KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Kiran suna na ta fara, da yake ban cika nauyin barci ba da safe, nafi barci harda minshari da dare, don saboda tsaban barci kana iya saceni ka gudu.

Tayi kira yakai uku na’ki ko motsi, sai ta fara jijjigani amma ko didim.

Auwal na tsaye yanaji gashi ya tsaida Aisha a waje .

Don haka sai ya shigo d’akin kawai yana cewa “mama bani ruwan sanyi kawai” bata musa ba kuwa tace “to tare da shiga bangi da don d’ako masa.

Bata jima ba ta kawo, jin tace ” gashi” yasa na mi’ke a zabure, ina zare ido fuska ta a had’e.

Dariya mama tayi tare da cewa “dama ai nasan kinaji na, dakin cigaba da ‘kaliya ai dakin ga aiki”.

Turo baki nayi tare da zuro ‘kafafuna a ‘kasa, shiko kamar wani ubana yana wani kauda kai ya had’e rai yace ” tashi kisa uniform mu tafi” kallon sa nayi tare da hararan sa.

Zuwa can nace “ai nayi latti , sai kuma gobe”.

” Baki isaba tashi kisaka uniform nace” “uhum banyi wanka bani, ba’a bu’kata wuce ni kina ‘batan lokaci” yace tare da barin d’akin.

Yana daga waje yace “ina jira minti biyar na baki, kika wuce rai ya ‘baci”.

” Kiji fa mam, sai kace wani ubana, to wai meye ruwan shi dani”.

Bugen baki mama tayi tare da cewa “karki shirya ki tsaya yau naga duka” daga haka ta fita itama………

Comment & share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????

‘KAUYEN ‘YAR KADDE

????????????????????????????

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO

Dedicated to Safiyya A W fan’s club, kuna bani nishad’i godiya mai tarin yawa

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

????2⃣9⃣to3⃣0⃣

Bayi na shiga, wanka ta nayi sannan na fito, koda na fito ganin kayan makaranta na da school bag d’ina a gefen katifa da kayan shafa, nasan duk aikin mama ne.

Janyo kayan shafan nayi ina hararan uniform d’in kamar shine ya min laifi, shafa mai nayi kawai na d’au kayan na saka, fuka babu komai na fito, tunda na fito ya kafeni da ido.

Kauda kaina nayi daga gare sa tare da tsaki a zuciya ta, nufan hanya fita nayi ba tare da na kula mama koshi ba.

“Baki sallame taba”, kamar ba dani yake ba na ‘kara gaba.

Girgiza kai kawai yayi mama tayi murmushi tare da cewa ” nagode yaro na, ubangiji ya taimake ka” “ameen” yace tare da bin bayan na.

Ina fito wa naga Aisha tsaye, muna had’a ido na d’auke kai na.

Cikin masifa ta nufo ni, tana cewa “ai da baki fito ba, da ya barki, kinje kin shanya mutane, kuma muje yau sai kinsha duka biyu, gana rashin zuwa gana latti”.

Kamar ba dani take ba na nufi hanya, lokacin ne ya fito motar sa ya bud’e, yana mai cewa Aisha ” shiga muje na kai ku” da farin ciki ta nufi motan.

Ina jin su ban ko waigo ba, tana shiga ya tada motan.

Ya fara tafiya a hankali, don garin namu hawa da sauka ne, ga wasu shegun duwatsu, har da uban ramu ka, gomnati ta’ki kawo tallafi. Koda yazo dai-dai inda nake sai ya tsaya ba tare da yayi magana ba.

Ganin haka na bud’e bayan motan na shiga tunda Aisha na gaba.

Ajiyan zuciya ya saki tare da lumshe idanun sa na wani lokaci, kafin ya nisa ya bud’e a hankali ya sauke su akan fuska ta.

Ta madubin motan, wani irin nishad’i naji yana tsarga ‘kashi da ‘bargo na, shima ta ‘barayin sa hakan ne.

Aisha ko washe baki take ta shiga motan da bata ta’ba shiga ba.

Fara tafiya yayi, a hankali yake tu’kin mota shiru kamar kurmaye, sai aukin kallo kamar zai cinyeni.

A haka har muka fito bakin titin shiga cikin gari, yana ganin sa a kwanlta yace yana mai kallon gefen da Aisha take “inane hanyan makaranta?” .

“Nan hanyan zaka bi” ta nuna masa gefen dama, daga nan ne ya fara tu’ki cikin kwarewa, da taimakon Aisha ya kawo mu makaranta .

Yana parking muka fita, kiran Aisha yayi don yaga sai faman had’e rai nake tunda muka fito.

Dawo wa tayi tare da le’ka kanta ta gilas d’in motan, kud’i ya mi’ka mata yace “kuyi break” godiya tayi masa sa’anan ta biyo bayan na da nake ta tafiya ta ba tare da na jira ta kona waigo ba.

Yana kallon na har na shiga class sa’anan ya bar wurin cike da tsanani ‘kauna ta.

“Wai besty yau Allah ya d’aga mu, kuma Allah ya cece mu, da yanzu muna can hanya muna cin kwakwa, amma gaskiya yana da kirki, kalli kud’in da ya bamu, da har inajin haushin tsaida ni da yayi”, kallo d’aya nayi na d’auke kai na, ” ga naki, banso” nace.

” Kai amma guy d’in nan ya had’u, idanun sa farare ‘kar dasu, gashin giran sa masu tsanani kyau da tsari, inama inama besty ohhhhhh Allah na” tace tana rugune hannun ta a ‘kirjin ta

Esha ke cewa bayan mun zauna, zancen ta na sufan tamin habibi yayi ba’in ‘bata min rai amma ban nuna ba nabar abin a raina yana cin raina, bamu dad’e da zuwa ba aka fara tsaron latt, malami ya shigo muka fara karatu.


Muna fito wa daga cikin makaranta muna tafe Aisha sai zuba take ita d’aya kamar kad’anya .

Bamu lura dashi ba sam, sai jinsa nayi dai-dai saitin kunni na yace “ku nake jira” cikin daddad’an muryan sa.

Bugawa zuciya ta tayi, na d’an juya kad’an na gansa gab dani, yana cikin kyakkyawan shiga, Aisha dajin muryan sa ta washe baki tare da cewa “sannu da zuwa yaya”.

” Kutumar uban can” nace a zuciya ta, murmushi yayi mata tare da cewa “yauwa ‘kanwa ta, kun tashi lafia? ya karatu dai?”.

“Lafia qalu, alhamdulillah” “masha Allah, muje ko?” yace yana mai nuna mana inda motar sa take.

Tare muka jera yana ta gefen hagu na, koda muka zo shiga motan bayan ya bud’e .

Zan shiga baya kamar yadda nazo da farko ya daka tar dani, tsayawa nayi ina kallon sa har iso gareni.

“‘Kanwa ta koma baya” yace da Aisha data hakince a gaba.

“To” tace tare da fita ta koma baya, “shiga” yace yana tsaye tare da kallo na, ban ce komai ba na shiga ya rufe ‘kofar tare da zaga yawa ma zaunin shi na drive ya shiga muka d’au hanya.

Kamar tafiyan farko haka mukayi wannan ma.

Bai tsaya a ko ina ba sai ‘kofar gidan mu, bud’e ‘kofar motan mukayi a tare kowa ya fita.

Aisha na cewa “mungode yaya, Allah ya saka”, ” ameen” yace yana murmushi idon sa na kaina da nake ninyan shiga gida ba tare da na waigo ba.

“Tsaya ‘kanwata ki kar’ba” bud’e but d’in motan yayi tare da ciro ledan shopping ya mi’ka mata.

Godiya tayi tana kallon sa cike da sha’awa a zuciyar ta tana raya “ashe yana da kirki?” tayi gida tana waigen sa.

Shiru yayi bayan shige wansu yana sosa kai da key d’in hannun sa.

Kallon kayan dake dam motar yayi, yana na zarin yadda zai kwashe su.

Ganin babu mafita yasa ya fara fidda kayan yana ajewa a zauren gidan, yana cikinyi ‘kanin Aisha ya fito, kiran sa yayi tare da mi’ka masa wani leda yace “shiga min dashi kaji aboki?”.

” To” yace ya shiga gidan su Joy dashi ya mara masa baya, Joy ne zaune tsakar gidan lokacin da ya shigo zaune da d’aurin ‘kirji ga bokiti a gaban ta tana ta faman ya tsina fuska.

“Sannu da dawo wa Anty Joy” Muhusin yace, d’ago da kai tayi tana kallon sa tare da cewa “yauwa yaro kirki”.

Aje kayan kusa da ita Auwal yayi shima Muhusin yayi hakan.

Haka Auwal ya kwaso kayan nan tasa tana zaune yana shigo wa dashi ba tace dashi ci kanka ba.

Duk da taso cewa wani abu, bakin tane yayi nauyi shiyya sa.

Sai da ya shigo dana ‘karshe ya sallami Muhusin tare da zama kusa da ita.

Kallon sa tayi da mamaki domin wurin da ‘kura amma ba tace komai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button