KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bansan sanda hawaye ya zubomin ba, ina zaune ya shigo shida mutumin ko yasan Allah yayi ruwana a wurin kwashe sauran sukayi tasa ina kallo hawaye nata kwaranya.
Bayan sun gama fita da kayan ya dawo don rufe gida, tsaye yake yayi shiru don baison magana ta had’a su ko kad’an.
Bai aune ba yaji an rungume sa tare da cewa “ina zaka doctor? nine ko? yi ha’kuri daga yau na bar maka magana don Allah ka zauna” nace ina kuka mai cin rai.
Wani irin mugun abu yaji yana fuzgan sa, domin ta mana masa a bubuwan ta a jikin sa.
Ji yayi ‘kafa funsa suna neman gagaran sa, yun’kurin ture ta yayi amma ina ta ‘kan’kame sa.
Cikin wani yanayi yace “don Allah rabu dani tafiya ce a gaba na, nd sau nawa nake gaya miki ki rabu dani ki fita harka ta?”.
” Nifa ba d’an iskan bane” “nima haka” nace cikin kuka ina zare jiki na.
Tsare sa da ido nayi tare da cewa “ina zaka?”.
” Inda kika aiken uwata” yace yana hararana.
Murmushi mai ciwo nayi tare da cewa “na takura ka ko?, oho miki, sanan banda lokacin kini sai kibi wani bani ba don ni Auwal gaba nayi”.
Dur’ku sawa nayi gaban sa tare da son ri’ke ‘kafar sa, han’barina yayi tare da cewa ” fita min a gida na rufe malama”.
Ko motsi banyi ba, wata irin tsawa ya daka min, ba shiri na mi’ke nunamin hanya yayi tare da cewa “maza barmin gida na, maza ko kuma na caza miki kaman nu”.
” Kuma gargad’i na ‘karshe ki fita gona ta” yace yana mai sake daka mata tsawa.
Da gudu na fita, domin ya mugun firgitani.
Rufe ‘kofar parlour da gidan yayi tare da shiga mota suka bar wurin .
Ina tsaye a cikin zaure ina kallon sanda motar tabar ‘kofar gidan.
Kuka na na cigaba dayi na dad’e ina kukan, ban bari ba sai ma shiga gida da nayi ina cigaba da kuka na, babu maganan girki sam don na manta da lamarin sa, kuka kawai nake ta…
••••••••••••••••••°°°°°°°°°°°°°•••••••••••••••••
Tunda Auwal yaga sun kusa layin su wani irin farin ciki yakeji, yau dai zai ga mami zai kwanta a cinyan ta, zata basa abincin ta mai dad’i zata cidashi.
Haka yayi ma mai taxi kwantan ce har suka zo ‘kofar gidan su.
Horn driver yayi, mai gadi ne ya fito har wurin motan yazo tare da kallon mai taxi d’in yana cewa don sam bai lura da Auwal ba.
“Wa kake nema ne malam?” Kafin ya bada ansa Auwal ya fito daga cikin motan.
Hararan sa yayi tare cewa “zaka bud’e ko sai ka rasa aikin ka?” da gudu ya nufi get d’in yana cewa “yi ha’kuri alhaji bansan kai bane”.
Koma wa motar Auwal yayi driver ya tada motar suka shiga, mai gadi na cewa ” barka da dawo wa ” hannun kawai ya d’aga masa.
A compound d’in gidan Auwal yace wa mai taxi ya tsaya, yana tsayawa ya fita a motar .
Mai aikatan gidan dake kai kawo suna ganin sa suka nufo wurin da gudu sauri-sauri.
Sannu da zuwa suka masa ya ansa yana shige wa ciki, yana shiga ‘kayataccen parlourn gidan babba dashi wanda aka ‘kawatashi da ababen more rayuwa.
“Mamina where are you?, am back, your handsome is back” yace yana kalle-kallen parlour don ganin ta ina mamin tasa zata fito.
Da murmushi farin ciki uwar ke sakowa daga steps .
Da gudu ya ‘karisa gare ta, yana isa gare ta ya rungume ta.
Cikin farin ciki tace “oyoyo my happiness, godiya ga ubangijin tali kai da ya dawo min da farin ciki na lafia, welcome back autan mami, jarumin jarumai”.
” Fitilar gidan Kabir Mu’azam, farin wata shakallo, sannu da zuwa shalelen Rahama da mami”.
Wani irin farin ciki da natsuwa yakeji jinsa a jikin mamin sa.
Cikin shagwa’ba yace “mamina I miss you so much” kamar zaiyi kuka.
Bubbuga bayan sa tayi tare da cewa “nima haka son, muje kayi wanka sai kaci abincin ka huta”.
Tana ri’ke dashi sukayi d’akin sa, had’a masa ruwan wankan tayi tare da kama sa, sai da takai sa bayin sanan tace ” maza kayi wanka ka fito my handsome ” ta fita.
Sai da ta fitar masa da kaya sanan ta sauka, zaune ta tarar da Baraka cikin girmama wa tace “HAJIYA wanda ya kawo autan ki yana jira a sallame sa”.
” Ayyah yana ina?” “yana compound, okay kun bashi abinci kuwa?”.
” Eh” “okay ina zuwa” tace tare da wuce wa d’aki.
Kud’i ta d’ebo masu yawa bata damu da ta duba ko nawa bane ta fito.
Har inda yake taje ta basa tare da masa godiyan kawo mata yaro cikin ‘koshin lafia.
Godiya shima yayi sosai yana mamakin karamcin da aka masa, yana mamakin irin kud’in da aka basa .
Cikin farin ciki yabar gidan bayan ya fitar musu da kayan Auwal d’in.
°°°°Cikin jin dad’i yayi wankan sa, gurje jikin sa yayi sosai da sosai, kai kace zai sake fata.
Yana fito wa ya wani fad’a bed d’in sa yana cewa “Allah sa mami karta yadda na koma wanan ‘kauyen mai cike da ‘kazamai”.
Tsaki ya saki domin Joy ce ta fad’o masa a rai.
Tashi yayi tare da shafa mayuka maau tsada sai ‘kamshi suke.
Kayan da mami ta fitar masa ya saka tare da feshe jikin sa da turaruka.
Fito wa yayi sak Auwal d’in mami ba na ‘kauye ba.
Tunda ya sako mami ta kafe sa da ido har ya ‘kariso gaban ta.
Hawaye taji nason zubo mata amma ta matse, ta’ba wuyan sa tayi lokacin ya zauna kusa da ita.
” Auta ciwo kayi ne wai?” turo baki yayi tare da cewa “mami ba sai da na gaya miki ba?, ai wanan ‘kauyen babu abinda bazai sa mutum ba. Don Allah mami na kada ki bari na koma idan ba haka ba sai kinyi kuka idan kika ga yadda yaron ki zai koma”.
” Kayi ciwon kenan?, a’a kawai ‘kauyen ne babu dad’i ga…ga……..” sai ya kasa fad’a.
“Ga me son?” kasa magana yayi.
Cikin damuwa tace “son gaya min don Allah”.
” Idan na gaya zaki hansu mai dani?”.
“Uhum fad’a kaji my boy” turo baki yayi domin ya tsani a kira sa da boy.
“Mami niba boy bane, don Allah kibar cemin haka dani boy ne aida ba ai yun’kurin yin min fyad’e ba”.
” What!!!” mami tace tana mi’kewa…………….
Maman kids???????????? ina godiya sosai.
Comment & share please????????????????
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????
‘KAUYEN ‘YAR KADDE
????????????????????????????
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
MASAUKIN SO
SHI NAKE JIRA
BA JINSIN MU BACE
HAMDIYA DA HAMNA
Dedicated to my blood sister (Fatima Aliyu wakili) Allah ubangiji ya’kara miki lafia keda baby na
My fan’s godiya a gare ku mai tarin yawa ina matu’kar ‘kaunar ku masoya, a koda yaushe ina alfahari daku, ina jin dad’in yadda kuke bibiya na godiya mara iyaka????????
MY SAHIBA, Allah ubangiji yabaki lafia, masoya muna baran addu’ar ku, don Allah kusa sahiba a addu’a Allah ya bata lafia????????????????????????
Sister Rukyn mama ina tayaki murna nan kamla littafin ki mai suna HUSSAIN Allah ubangiji yaba da ladan fad’a sai munjiki a sabon wani littafin nan kusa????
Besty (maman Muhammad) kwana biyu shiru????Allah ubangiji yasa kina cikin ‘koshin lafia.
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
????2⃣1⃣to2⃣2⃣
Ya mutsa fuska yayi tare da had’e rai yana cigaba da cewa “da gaske nake mamina, har cikin gida wata shegiyar arniya tazo min fyad’e”.
” Kutumar uban can, waye uban ta shegiya da zata lalata min yaro?, amma dai bata maka komai ba ko?” shiru ya mata.
Kallon sa tayi na wani lokaci sanan tace tana mai koma wa inda ta tashi “my son tell me the truth”.
Shagwa’be fuska yayi tare da cewa ” yanzu mami na baki yadda da yaron ki bako?, tom shikenan ai inaga sai tamin ciki zaki yadda”.