KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Jan nufashi yayi murya can ‘kasa yace ” Joy” ido kawai ta tsira masa.
“Ina son ki” sai yayi shiru, murmushi ne ya su’buce min a take, kallo na yayi shima ya saki murmushi tare da kauda kai yace “alhamdulillah, don alamu sunnuna itama tana son sa”.
Cigaba da cewa yayi ” ina tsanani ‘kaunar ki, kuma ina da kishi mai tsanani akan ki, ga kaya nan don Allah kirin’ka sawa kibar sa wad’an kike sawa don zuciya ta na ‘kuna duk lokacin da nagan ki dasu”.
“Duk da nasan addinin mu ba d’aya ba, amma zuciya ta tafi na’am da kayan mu, ki daure ki saka su”.
Juyo wa yayi gaba d’aya yana kallon ta, yace ” kina sona?” babu kunya na d’aga masa kai ina murmushi.
Farin ciki na ya’ki ‘boyu, kallon na yake cike da ‘kauna .
“Har da irin wannan zaman a dai na please” yace yana nuna d’aurin ‘kiri dake jikin ta.
Rufe fuska tayi tare da cewa “wanka zanyi shiyya sa” a hankali.
“Zaman me kike to baki shiga bayin ba?” shagwa’be fuska tayi tare da cewa “na gaji ne shiyya sa” dariya yayi tare da mamakin ta.
Kafeshi da ido tayi kamar zata lasheshi, “kallon fa?” yace yana mai gintse dariyan sa .
“Kafi kyau idan kana dariya, Allah ko?” yace yana ‘kale mata ido d’aya.
Kallon a gogon hannun sa yayi tare da cewa “muje na miki ankusa kiran sallah” zaro ido tayi tare da cewa “a’a, na yafe, hmmm, shikenan ai aukau lokacin da ko kince bazan bari ba. Mama fah?, tana barci” tace tana kallon cikin idanu wansa.
“Ta kyau ta, ki dai na kallo na haka idan ba haka ba akwai babban matsala” dariya nayi tare da cewa “tom, bari naje nayi wankan Allah har da yunwa nakeji, nima haka” yace yana shafo cikin sa.
Cikin tausayawa tace “bari na kawo maka kaci” tace tana mi’kewa, yamu ya had’iye kut tare da kauda kai da sauri.
Bata ‘bata lokaci ba ta dawo hannun ta d’auke da tire, dire wa tayi a gaban sa tare da zama.
Bud’e kwanon tayi, shinkafa ne da miya, gaskiya bazai iya cin wannan shinka fan ba.
Don haka sai yace “kici kawai bari naje masallaci” ‘bata fuska tayi ba shiri ya fasa mi’kewa.
Tura masa kwanon tayi gaban sa, kallon ta yayi ta masa nuni da yaci.
“Bani to” yace yana bud’e baki, kallon tsabtataccen bakin sa tayi, yayi matu’kar burge ta.
Babu damuwan komai ta saka cokali ta d’ebo ta nufi bakin sa dashi.
Ta bashi kusan sau biyar aka kira salla, don haka ya dakatar da ita.
“Maza kiyi wanka kafin na dawo mu cigaba da fita” yace yana gab da fita.
“Oho har da abinci kici kinji?” d’aga kai nayi ina mai jefan sa murmushi, shima ya mayar mini.
Comment & share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????
‘KAUYEN ‘YAR KADDE
????????????????????????????
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO
Tell my mistake to me, not to others. Because my mistakes are to be corrected by me, not by others.
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
????3⃣1⃣to3⃣2⃣
Bayan fitan sa na kwashe kayan da ya sayo min na kai d’aki na aje na fito, dawo wa nayi inda na tshi na zauna, wani irin farin ciki naji yana mamayeni, kasa tashi nayi daga wurin har na tsawon wani lokaci, ina nan zaune sai faman murmushi nake Aisha ta shigo, kallo na take tunda ta shigo, nayi nisa bansan ta shigo ba.
“Besty! Besty!! Besty!!!” sau uku duk banji taba, gashi sai faman murmushi nake ina karkad’a kai.
Jin kiran sunana da tai tayi shine ya farkar da mama, fito wa tayi tana cewa “kun dawo yaushe Aisha?” .
“Tun d’azu, mama anya ‘kwa’kwalwar besty lafia yake kuwa?” dariya mama tayi kad’an tare da cewa “mai kika gani?”.
” Matso kiga mama, wallahi tunda na shigo take a haka, kuma nakira sunan ta bata san inayi ba”.
“Joy” mama ta kira ta da ‘karfi, firgit na dawo daga duniya ta nida hubby na, kallon Aisha nayi dake gaba na.
Murmushi da tunda nake da ita bata ta’ba ganin nayi wa wani ba bare ita taga na mata.
“Besty wannan fara’an fah? da murmushi fah?” rungume ta nayi ina ta faman sakin murmushi.
“Shafa min mana besty mai muka samu bayan dawo war mu?”.
” Am very happy today my ‘kawa” nace ina kallon ta, itama ni take kallo fuska ta d’auke da murmushi.
“Really?” d’aga mata kai nayi tare da sake rungume ta, mama na tsaye tana ganin ikon Allah.
“Burina, farin ciki na, rauwata, anashuwa na, walwala na” sai nayi shiru.
“Uhum, ina sauraron ki fad’a min na tayaki murna sosai” cewar Aisha.
Lumshe ido nayi na bud’e su, basu sauka a ko ina ba sai a kan kyakkyawan fuskan sa da shigo wansa kenan, ya dawo daga masallaci ko gida bai shiga ba yazo yaga ko tayi wanka taci abinci.
‘Kayataccen murmushi na masa, ‘bata fuska yayi tare da harara na.
Fuuu naji gaba na ya fad’i, ido na zuba masa shiko ya d’auke kai.
“Shigo mana doctor” cewar mama, murmushi yayi mata tare da ‘kari sowa ciki yana cewa “sannu da gida mama, nazo kina ta barci”.
” Hmmm, kai dai bari wallahi jin jikina nayi duk a gajiye bayan na gama girki shiyasa na kwanta na huta har basan su Joy sun dawo ba ” tace .
Kallon sa nake har yazo ya wuceni ko kallo na baiyi ba.
Shagwa’be fuska nayi tare da shashsha’ka, kamar zanyi kuka.
“Lafia ke kuma?” cewar mama, “ai ba lafia yau mama inaga sai yaya na ya duba ta dai, jifa yanzu take fara’a da farin ciki, amma lokaci d’aya ta canja” cewar Aisha.
Hararan ta nayi tare da turo baki ina waigo wa, had’a ido mukayi ya kauda kai.
Cikin shagwa’ba nace “bashi bane” nace ina le’ka fuskan sa da ya juya dashi gefe.
“Wake nan?” inji mama, jin haka yasa ya waigo mi’kewa nayi tare da cewa “ba gashi a gaban ki nan ba”.
Zaro fararen idanuwan sa yayi yana kallo na, murmushi na sakin masa tare da ‘kale ido nayi cikin d’aki.
” Ban son sharri daga shigo war sa, zaki wani ‘bata rai kice shi” cewar mama “aiko dai, mai yaya na zai miki? muna zaune muna gani ya shigo ko kallon ki baiyi ba, dama besty kin iya sharri ban sani ba?”.
Jin bai ce komai ba yasa na fito, tsayawa nayi akan sa, lokacin mama ta nufi kitchen, kallon sa nayi tare da cewa ” ka rantse baka kalleni ba daka shigo, kuma ka rantse sharri nake maka baka min komai ba “.
Kamar ba dashi nake ba yayi banza dani, bubbuga ‘kafa na farayi a ‘kasa da fara shashsha’ka.
Kallo na yayi tare da mi’kewa yace a hankali yadda Aisha baza taji ba ” wallahi nafi ki iya rashin kunya, a gaban mama kikewa saurayi shagwa’ba?, to Allah zan kunya taki”.
Turo baki nayi tare da cewa “to bakai kaja ba to” “niko?” yace yana matsowa kusa dani.
“Uhum, lallai wannan shine a dake ka a hanaka kuka, mai nace miki fisabilillahi kafin na tafi masallaci?”.
” Wanak da cin abinci” nace ina turo baki, kallon bakin yayi tare da runtse ido had’e da cije le’be.
Yace cikin wani yanayi “to mai yasa baki ba?” far nayi da ido, wanda saura kad’an ya fad’i yayi maza ya dafa bango tare da cewa a cikin zuciyar sa “yarinyan nan zata kashe ni idan banyi wasa ba”.
Matsowa nayi gaban sa, dai-dai nan mama ta fito hannun ta ri’ke da abinci.
Ganin zan ta’ba sa yayi maza ya kauce, ban ha’kura ba na sake matsoshi ina mai cewa cikin damuwan da na shiga take ganin zai fad’i “maike damun ka?”.
Kafin ya bani ansa mama tace ” wani abu ya same shi ne?” tana mai aje abinci a kusa da kujeran da ya tashi.
Turo baki nayi cike da shagwa’ba zanyi magana yayi saurin cewa “ba komai mama”.