KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Son da take masa yasa ta kasa yin abinda tai ninya don haka sai ta tashi tabar masa gidan sa.

Ganin comments zai taimaka matu’ka wurin cigaba da labarin nan.

Amma banyi al’kawarin kullum ba, idan na samu time zakujini. Kuyimin uzuri don Allah, ba’a son raina bane, ina tsananin ‘kaunar Ku masoya na farin cikin ku shine nawa ngd????????

Comment & share please
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????

‘KAUYEN ‘YAR KADDE

????????????????????????????

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
MASAUKIN SO
SHI NAKE JIRA
BA JINSIN MU BACE
HAMDIYA DA HAMNA

Dedicated to my family

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

????1⃣9⃣to2⃣0⃣

°°°°°°

Joy tunda ta tashi take jin ta wani iri, haka take shirin makaranta cikin sanyin jiki, bayan ta gama ta sallami maman ta ta fito, tsaye take a ‘kofar gidan su tana kallon gidan Auwal tana jin fad’uwan gaba mai tsanani a tare da ita. A haka Aisha ta fito ta ganta, ‘kariso wa wurin ta tayi tare da ta’ba ta domin tayi nisa a tunani, tace da ita “besty muje” figit ta dawo daga dogob tunani da ta tafi.

Har sun fara tafiya ta waigo tana mai sake kallon gidan Auwal, gani take zai fito, “lafia kuwa kike besty?” Shiru babu ansa sai ma kauda kanta tayi idon ta fal da hawaye jikin ta na bata cewa wani mummunan abu zai same ta.

Wani zazza’bi taji yana son kama ta, domin fad’uwan gaban ta ‘karuwa yayi wanda har sai da Aisha taji.

Tsayawa tayi tare da ru’ko ta, tana ware ido cikin tsoro da damuwa tace “besty baki da lafia ne?” kallon ta tayi tare da bud’e baki da ninyan yin magana, amma ta kasa sai ma fashewa da kuka tayi tare da zamewa ta zauna a dam’ban kan hanya.

Dur’ku sawa Aisha tayi itama har ta fara kuka, domin Allah ya saka mata tsananin ‘kaunar Joy d’in.

Kamo ta tayi da ninyan d’ago ta amma ta’ki bata dama.

Cikin kuka tace “besty tashi mu koma gida tunda baki da lafia” girgiza mata kanta tayi, alamar a’a.

“Meke damun ki besty? kanki d’aya kuwa?, kina ganin inda kike zaune kuwa?” shiru babu ansa sai cigaba da kuka take mai matu’kar ban tausayi.

Rungume ta tayi suka cigaba da kukan su babu mai lallashin wani, ga garin shiru-shiru da yake anyi ruwa sama da asuba kowa ya ‘boye a d’aki saboda sanyi.

°°°°°

“Ya zanyi na sami motar da zata kaini gida?, shegen ‘kauye babu ko taka mamman mashin bare ka samu mota, wallahi yaya kun cuceni” cewar Auwal da ya gama shiri tuntuni yana mai burzar da isaka.

“Wayyo mamina ya zanyi yanzu?” d’ako wayar sa yayi tare da dialing number mamin tasa.

Tana peaking ya fashe da kuka kamar wani yaron goye.

“Menene son?” shiru ya’ki magana sai cigaba da kukan sa yake.

“Na shiga uku son meya faru kuma? yi magana mana, koso kake ka ruguza farin ciki na? ina murna zaka dawo yau na ganka amma kana kuka, oh Allah na yaushe yaron nan zai girma”.

Cikin shagwa’ba yace ” mami babu mota fah a garin nan, yanzu ya zanyi na taho? ko mashin basu da”.

“Jiya da zani cikin gari ba’karamin wahala nasha ba” .

“Yi ha’kuri my son, ka fita kaje cikin gari ka nemo taxi ya kawo ka, ko nawa zan biya kaji? maza my son”.

” To mami na, amma fah da wuya ‘kafana bai kumbura ba, jiya mafa ‘kafana na taka har na kusa barin garin sanan na samu mashin”.

“Insha Allah bazai kumbura ba, da yarda Allah kana fita zaka samu maza yaron mami”.

Kashe wayar yayi tare da mi’kewa ya fita, sanye yake cikin ‘kananun kaya kayan sunyi matu’kar kar’ban sa, saboda sanyin da ake sai ya sanya jacket akan kayan.

Tafiya yake cikin natsuwa, da kagan sa kaga had’ad’an gaye.

Har yanzu suna nan zaune suna ta faman kuka kuma cikin sanyin, fad’uwan gaban ta yana ‘karuwa, jikin ta na bata yana kusa da ita.

Waigen hanyan gidan su tayi ta hango sa gaf dasu, murmushi ne ya su’buce mata, tare da kafeshi da ido tana share hawaye dake zubo mata.

Da mamaki Aisha ke kallon ta, murmushi da bata ta’ba gani ba a fuskan ‘kawar tata ce ta gani kwancen a fuskan ta.

” Besty kece kuwa? wallahi kinyi mugun kyau, ko dama ke kyakkyawa ce, kin ‘kara kyau” Aisha tace tana mai ta’ba ta.

Ta’ba tan da tayine ya fargar ta ita ‘baran-‘bara man da take son tafkawa.

Domin tayi al’kawari ko son sa zai kashe ta ko uwar ta baza ta sani ba har sai idan ya furta mata cewa yana son ta.

Kauda kanta tayi daga kallon sa don kar Aisha ta d’ago wani abu.

Murmushi gefen baki tayi tare da cewa cikin miskilancin ta tana mai kallon sa da ya kusa inda suke.

“Nagode” tace tare mi’kewa, mi’kewa itama Aisha tayi tana cewa “besty kin ‘bata kayanki, kuma kinsa mun makara sosai mu koma gida tunda haka kike so”.

“Amma wai don Allah me yasaki kuka ne haka? kuma lokaci d’aya kin ware?”.

Share ta tayi tana mai du’kar da kai ‘kasa, domin Auwal yazo dai-dai dasu.

Yana ganin su ya d’auke kai fuska a murtuke, yana wuce wa Joy ta sani numfashi tare da dafe zuciyar ta.

Tayi shiru na wani lokaci sannan ta fara tafiya, biyo bayan ta Aisha tayi tana mamakin miskilancin bestyn nata.

Haka suka zo har gida babu mai ce da d’an uwan sa komai.

Aisha ce dai tace da Joy lokacin har tasa ‘kafar ta a cikin zauren gidan su ” sai anjima besty” kai kawai ta d’aga mata tare da shige wa gida.

***”Lafia kika dawo yanzu? anya ma kuwa?, bakuje makaranta taba” cewar maman Joy.

Jefar da jakan makarantan tayi a tsakar d’akin ta zauna a kujera tayi shiru na wani lokaci.

Sannan tace cikin ‘kasa da murya “bamu sami zuwa ba. Meya sa to” cewar uwan shiru nayi bance komai ba sai ma kwanciya ta da nai ina mai lumshe ido.

Girgiza kai mama tayi tare da cewa “ubangiji ya shirye ki” ta shige cikin d’aki.

Murmushi nayi tare da cewa a hankali “ameen, handsome ina zaka ne haka cikin kyakkyawar shigan dani kad’ai ya cancanta na gani?”.

” My man karka kalli kowa please, zama makaho kaji, ka zama kurma kaji”.

“Allah sa karsu kallan min kai” tace tana dariya a hankali tare da rufe fuska.

A haka mama ta fito ta same ni, “anya bazan kaki a duba ‘kwa’kwalwarki ba?, kwana biyun nan baki da aiki sai dariya da magana ke kad’ai”.

Kallon mama nayi tare da shagwa’be fuska ina mai cewa ” lafia ta qalau” na mi’ke, cire uniform d’in nayi tare da shiga cikin d’aki na d’ako zani na d’aura a ‘kirji.

Har zanyi bayi sai mama take cewa “bari na le’ka ‘kawata na dawo, tunda yau kin’ki makaranta sai ki mana abinci” har ta fita ta dawo ta sake cewa “Joy kina ganin doctor kuwa?” shiru nayi ina maijin sanyi a raina danaji an anbaci masoyina.

“Ina magana kina jina kuma, banson iskanci” cikin sanyin murya nace “a’ah” kawai nayi toilet.

Ina jinta tana cewa “ko lafia yake oho” ta fice.

Na fito wanak kenan naji ‘karan mota, gabana naji yayi mugun fad’uwa don haka banjira komai ba nayi waje da d’aurin ‘kirji.

Mota nagani a dai-dai gidan Auwal, tsayawa nayi tare da kallon gidan inajin wani yanayi .

Ganin wani ya fito a gidan da kaya yasa nayi cikin gidan.

Karo mukaci dashi, “asshhh” nace ina dafe goshi na.

Kallon sama da ‘kasa yayi min tare da tofar da yamu ya ra’ba ta gefe na ya kwashe kayan da suka zuba ya fita ya barni a wurin.

Shiga cikin parlour nayi naga kaya a tsakar parlour harda akatin kayan sa.

Zama nayi ji’bus tare da ri’ke kaina da ya saramin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button