KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

” Na’ki gida kawai nake son dawo wa, mai yasa?” tace dashi, “‘kauyen babu dad’i, ina son na dawo kafin ki dawo, don Allah ki ro’ki Dady na dawo”.

” I miss you sister nd mamina, Auwal kenan Dady fa ya kafe ya nace yace sai ka gama sannan zaka dawo, kuma ma idan nazo dole nazo na ganka”.

“Kad’an mafa ya rage maka, sister baza ki gane ba Wallahi ni gida nake so”.

“Yanzu ya kake son ayi?, ki ro’ke sa nasan zai amince na dawo kinji tawa”.

Shiru tayi ya sake cewa ” pleaseeeee” .

“Naji, amma kamin al’kawari zaka koma duk lokacin da aka bu’kaci hakan”.

” Na amince” nan dai sukai sallama.

            °°°°°

Kwana hud’un nan Joy ta kasance cikin tsananin damuwa, damuwa ba d’an kad’an ba.

Tana son ganin sa, tana son jin murya sa, amma ta yaya? tunda ya’ki fita daga gidan.

“Inason ganin sa, bazan iya barci ba yau idan ban gansa ba” tace cikin damuwa.

Mi’kewa tayi tare da shirya wa, yau anyi abin arzi’ki, domin shigan dogon riga mai roba d’in nan tayi.

Yayi mata Kyau matu’kar gaya, har dasu rolling.

Da yake yau Sunday akwai church madam Gloria ta dad’e da tafiya.

Ta fashe jikin ta da turare mai dad’in ‘kamshi, tana gama shirya wa ta kulle gidan sanan ta nufi gidan Auwal gaban ta na mugun fad’uwa.

Tura ‘kofar tayi taji ya bud’e, tana jin mugun fad’uwan gaba tayi cikin gidan cikin sand’a kamar wata ‘barauniya.

Tunda ta shigo take jin ‘kamshi girki da mamaki ta ‘karisa shigo wa.

Babu kowa a tsakar gidan don haka d’akin taga an sakayo ta nufa.

Tura wa tayi wani sanyin dad’i da ni’ima taji, “hmm, komai naka cikin tsarin yake kuma mai kyau ne. Ina son ka my man”.

Shiga tayi babu kowa a parlour, zama tayi a d’aya daga cikin kushin d’in parlour.

Tayi kusan 5mint babu alamar sa, don haka sai ta nufi bedroom d’in sa.

Fito war sa kenan daga toilet, towel d’aure a jikin sa, d’aya kuma yana goge fuskan sa.

Tana ganin haka ta dawo baya tana mai runtse ido tare da dafe ‘kirjin ta dake bara zanan fashe wa.

Ga wani mugun tsoron sa da taji ya ziyar ce ta, don sai yanzu take da nasanin shigo masa gida.

” Oh my god!! bari na bar masa gida tunda bai ganni ba, don idan ya ganni Allah kad’ai yasan abinda zai min”.

“Uwa uba zargin sa zai ‘kara tabbatar wa” tace tana mai fita daga parlour kamar yadda ta shigo, haka har ta fita gidan.

Tana fita ta fara sauke numfashi kamar wacce tai gudu, tana cewa “thank god! I’m safe”.

Tana mai dafe da ‘kirjin ta.

Jin kamar motsi tabar jikin gidan da gudu ta koma nasu Aisha.

” Ashe ba kowa bane” tace tana dariya da tunda nake da ita ban ta’ba ganin tayi ba.

Kuma dariyan ba ‘karamin kyau yayi mata ba.

Tana nan tsaye na kisan 30mint sai gashi ya fito cikin shiga na alfarma.

Farar shadda yasa, shaddar tayi matu’kar ‘kar ‘bansa.

Bai lura da ita ba sam har ya rufe gidan nasa, yazo zai wuce ne ya gan ta.

Kauda kansa yayi tare da had’e rai, gaban ta taji ya fad’i amma ta daure tace cikin sanyin murya “doctor barka da safiya” yayi banza da ita.

“Doctor I’m sick” nan ma ya share ta, domin tafiyar sama yake.

“Hmm” tace tare da lumshe idanun ta, tana mai kallon bayan sa har ya ‘bace mata.

“Allah tsareka ya kareka my one nd only” tace farin ciki na cika ta.

°°°°Shiko Auwal yaje sayowa su mami tsaraba ne domin anci nasara Dady ya yarda ya dawo yayi kwana goma.

Saboda farin ciki yasa yaje har cikin garin keffi yayi musu tsaraba na gani na fad’a.

***Joy ko bayan tafiya sane ta nufi church tana ta faman murmushi, koda tazo uwar tayi garin ciki sosai domin bata ta’ba zuwa da wuri irin haka ba.

Bata tashi zuwa sai an tashi ko an kusa tashi, duk fitinan uwan da masifar ta bai sa gobe taje da wuri.

Bayan sun tashi barin uwar tayi tayo gida domin ganin sanyin idanun ta.

Koda tazo bai dawo ba, don haka sai ta bud’e gidan su ta shiga, wanka ta sake she’kawa .

Bayan tai wanka ta zauna ta tsantsara kwalliya, tasaka riga da wando, rigan mai dogon hannun sai dai ya kamata cif.

Wandon ma dogo ne amma ya matse ta, a shekarun nan nata tana mamaki girman halintatan ta, tana ganin wad’an da suka girme ta da shekaru goma ma basu da cikin halita irin tata.

Komai ta mallaka, jujjuya jiki ta kamayi tana kallon mirror, ta saki wani ‘kaya tattacen murmushi.

“Kai ma nasan kana ‘kasa wa, nasan ina burge ka, nasha jin anace wa maza nason irina”.

” Kama kana so ko?” tana mai kashe ido d’aya, dariya ta fashe dashi.

“My man, humm, kana mugun burgeni, kana tafiya da imani nah” tai ‘kwal-‘kwal.

Cikin tausayin kanta tace “zaka aure ni?, ka aure ni don Allah, wallahi babu wanda ya ta’ba sanina, ban ta’ba fasikanci ba. Zina! Na tsane sa, abinda baka sani ba inda tsoro bazan iya bawa wani kai na ba”.

” Nasan darajan kaina, ganina da d’an iskan nan da kai Wallahi fyad’e yake son min, bai min komai ba shine ka ceceni”.

“Ka bar zargi na don Allah” ta fashe da wani irin kuka mai tsanani bayan ta gama surutun ta.

Sai da tayi mai isan ta sanan taje ta wanko fuskan ta, wanan karon powder kawai tasa sai man baki

Fita tayi waje, ganin ‘kofar gidan sa a rufe yasa ta tsaya ‘kofar gidan su idon ta nakan hanya don ganin ‘bilowar sa.

Tana nan tsaye Aisha ta fito, ido Aisha ta kura mata kamar wacce bata ta’ba ganin taba.

Hararan ta Joy tayi tare da d’auke kai, dariya ta bawa Aisha, ‘kariso wa gare ta tayi tana mai cewa “Allah besty kinyi kyau, wanan da dama dama dai, Allah sa kidai na saka irin wad’an nan ki dawo saka namu”.

” Shigan mutunci sai yafi kyau dake” ta ‘karsa murmushi d’auke a fuskan ta.

“Bazai ta’ba yuwu wa nasa kaya irin naku ba, ke bazan iya ba sam, haka kawai nasa kayan da zai rin’ka damuna”.

” Uhum’um bazan iya ba, ku muslmai gaskiya addinin Ku da kawai takurawa”.

“Muko namu sam babu ta kura, za kai shigan ka yadda kaso”.

” Ni wallahi kinzo kina ma damuna, kina samin ciwon kai kina ta sani surutu”.

“Allah baki ha’kuri besty nayi nan” ta gane sarai fishi tayi amma ko a gefen gyelen ta.

Tafiyan Aisha da kad’an sai ga Auwal ya fito daga taxi.

Kayan sa ya fara fito wa dashi, bayan ya gama fito wa dasu tas ya sallami wanda ya kawo sa.

Waige yayi ko zai sami wanda zai taimaka masa, kawai sai yaga Joy tsaye tana kallon sa.

‘Dauke kai yayi tare da bud’e gidan sa ya fara shiga da kayan.

Ya kai na farko da na biyu duk tana tsaye, ya dawo domin sake kwashe sauran.

Ya kai hannun sa da ninyan d’auka itama takai nata.

‘Daga kai yayi tare sa wurga mata wani hararan mai firgitar wa.

Ta tsorata matu’ka amma bata dan dara ba.

Yana d’auakn wanda takai hannun yayi ciki dashi ita kuma ta kwashe sauran ta bisa.

Ya aje kenan ya juyo sukai karo.

Sakin kayan tayi tare da sakin ‘kara “wayyo Allah doctor akawai zafi sosai wallahi” tace cikin shagwa’ba.

Cikin masifa yace “amma dai ke jakace ko?” shiru tayi cikin jin zafin maganan sa tana kallon sa.

“Dai na kallo na mayyah da ‘ki’kiya, ballagaza, shashsha sauran maza”.

” To duk mai tanki nafi ‘karfin ki wawuya kawai, fice min a gida idan ba haka ba” yayi ‘kwafa.

Kuka ta fashe dashi tare da cewa “ni kazaga?” Yace cikin tabbatar wa “eh dan ubanki ko kina da abinda zakiyi ne?”.

Zuciyar ta taji yana ta farfasa, don haka tace ” karka sake zagin ubana idan ba haka ba zakai nadama”.

“Nadamar uwarki zanyi wawuya?, to ance ubanki ke uban naki ma yaci uban sa, kakanki kenan”.

” To wallahi duk maitarki haka zaki bar Auwal, fita maza”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button