KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi gefen baki nayi tare da cewa “sannu da dawo wa mama”.
” Yauwa Joy sannu da gida”, ban ansa ba ina kallon sa tage fen ido mama ta nuna masa inda muke aje kayan abincin mu ya aje.
“Sannu kaji? nagode fa, bari na kawo maka ruwa kasha, ko Joy kawo masa bari na duba cincin mu ya rage sai na bashi yau ya dawo yace, gashi bamu dafa abinci ba sai ya faraci kafin na d’aura yanzu”.
Kamar ba dani take ba, ko motsi banyi ba, don kamar maye haka ya kafeni da ido.
” Joy ba magana nake ba” mi’kewa nayi ba don naso ba nayi kitchen.
Cup mai kyau na d’ako tare da d’ebo ruwan randa na fito.
Ina zuwa na aje a gaban sa na wuce, lokacin ne mama ta fito da ba’kin leda a hannu ta.
“Joy ansa ki sayo masa zo’bo mai sanyi ya rage yunwa kafin na dafa abinci”
Kar’ba nayi tare da nufan hanya, shi kuma ta mi’ka masa cincin d’in. Ransa idan yayi ba’ki ya ‘baci, babban matsalan shi da Joy kenan shigan banza.
Kuma shine sulan ‘kwad’ayin wasu, ko yau da dama-dama.
Bin bayan ta yayi mama tace “kabari ta kawo yanzu zata dawo”.
Murmushi ya’ke yayi tare da cewa ” idan ta dawo na kar’ba” don Allah Allah yake yaje ya han ta tafiya.
“Auwal kenan kai wai har yanzu baka saki jiki damu ba, jeka to” murmushi ya sakeyi tare da rufa mata baya.
Koda ya fito da yake ba sauri gare taba ya tarar da ita tana gaf da gidan zo’bon, domin daga gidan su, gida uku ne sai na masu zo’bon.
“Joy” ya ‘kwala mata kira, wai gowa tayi don jin muryan sa, fuska d’aure ya kauda kansa ganin ta juyo.
Tsaye take daga inda take tana kallon sa, ita ba tai gaba ba, ita ba tai baya ba.
Ido kawai ta zuba masa, jin shiru bata dawo ba kuma tasan sa rai kiran ta na nufin ta dawo ne .
Sai ya wai go don ganin tsayuwan da take kuma gashi gaba da gidan da take tsaye majalisan maza ne.
Wani sa’in harda d’an iskan saurayin ta (Isah), ya tofar da yamu tare da tsaki.
Kallon sa kawai take, ganin zai waigo yasa na kauda kai na tare da d’aga kai don cigaba da tafiya.
Cikin jin haushi yace “dawo bansha” yadda zataji, “to ai bakai ka aikeni ba bare ka hanani tafiya” nace a zuciya ta tare da cigaba da tafiya ta bako wai waye.
Cije le’be yayi tare da girgiza kai, ransa ba’kin ‘kirin, yana hangen yadda samarin ‘kyauye suka kafe ta da ido.
Wani har da hanci wurin kallon.
Shige wa gida yayi don ba’kin ciki tare da buga ‘kofa garau.
Zama yayi a fararen kujerun sa na far fada, tare da jingina ya rintse ido, tuno ranan da yayi mummunan ganin yayi.
Dafe zuciyar sa yayi saboda yadda take mugun bugawa.
•••••••••••••
“Mama gashi” cewar Joy a bakin kitchen, waigo wa mama tayi tare da cewa “baki gansa waje ba?, uhum” kawai nace.
“To taimaka ki mi’ka masa a gida, nasan yana nan”.
” To” nace tare da fita gidan, koda naje ‘kofar gidan nasa na dad’e ina tunanin yadda zan shiga.
Kudum bala nayi na daure na tura ‘kofar gaba na na fad’i.
Shiga nayi na gansa zaune idanun sa a rufe, jin motsin tafiya yasa ya bud’e idanun sa dasu kai jajazur dasu.
Ganin itane yasa ya maida ido ya rufe, zuwa gaban sa nayi na aje zan juya ba tare da nace dashi komai ba.
Yace “d’auki” kallon sa nayi still idon sa na rufe, juyawa nayi don tafiya ta.
“Nace ki d’auka ko?” cikin tsawa, niko taurin kai sai nai kamar banji sa ba nasa kai.
Banyi taku uku ba naji an ri’ko hannu na, waigo wa nayi ya wurgamin wata matsiyaciyan harara tare da sakin min hannu nawa, yayi min nuni da zo’bon da na aje.
Tura baki nayi ina cewa “mama tace na kawo ni, amma kafin ki sayo mai na sanar miki?”.
Ya tsina fuska nayi sa’an nan nace kamar mai ciwon baki ” gani nayi ai bakai ka aiken ba” tare da zum’bura baki.
“To sai ki d’auka kisha, don ni banshan ‘kazan ta” kallon sa nayi shima ya d’ago daradaran idanuna sa.
“Eh, yadda kikajin nan” “ummm, hakan yayi” nace tare da matsawa na d’au zo’bon zan wuce.
“Shanye shi anan ” yace fuska a d’aure kamar wanda bai ta’ba dariya ba.
Tsoro ne ya kamani na kafa kai bayan na bud’e goran .
Bige goran yayi ya zube min a jiki, sanyin zo’bon har cikin kaina.
Kallon sa nayi shima ni yake kallo, fuska babu walwala yake “duk ranan da na sake ganin ki da irin wad’an nan tsuma ko makaman tansu, tabbas rai zai mummunan ‘baci”.
” Fita min a gida” yace cikin tsawa daya firgitani, da gudu na fita.
“Sai yanzu naji sa’ki a zuciya ta, na fanshe haushi na” yace tare da shige wa d’aki, alwallah ya gaba tar don anfara kiran sallan magariba, ya fito don tafiya massalaci.
•••••••••••••
“Mugu kawai” nace lokacin da na shigo gida, “kada wa Joy?” cewar mama daga kitchen.
“Ba kowa” nace tare da nufan d’aki ina jin ta tana cewa “kin zama mahaukaciya ba ai dole” bance komai ba na bud’e gana mazgo na don canza kayan jikina.
Kallon kayan nayi ina tunanin maganan sa, don gaskiya na tsora ta sosai.
Ganin haka bai min ba na zazzage kayan ciki kaf a tsakar d’akin.
Da ‘kar na samu wani dogon riga mai gajeran hannu ya wuce guwa nasa ina mai cewa “ka nunan kayan da zam saka tunda kasayo min” ina mai murgud’a baki kamar yana gaba na.
°°°°°°°°°°°°
Shiru- shiru har 9:30pm mama bata gansa ba, don haka tace “tashi ki kaima doctor abincin nan”.
Zabura nayi tare da cewa ” Allah mama bazani ba, doctor d’in nan fiti nan nene” zata sake magana sai ga Aisha ta shigo.
“Yauwa tunda ban isa da d’ayan ba nasan wannan baza ta’ki ba” ya tsina hanci nayi tare da ta’be baki.
Dariya Aisha tayi tare da cewa “waya ta’ba min besty? eyeh? mai mukayi ne mama” duk cikin tsokaana tayi.
Hararan ta nayi tare da gyara kwanciya ta.
“Uhum mama bani sa’kon mai zan miki kiga cika aiki yanzu tunda wata bata son albarka”.
Tsaki nayi mama tace ” ma’kocin ku likitan nan zaki mi’kawa abinci”.
“Aiko yanzu na barsa waje yana shan iska, yauwa kai mai” mama tace tana mi’ka mata.
‘Kar’ba tayi ta fita, bata jima ba ta dawo ko nace suka shigo tare hannu ta d’auke da kwanon abinci.
Waiga dukan mu mukayi kallon d’aya na masa na d’auke kai da sauri saboda hararan da yayi min.
Duk da dare ne akwai farin wata kamar rana.
Turo baki nayi, “Auwal ya haka?” lokacin da Aisha ta aje abincin.
Murmushi yayi tare da cewa “nagode mama naci abinci ko?” yace yana zama kusa dani kad’an.
Cikin ‘kasa da murya yadda babu wanda zaiji yace “bakijin magana ko?” kallon su mama nayi naga hakalin ta naga abincin da aka aje Aisha cema naga tana kallo na.
“Bani da wasu sai irin su” nace a hankali, zaiyi magana mama tace “yanzu ka kyauta?, haka mukayi da kai?”.
” Ayi ha’kuri gobe zanci” yace yana murmushi kad’an, “to nayi”.
Fira suka d’an ta’ba da mama ya tashi yayi mata sai da safe ya fita, ba tare da ya kalleni ko ya sake kulani ba.
Kamar ma baiji mai nace ba..
Washe gari ina cikin barci safen da na saba, naji muryan sa yana ce da mama ” mama yanzu naga waccen yarinyan da suke tafiya makaranta da Joy ta tafi, nace lafia bata tafi ba, ko ta riga ta gaba ne?”.
“Wai Joy ai tayi kwana biyu bata zuwa, nayi nayi ta’ki, kuma ko jiya bayan kafita maganan makaranta yarinyan tazo mata, amma fir tace baza taba, ko naji tana ce da ita next week zata”.
” To mai yasa?, oho gata can bata da sana’a kullum sai barci, don ko church yanzu taba tafiya, nai magana har bakina yayi tsini amma ta’ki haka ma zuba mata ido”.
Inajin su sukai ta magana, har takai ga yace mama ta tasoni, zuwa ko tayi tashi na d’in nayi kamar ina barci.