KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Au mijin ki bai fad’a miki ba? ruwan shi d’azun, barka da zuwa na mami”.

” Muje kasha ruwa, Iman ina momy? “.

” Tana gida, ina wuni Anty” “lafia lau ta uncle”.
Fridge taje ta kawo musu abu mai sanyi, kur’ba kawai Auwal yayi ya mi’ke “mun tafi” cewar Mufy.

Kallon Auwal tayi ya d’auke kai sai tace “ina zaku yaran uncle da yamman nan?”.

” Gidan grandma okay ku gaishe ta ” suka bi bayan Auwal da ya fice da gudu.

Mami zaune ita da Dady a parlourn suka shigo, da gudu suka nufe kakannin nasu.

“Oyoyo, oyoyo amarena, oyoyo abokina” cewar Dady yana runguman su d’aya bayan d’aya.

“Da zabiya da bilaki, to Ku ‘kara gaba banan ba baza ku ta’ba kasuwa ba. Don na kere Ku babu abinda zaku rud’e sa dashi”.

” Can miki me zanyi da tsohon mijin ki? sai dai ko Iman” cewan sarkin tsiwa da rashin kunya Mufy.

“Iye mijin nawa ne tsoho?, uhum” tace tana turo baki.

“Auta mai kaka wo min rasai tamin a gida?”.

” Mami ni yarana duka masu kunya ne ko Mufy na?, eh uncle ” suka ce tare da tafawa.

Ta’be baki tayi tare da cewa “zamu had’u idan sun tafi”.

Dariya Dady yayi tare cewa “gumma ya kwaye muku ko yaro na yayi hankali, kinbi kin ‘bata min yaro”.

” Haka ma zaka ce ko?, to mezan ce dama idan ba gaskiya ba”.

Share shi tayi tare da cewa tana kallon Akram “miskili kai kenan kullm a haka, auta kukai yaron Ku asibiti da wuri fah tunkan abin yafi ‘karfin Ku”.

Ta’be baki yayi tare da mi’kewa ” ina zuwa my son?” hanyan steps ya nufa.

Sai da ya hau sannan yace “d’akin ka?” a hankali.

“Me zakyi?, kwanciya. Ka bari sai bayan isha babu kayu kwanciya magrib”.

Bai ce dashi komai ba sai dawo wa da yayi ya zauna nesa dasu.

              °°°°°°°°°°°°

Kwace madam Gloria ta dawo ta tadda ta sai faman rizga kuka take, da sauri uwan ta nufe ta.

‘Dago ta tayi tare da cewa cikin tsananin damuwa.

Share hawaye fuskan ta tayi tare da du’kar da kan ta ‘kasa.

Tatta’ba fuskan ta tayi tare da cewa cikin sanyin murya ” what happened? why are you crying?”.

Murmushi ya’ke tayi tare da cewa “nothing”.

” Ya zaki ce haka? bayan fuskan ki ya nuna kin dad’e kina kuka?”.

“Ina lura dake kwana kin nan kina cikin damuwa, wato kina ‘boye min damuwar ki ko?. Wakike da bayan ni? ashe ban cancanci sanin damuwar ki bako?”.

Kukan da take matsewa ne ta fashe dashi.

Ganin bata da ninyan barin kukan yasa uwan tace ” kenan ni zaki ‘boye wa wani abu? ba damuwa na bar ki” tace tare da mi’kewa.

Ri’ko hannun uwan tayi tana girgiza kai tare da cewa “a’a mama, nothing of that sorts”.

” To fad’a min ” cikin kuka nace “I’m in love with him” sai nai shiru tare da cigaba da kuka na.

Zaro ido mama tayi tare da cewa “who?”.

” Doctor…… doctor Auwal…. ” kallon ta tayi cikin mamaki, amma da ta tuno baya sai mamakin ya gushe.

Hasali ma mikin ta taji yana son tasowa, don haka cikin tsananin tausayi ‘yar tata tace “idan na fahim ta bai sani ba?” d’aga mata kai tayi.

Sauke numfashi tayi tare cewa “kisa same sa ki fad’a masa”.

” Ya tafi” nace ina mai sake fashe wa da kuka mai tsanani.

Cikin damuwa tace “ina ?, ban sani ba amma kaya da yawa yasa a taxi suka tafi”.

Shiru tayi na wani lokaci kafin tace ” to yanzu ya za’ai? ko ki manta dashi kawai, kinga soyayyar sa ma zaki rabu da ita ki huta, tunda bamu san inda yake ba”.

Hawayen idanun ne suka ‘kafe tare da cewa “I can’t, I cannot forget him or stop loving him. I love him mama” nace ina mai fashe wa da kuka.

Cikin tausayi ta tace tana mai ruruguma jin ta tana shafa mata baya alaman rarrashi “don’t cry joy. I am here for you”.

” Nasani mama, amma shifa ? bashi baya tare dani”.

“Kiyi ha’kuri ubangiji zai duba komai”………………

Comment
&
Share

‘Yar Aliyu ce✍????
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????

‘KAUYEN ‘YAR KADDE

????????????????????????????

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

????2⃣3⃣to2⃣4⃣

Hawaye idanuna ne suka ‘kafe tare da cewa “I can’t, I cannot forget him or stop loving him. I love him mama” nace ina mai fashewa da kuka. Cikin tausayi ta, tace tana mai rungume ta, tana shafa mata baya alaman rarrashi “don’t cry joy. I am here for you”, ” nasani mama, amma shifa? bashi tare dani, kiyi ha’kuri ubangiji zai duba komai kinji “.

Gyad’a kai kawai nayi tare da tsayar da kuka na, jin nayi shiru yasa mama ta d’ago da fuska na, share min hawaye tayi tana murmushi tare da cewa ” yauwa yarinyar kirki” had’e da jan min kuma tu.

Murmushin ya’ke kawai nayi, “kinci abinci kuwa?” Sai lokacin na tuna da cewa mama ta sani girki, shiru kawai nayi mata.

Sake tambayan ta tayi “nace kinci abinci?” turo baki nayi tare da cewa “a’a” ta sigan shagwa’ba.

“To mai yasa Joy?, ya tsina fuska nayi sannan nace ” ban girka ba” cikin ‘kasa da murya.

Ba tace komai ba sai mi’kewa da tayi, cikin gaggawa ta musu abinci mai sau’ki ta kawo min har gado.

Ansa nayi tare da mata murmushi nace “nagode momana” jan kuma tuna tayi tare da jifana da murmushi ita ma.

“Maza kici ki ‘koshi ‘ya guda, duk da ba wani cin kirki kike ba, shiyasa gaki nan kullum kaman one”.

Dariya na fashe dashi tare da cewa ” kai mama nine kamar one?, uhum maza ci ni ina zuwa” tace tana mi’kewa.

Wanko hannu na nayi a roban da ta d’ebomin ruwa domin haka na fara cin abinci na, duk loma d’aya sai na dad’e kafin na had’e.

Domin tunanin abin ‘kauna yayi min katutu, duk wani dariya da murmushi da nakeyi inayi ne kawai domin mahaifiya.

Don tafiyan Auwal yayi matu’kar tada hankali na, tuno irin kayan da naga anloda a motar kuwa na samin fad’uwar gaba mai tsanani.

Haka dai na daure naci kwatan abincin na tura gefe, lokacin ne mama ta dawo d’akin.

Kallon kwanon tayi sanan ta maido da idon ta kaina, tace cikin had’e rai “har kinme Joy?”.

Turo baki nayi tare da had’e fuska don banso ta matsaminci.

Nace ” na’koshi” girgiza kai kawai tayi tare da d’auke abincin ta fita dashi.

Zuwa tayi ta ‘kara wani akai don mama akwaici ta kamaci.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Auwal kuwa hankali kwance yake rayuwar sa, yama manta da wata yarinya wai ita Joy.

Kwana biyar da zuwan shi yayar sa ta dawo ‘kasar tamu, zo kuga murna wurin Auwal, yanda ku kasan yaron goye haka ya zama, ashe shagwa’ban da akewa mami kad’an ce.

Tsaraba ko yasha shi, kai kace don shi akayi tafiyan, a tsaraban harda na matan sa, cewar yayan tasa.

Dariya kawai mutanen palon suka kwashe dashi, wanda har sai da Ikilima ta kasa shiru tace “mutumin da bai da budurwa inashi ina zancen aure, kawai a bamu”.

Hararan wasa Rahma ta jefa mata tare da cewa ” ba sai kuzo ku danneni ba ku ‘kwace, ai tari zan dunga wa ‘kanina har zuwa lokacin da zuciyar mu zata zo. Bare ma jikina na bani ‘kanina ya fara soyayya”.

Sai a wannan lokacin ya tuno da wata aba Joy, duk da bawai ya manta da ita kwata -kwata bane, duk da hakan shine burin shi.

Amma ina can cikin ‘kar’kashin zuciyar sa itace ciki male-male.

Tuno ta da yayi ya haddasa masa ‘bacin rai sosai, domin har da mummunan ganin da yayi mata da Isah ya tuni.

Auwal mutum ne mai tsananin kishi, musamman akan abinda yake ‘kauna.

Girgiza san da RAHAMA tayi shine ya dawo dashi daga dogon tunanin da ya lula tare da kafe ta da idanuwan sa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button