KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani irin kallo na masa, yayi saurin d’auke kai a zuciyar sa yana cewa “bazan iya kasance wa kusa dake ba, musamman idan mu kad’ai ne, idan ba haka ba sai nayi sa’bon Allah, yanzu dama haka yarinyan nan take kana ganin ta shiru-shiru?”.

” Ga abinci ka doctor ” murmushi yayi tare da cewa “naci ai mama d’azu kina barci”.

” Kai my…………..” da sauri ya kallo ni, gar gad’i yayi min, Allah saura kad’an nayi dariya na gintse, ko meye tsoron sa oho.

Don haka na murmusa tare da cewa “mama ina sabulu wanka yake? na duba kwando bashi inda kike ajewa kuma ban gani ba”.

Kafin ta bani ansa sai da tace da doctor ” ka ‘kara to” bai son mata gaddama yace “to” tare da bismillah ya fara ci.

“Wai wanka zakiyi ne?” cewar Aisha, “uhum” nace da ita ido na nakan doctor da yafara cin abinci.

“Kafin ki shiga bani littafin Husna da kika ara zan duba wani abu, to” nace da ita tare da shiga d’aki na d’ako na bata.

“Yauwa bari naje kiga, mama sai anjima, yaya sai anjima” tare suka ansa shida mama.

Ido na nakan doctor da ya d’ago yana kallo na yana min magana da ido, wai naje nai wanka nazo muci.

Tura baki nayi tare da cewa “mama sabulun” “sabulun nan sai dai kisiyo” tace tana shiga d’aki.

Kafin ta d’ako kud’in na zana kusa dashi har guwana na ta’ba nasa, da yake mama ta shinfid’a masa tabar ma.

Runtse ido yayi tare da cewa “meye haka?, mai nayi” nace ina dube dube.

“Ansa kisiyo” na kar’bi kud’in tare da mi’kewa, tara tafiya nayi bai ninyan magana ba yace “amm…….” sai kuma yayi shiru, waigo wa nayi tare da cewa “kana magana ne? duba kayan nan akwai” daga haka ya gintse bakin sa.

Yana mamakin ta sosai, yace a zuciyar sa “yanzu ba don nace ba da haka zata fita duk mazan garin nan su gama gane min ita” tsaki yayi tare da cewa “musulunci yayi gaskiya”.

Kallon mu mama tayi duka, tana mamakin sauyin da ta gani a tare damu duka, amma taje baki tayi shiru.

‘Daki naje na bud’e kayan d’aya bayan d’aya ina mamaki da alajabi, har naga wanda sabulun wankan yake ciki.

Wani irin sonsa da ‘kaunar sa naji ya ‘kara nunkuwa a zuciya ta.

Gaskiya Auwal ya kashe kud’i, ya narke kud’i kamar bai so.

Cikin sanyin jiki na mai da kayan sannan na mi’ke.

Suna zaune da mama na fito, suna d’an ta’ba fira, ya bar macin abinci.

Kallon sa nayi koya waigo, wuce wa nayi na d’ebi ruwan zanyi bayin tsakar gidan.

“Mama yanzu ruwan sanyi zatayi wanka dashi?” daga ni har mama juyo wa mukayi muna kallon sa.

Ganin kallon da mama take masa yasa ya kauda kai yanajin kunya.

Murmushi mama tayi tana kallo na, nima kallon ta nayi tare da d’age mata gira ina murmushi.

Numfasa wa tayi da fara’a a fuskan ta tace “gata nan dai hanata yau ‘kila ta bari, don naga tana ganin ka da gashi”.

” Tafi shekaru uku tana wanka da ruwan sanyi” zaro ido yayi yana kallo na, “wuce ki dafa ruwa sai kiyi wanka” yace yana d’aure fuska.

“Inama da ruwan d’umi a kitchen d’in” cewar mama, ban musa ba na dawo nayi kitchen.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*

Washe gari tun da asuba na tashi kai kace sallah zatai nace da ita, kallo na tayi tare da cewa “sorry Mrs ba addinin mu d’aya ba bare kiyi tunanin haka, saboda son ganin masoyi na yasa na tashi da wuri, don yau basai antasheni ba” Dariya nayi tare da cewa “a’a kinji ‘kawan kwanta ruwan sanyi na jira” murgud’amin baki tayi tare da cewa “aniyanki ta biki, don yau na tabbata ko makaranta nace ba zani ba babu abinda zai min, ban cin karki ce nai rashin kunya da nagaya miki yadda zai tasheni ko ban tashi ba. Oh da gaske?” d’an kai tayi kawai tare da cigaba da sabgan gaban ta.

Don sai a wannan lokacin ne take bitan abinda aka koya musu a makaranta.

6:30am ta gama wanka tsaf ta shirya, wanda ganin ta shirya yasa mama koma wa barci bayan ta aje mata break fast.

Koda na gama shirya wa banko tashe taba na fito gidan a bina, tsaye nake a bakin zauren gidan mu ina kallon yanayin anguwan namu tsit kamar ba mutane.

Ko na abin mamaki bane, idan nai la’akari dako ‘karfe nawa ne yanzu.

Murmushi na saki ina kallon gidan su besty da yake a rufe, alaman basu bud’e ba.

Kallon na sahibi nayi naga shima a rufe, ga motar sa a gefe.

Nufan ‘kofar gidan nayi, tura wa nayi naga ‘kofar ta bud’e, murmushi na saki tare da shiga ciki.

Komai tsaf kamar yadda yake haka komai na gidan yake a tsabtace a gyare.

Ga inji a kunne daga gefe kanajin karatun Qur’ani na tashi.

Zuwa nayi ‘kofar palon, itama a bud’e take, nayi mamaki matu’ka .

“Bai tunani azo a sace masa?” nace a zuciya ta, shiga nayi babu kowa a palon, nufan bedroom d’in sa nayi, ina zuwa d’aga labule nayi, hango mutum nayi kwance a lullu’be akan gado.

Girgiza kai nayi tare da aje jaka ta akan sofa na nufi katifan ina dariyan abinda zan mai.

Ina zuwa nai tsalle na fad’a kansa, “innalillahi” yace tare da fara bud’e idonun sa, ai bai san sanda ya bud’e suba gaba d’aya yana kallon agogon bangon dake d’akin.

Mai da idonun sa yayi kai na tare da harara ta, niko na fashe da dariya, muskutawa yayi tare da cewa “d’aga ni, wai ma meye na zuwa tashi na da sassafen nan?”.

Turo baki na nayi dake gaf da nasa ina kallon cikin ‘kayan idanuna sa, nace ” makaranta zaka kaini”.

Kauda fuskan sa yayi don yaga kamar tana ninyan had’e bakin su yace “makaranta ne da uwar safen nan?, uhum, gari fa ko gama haske baiyi ba, ba ina ganin yadda kuke tafiya ba?”.

” To naji, nazo na ganka ne” “hmmm, d’agani tom” ‘kin d’aga san nayi, don haka sai ya fido hannun sa daga cikin abin rufan yace cikin lallashi “d’aga ni Queen d’ina kinji” ma’ke ka fad’a nayi.

Shiru yayi yana kallon yadda ta had’a fuska, “Allah barci bai isheni ba, jiya kin kanai nayeni kin hanani moruwa, ko asibiti fa banje ba”.

“‘Dagani kinji baby na” sauka nayi tare da kwanciya a gefen sa “oh Allah” yace yana runtse ido.

“Tashi kijirani a Palo yanzu zan fito, a’a muyi barci kawai” nace ina mai d’aura hannun na a jikin sa.

“Barcin ya tafi kuma ai, jeki yanzu zanzo” ma’ke kafad’a nayi tare da rufe ido kamar zanyi barci.

Rasa yadda zaiyi yayi, don haka sai shima ya rude ido, domin har ga Allah bai son kusancin nan nasu haka, don komai na iya faruwa, ‘karin dad’i daga shi sai guntulallen wando.

Jin shiru yasa na d’ago tare da cewa “ka koma barcin ne?, a’a, ai na gaya miki ya tafi, kije palo kijiran nayi wanka mutafi, kin maci abinci kuwa?”.

” A’a, mai yasa to?” yace yana mai bud’e ido, “tare nake son muci”.

” To jeki kitchen kima kafin na fito wanka” mi’kewa nayi tare da fita a d’akin.

Ri’ke kai yayi tare da cewa “zan sha aiki” ya mi’ke bayan ya yaye bargon……………..

Comments nake da bu’kata, idan ba haka ba sai bayan sati biyu????

Luv you all my fan’s❤❤
[11/5, 9:53 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????

‘KAUYEN ‘YAR KADDE

????????????????????????????

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

????3⃣3⃣➡3⃣4⃣

Jallabiya ya nema ya saka, ya saka kenan ta dawo cikin d’akin kallon ta yayi kamar yadda itama idon ta ke kan nasa, d’aga kai yayi alaman ya akayi ne, sai da ta ‘kariso ciki gab dashi sannan tace “ina kitchen d’in yake?” kallon ta yayi tare da cewa “kai Habibaty, kitchen d’in ne baki gani ba?, uhm,” nace ina kallon sa, don gaskiya bana gaji da kallon hasken idaniya ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button