KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Fashe wa da dariyan babban wansu dake tsaye tun fara shirmen Auwal yayi.

Waiga wa sukayi dukan su suna kallon ‘kofar parlourn.

Hararan da mami ta jefa masa ne yasa shi gintse dariyan sa.

“Na shigo?” yace yana mai danne dariyan sa, a zuciyar sa kuwa yana mai mamakin yadda mamin tasu ke zama tana sauraron shirmen autan nata.

Mai da fuskan ta tayi kan Auwal tare da cewa “oho ma, kuma mutum ya daina mana la’be ko autana?, uhmm mami na, kuma na sani sarai sai ya kai maganan gaba. kuma kin san wani abu?” yace yana mai kai bakin sa kunnin ta don kar yayan yaji, nima bai bani daman jiba.

Sai mamin da take cewa “sun ma isa ne” kawai mukaji.

Tako wa yayi ya shigo ciki, yana mai jefa ma Auwal d’in mugun kallo.

“Mami kin gansa ko?, meka masa daga dawo wan yaro?, ban san fitina fah. A saki ma yaro na mara yayi fitsari, Allah wanan karon ran kowa zai ‘baci a gidan nan”.

Gyad’a kai Auwal yayi kamar wani yaro, hakan ma yake jin kansa indai yana gaban mamin tasa.

” Tashi muje kaci abinci idan ka huta ma ‘karisa magana”.

“Ku ‘karisa shirme dai” cewar yaya nasa murya ‘kasa-‘kasa, “mai kake cewa?”.

” A’ah, ni bance komai ba mami, kama ce ” tace tana ‘kwafa.

Dining sukayi, jan masa kujera tayi ya zauna yayan na kallon su ta fara feeding d’in sa.

Ganin ba zai iya jure kayan takaici ba yace “mami ina wuni” “lafia” tace tana mai cigaba da bama shalelen ta abinci.

Shiru ya zauna kafin ya mi’ke tare da cewa “sai anjima mami” ya fara tafiya.

Cikin d’aga murya tace “dawo” dawo war yayi “shin baka ga auta ya dawo bane?”.

” Na gansa, shine ko gasheshi da hanya bakai ba?” zaro ido yayi tare da cewa “kai mami shine gaba dani koni? tayaya bai gaidani ba ni na gaida sa?”.

” Amma ai kasan daga uwa duniya ya fito ko?, sai kabari ya huta idan bai gaida kaba sai kace amma ba yanzu ba, maza masa sannu da hanya”.

Kamar zai kuka saboda ba’kin ciki yace “wallahi abinda kike baki kyau tawa sam mami”.

” To ubana nuna min abinda zanyi” “idan bai nuna miki ba ni gani nazo zan nuna miki” cewar dady dake shigo wa parlourn.

Shiru tayi kawai bata iya cewa komai ba.

Kar’ban jakar hannun sa yayan yayi sukayi sama suka bar su nan.

“Mamina mai yasa Dady bai sona?” Auwal yace yana mai jin zafin yadda Dadyn ya nuna halin ko in kula a kansa.

“Mami yau fah na dawo amma duba babu ko farin ciki a tattare da Dady, anya kuwa mami? anya shi ya haifeni?” yace hawaye na fita daga idanun sa.

“Shishhh autana, dai na zancen nan Dadyn ka na tsananin ‘kaunar ka, yafi sonka fiye da ‘ya ‘yan da..” sai tayi shiru.

Lallashin sa tayi, bayan ta gama lallashin sa sai suka mi’ke daga dining d’in suka nufi sama hannun sa sar’ke cikin na mami.

Dai-dai ‘kofar part d’in Dadyn tace “muje ka masa sannu da zuwa ko yaron kirki?”.

” Hmm” kawai yace sukai knocking suka shiga.

Zaune suka taddashi yana ma Yusif bayanin wani abu.

Zama mami tayi a kusa dashi, Auwal ya dur’kusa kusa da ‘kafar ta tare da cema Dady “ina wuni Dady” cikin sanyin murya.

Da fara’a a fuskan Dady ya ansa masa, tare da cewa “maraba da autan mami shalelen RAHAMA”.

” Yaushe a gari?” turo baki yayi tare da cewa “d’azu”.

” Madallah, ya hanya? Alhamdulillah”.

“Masha Allah” Dadyn yace yana mai cigaba da abinda suke.

Suna zaune suka gama ya sallami Yusif d’in.

Bayan fitar Yusif d’in ne take cewa “sannu da zuwa alhaji, yauwa madam, ya gidan?”.

” Lafiya qalau, ya aikin?”. “Sai godiya ubangiji” cewan dadyn. “idan kin sallami yaron naki sai ki sallameni nima” yace yana nufar bedroom.

Shafo gashin kan Auwal tayi dake she’ki kamar na larabawa.

“Son jeka huta ko ina zuwa na baka labari” murmushi yayi tare da mi’kewa yace “to mamina, barci ma zanyi idan nai sallan la’asar”.

” A’a my son ba kyau barcin yamma ban yadda ba kuma kar ayi”.

“Kaji?” “tom first love bazan ba” ya fita daga d’akin.

‘Dakin sa ya nufa, bayan yayi alwallah yayi sallah sai ya d’an kishin gid’a yana kallon t.v, barcin yakeji “amma tunda mami ta hana ba zanyi ba” yace yana mai barin d’akin gaba d’aya.

‘Dakin mami ya shiga, wurin da take aje keys d’in mota yaje, duba nasa yayi bai gani ba.

Sai ya d’au na RAHAMA guda d’aya ya fito.

Koda yazo wurin motocin sai yaga duk sunyi ‘kura da alama dai ba’a anfani dasu tunda ya tafi, daga nasan har na RAHAMA.

Koma wa yayi ya d’ako na mami ya shiga, bata wuta yayi tare da danna uban horn tun kan yaje get d’in.

Da gudu mai gadi ya bud’e masa, fita gidan yayi.

Direct gidan wansa Sani yayi, horn yayi aka bud’e masa yayi ciki parking yayi tare da fita a motan yayi ciki.

Da sallama a bakin sa ya shiga parlour ansawa sukayi yayan har da Ikiliman.

Da gudu Iman ta nufo sa tana cewa “oyoyo uncle” cafe ta yayi tare da d’aga ta sama.

Yace “oyoyo my angle” dariya tayi, zama yayi tare da Iman d’in.

Ikilima tace “oyoyo mijin kwali” ta’be baki yayi tare da cewa “gayi nan a gaban ki, don nafi ‘karfin kwali nine na ‘karfen maza azo ayi tarba ta musamman ko kuma mutum ya koma gidan su”.

” Gida kuma? a’a ai mutu karaba nida kai, mai zakaci a kawo maka?”.

“Abinda mijin ki yaci”

“Babban magana to ya ‘kare” d’auke kansa yayi kamar magidanci yace “a kirka wani yanzu”.

” Wallahi baka isaba dan ubanka, haka kawai kasa matata aiki da yamman nan, sa Larai ta masa”.

Murmushi gefen baki yayi tare da cewa kamar gaske “oh yaya dama kana nan?” bai tanka masa ba ya ‘kara da cewa “ina wuni yaya” bai damu da ansa wan saba ya cigaba “mun same ku lafia?” nan ma shiru.

Dariya Ikilima ta fashe dashi tare da cewa “Allah shirye ka Auwal, mami ta gama ‘bataka wallahi. Antura ka ‘kauyen nan ko zakai hankali ne ashe dai akwai aiki”.

Murgud’a baki yayi kamar mace yace “‘kila da naki nake yawo”.

Bata barsa haka ba tace ” inaga kuma sa aure kawai idan ya fara tara yara zaiyi hankali “.

” Maza kuyi” yace yana mi’kewa.

Ganin zai fice tace dashi “dawo ‘kanin na dafa maka, banci mamina ta cika min ciki”.

“Daga nan sai inah” banza da ita yayi, Iman ta’ba ta fuska tare da cewa “momy don Allah Ku daina wa uncle haka” tana mai zum’buro baki ta bisa.

Har ya shiga mota ta ‘kariso, “uncle kayi ha’kuri kaji” murmushi yayi tare da janyo ta ya d’aura ta a cinyan sa.

“Da akayi me baby na?” turo baki tayi irin yadda yakeyi, domin yarinyan tana mugun kama dashi, idan kuka ga Akram bancin ‘karami ne zaka ce shine.

“Ba momy ta ‘bata maka rai ba?” .

“Ko d’aya my baby, muje gidan su Mufi, daga nan sai mu wuce duka gidan mami Ku kwana ko?”.

” Yeeeeeeeee, muje uncle ” dariya yayi tare da sata a kusa dashi ya tada motar suka bar gidan.

Zai shiga yayan zai fita ganin motar mami yasa Yusif tsayawa yana mamakin ganin mami bancin bai dad’e da barin gidan ba.

Ganin Auwal ne cikin motar yasa yayi tsaki tare da ficewa.

Dariya Auwal yayi tare da parking, shiga sukayi Iman ta fara kiran “Mufy” da ‘karfi, aiko sai ga Mufyn da gudu.

Akram a bayan ta, tafiya yake sak Auwal, sai dai shi miskiline na ‘karshe.

Zuwa yayi ya rungume Auwal tare da cewa a hankali “sannu da zuwa uncle”.

” Yauwa yaro na” haka itama Mufy tace.

“Ina Momyn ku?, tana sama” cewar Mufy.

“Okay Ku muje idan na gaida ta sai mu wuce gidan mami don yau gidan mami zaku kwana”.

Mufy ta saki eyhun murna, shiko Akram murmushi kawai yayi sam bai da hayaniya.

Suna hawa tana sakkowa, da murmushi tace ” uncle mai yara yaushe a gari?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button