bakin mahaifin nata, wai bayason wata bid’ar tafiya gida wanka hakan baiwa mahaifiyar ZAINAB dadi ba,amman su iyayen RABI’U sai sukaji dadi kalmar MALAM AUDU domin kuwa suna ganin baya kyau tuwa ayi sunan surukar tasu a gidan iyayaenta, tunda daga asibiti MALAM AUDU yayi ma su mahifin RABI’U sallama yace zai koma gida ya shirya yaje kauye domin sanar da danginshi ya dauko wacce zata kula da ZAINAB wajan yi mata wankan jego godiya, suka k’ara yi masa da yabawa bisa hallacin da yayi musu sannan ya tafi,. Ita kuwa mahaifiyar ZAINAB kafarta kafar yarta har gidan ta,inda suka rankawa tare da iyayen mijin ZAINAB din ,suka tarar da RABI’U yana gidan yanata sharbar bacci abinshi har wannan lkc,mahaifiyar ZAINAB batayi mamakin abinda yayi musu ba tun daga daren jiya har kawo safiyar yau din” shi kanshi RABI’U tashi yayi a kunya ce bisa ga abinda yayiwa iyayen matar tashi, koda ya fuskanci basu sanarwa mahaifanshi ba sai ya marzaye idon shi kamar bashi yayi wannan rashin mutuncin ba. Da mahaifiyar ZAINAB da tashi, haka da sauran dangin haka suka hadu suka gyara ZAINAB da babynta kana suka gyara komai wanda ya lalace tun farkon fara nak’udar ZAINAB ta fara a gida” daga k’arshe mahaifiyar ZAINAB tayi musu sallama itama ta koma gida domin ta sanarwa nata dangin da mak’ofta cewar ZAINAB ta sauka lfy, “Tana isa gida ta fara aikawa makwaftanta cewar ZAINAB ta sauka lfy” nan fa gida ya cika da jama’a duk da ba ta sami natsuwar da zata aikawa da sauran danginta da suke nesa ba,amman anyi mata kara iya mutuk’a” shi kuwa MALAM tun bayan dawowarshi daga asibitin shima gida ya dawo ya shirya ya tafi kauye su watau GULU domin sanar da yan uwanshi cewar ZAINAB ta haihu lfy, ko da ya isa ya sanar musu da hakan sunyi matuk’ar farin ciki da jin yar tasu ta sauka lfy,haka dai sukai ta aikawa ‘yan uwansu na kusa ana sanar dasu cewar ZAINAB ta haihu” MALAM AUDU bai baro kauyesu ba sai da yayi duk wata shawara da yan uwanshi kan cewar INNA TALATU ce zata zaunawa ZAINAB tai mata zaman da6aro” sakamakon ita kade ce mace a gurin mahaifan su MALAM AUDU” tana zaman gida ne sakamakon rasuwar mijinta wannan hujjar ce tasa koda suka sanar mata da kudirin yayan nata,batayi musu ba, batada miji bare ta buk’aci jiran umarni” a yammacin ranar suka taho da yayan nata hadi da kayan sha tara ta arziki wanda yan uwa da dangin suka hado aka fara yo gaba dasu kamin su biyo bayan su kashe gari Domin ganin lfy maijego”
bayan saukar MALAM AUDU gida da shi da y’ar uwanshi, gaisawa kawai tayi da matar yayan nata, tayi musu sallama da cewar ta tafi kula da tafiyar yarta watau ZAINAB” zo kaga rawar kai gurin angon karni watau RABI’U domin shima kayayayaki ya sayowa jaririyar da ZAINAB masu kyau da tsada, sai shiga yake yana fita shima kamar bashine yake nuna halin ko in kula da ZAINAB din ba”Ita kanta tayi mamakin yadda taga cikin k’ank’anin lkc mijin nata ya sauya kamar bashi ba”.
“Dangin mahaifinta dana mahaifiyarta duk sunzo ganin lafiyarta kashe garin da ta haihu kamin yan suna su zo suna”.
Haka dai RABI’U yayi ta hidima shida iyayenshi da sauran dangin da abokanan arziki” Suma a nasu 6angaren dangin mijin na ZAINAB sunyi duk abinda ya dace sannan domin kuwa tunda suka dawo daga asibiti lbr ya ishe sauran danginsu haka sukaita zuwa ganin jaririya da kayayayyakin su na barka”Abufa yakai Abu domin kowa yasan mahaifan RABI’U mutane ne masu kara da zuminci shi yasa duk wanda yaji matar d’ansu ta haihu baya k’asa a gwuiwa sai yazo yaga lfy ZAINAB da ‘yart haka dai ‘yan uwa da abokanan arziki sukai ta zuwa da abin arzik’insu”.
Acan ma gidan su ZAINAB haka iyayenta da danginta suka kawo nasu kayan sha tara ta arzik’in suka kawowa ZAINAB,”
“har akai suna yarinyar taci suna MARIYATU sunan kakar RABI’U ce ta wajan uwa gidan baya yankewa da jama’a wannan ce tasa RAB’IU ya mayar da hankalinshi sosai kan ZAINAB da ‘yarsu gudun kar aga wani bak’on yanayi daga gareshi lbr ya sami iyayenshi wannan ce tasa ya mantar da ZAINAB duk wata cusgunawar da yayi mata a baya”…………..