KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganin suna mata dariya sai ta fashe da kuka harda birgima.

Ba shiri suka gintse bakin su, mami ta tashi tayi d’akin ta tare da iman.

Itama ikilima ta biyo su tana cewa “” baruwa na mami ni banma autan ki komai ba, oho dai kwaji dashi daga ke har munafikin mijin ki “”.

“” Kai mami ni d’in ne munafiki? eh kai ko bakai ne kaja za’a turamin auta sauro ya kashe min shiba?”” Shiru yayi yana Sosa kai.

“” Kaban ansa mana”” tace tana mai zama akan sofa dake ciki d’akin nata.

Ya’ki bata ansa domin yasan bai dai gaskiya sai ma wayan cewa yayi da cewa “” bari na wuce office idan nataso zanzo d’aukan su, oho maka kuma ta Allah bata mutum ba insha Allah babu abinda zai samamin yaro, kuma mutum yasani nan gani nan bari ehey mutum ya fita harkan yarona, ‘kwarai ma kuwa mami na”” yace yana mai shigowa d’akin.

“” Ga sojan ki can na hango sa yana parking motar sa, shima karki raga masa mamina kija masa kunni, harda shi bakin su d’aya Sam basu so suganni kusa dake sai sukama cewa wai bana abinda ya dace, kome nakeyi mara Kyau oho musu”” ya’karisa yana turo baki.

Dariya iman tayi tana cewa “” uncle kabar yin shagwa’ba kaga ka girma idan ba haka ba ko ‘kawayena suka ga kana haka dariya zasu ma”” dariya suka soyi, amma sai suka matse. Domin yadda mami ta had’a fuska zataci ‘kaniyan su.

Sun d’anyi shiru na wani lokaci shiko Auwal yana ma’kale kusa da mami kamar zai shige mata ciki so kawai yake babban yayan nasu ya shigo ayi masa nasa sanan yabar wurin.

Aiko sai gashi da alama tsaikon nashi yatsaya gaisawa da masu aikin gidan kamar yadda ya saba.

Aiko daga Auwal har mami suka had’a fuska kamar hadari.

Gaisuwar matarsa kawai ta ansa shiko sai faman hararan sa take.

Murmushi kawai yayi domin yasan kwana nan zancen don haka sai yace cikin ladabi “” Allah huci zuciyar mami ayi ha’kuri don Allah, mami kuma ma ai taimakon ‘KAUYEN zaiyi, aikin lada zaiyi idan kikaga matsalan doctors da suke saikin zubar masu da hawaye “”.

“” Kum………..,yimin shiru malam, ai ba haka bane kad’ai hanyan da za’a taimaka musu ba, kuna iya nemo wasu kukai masu ba yarona ba, mami taimako fah kuma ma babu ruwan mumu bamu muka turasa ba, Allah mami har ina shi’awan idan yagama bautan ‘kasan sai mune masa aiki koni nar’inka biya tunda aikin laddane””.

Cikin fad’a “” tace tofar da yamun bakin ka ba’inda yarona zashi ka tura matarka mana ainaga aikin ta ne””.

Auwal yace “” mami duk nagane su so kawai suke yaronki ya’kara baki wani cuta ya kama mikini, ba’kin ciki kawai suke dani”” hararan sa yayan yayi ganin zai sake magana sai yayi kamar zai makeshi sai yayi shiru tare da mi’kewa yana tura baki.

“” Bebyna muje, ke kuma ina Akram da Mufida?” Yace da matar babban yayan tasa, “suna gidan mu,”” yayi amma aikin san yau nan gidan suke wuni tare dani to shi kenan na barku lafia “” yace yana mai ri’ke da hannun iman.

              ***

Haka maman tata tagama mata fad’a ko gezau, haka ta tasa ‘keyar ta sukayi gida. Suna komawa wanke wanke tafara domin batayi ba ta tafi, maman kuma ta tafi kasuwa domin yo cafenen girki.

Koda Joy tagama ta gara gida sai ta sakayo gidan tayi gidan su Aisha ‘kawar ta.

Bayan ta gaida iyayen Aishan sai ta shiga d’akin Aishan, da farin ciki ta rungume ta kai kace sun dad’e basu had’u ba.

Fira suka farayi duk da Joy ba wani fira take ba domin bata iya surutu ba miskilace na’karashe, suna tsanani ‘kaunar junan su ita da Aisah akwai kyakkyawa fahimta a tsakanin su.

Iyayen Aisha basu ta’ba karanta ko ‘kamanta ba, suna nuna mata soyayya irin ta yada suke nunawa Aisha domin suna mata ‘kwad’ayin musulunci.

Wacece Joy?

Joy dai haifaffiyar Abia state ne, maman ta Gloria ‘yar garin abia ne, iyayen ta haifafun garin ne, su arnane gaba da baya, iyayen ta ita kad’ai suka haifa sai suka d’au son duniya suka d’aura mata uban ta ba wani mai shi bane sai dai rufin asiri.

A hakan bai hana kulawa da ‘yar tasa fiye da tsamanin Kuba masu karatu.

Watarana Allah ya had’a Gloria da wani musulmi, ba’kone ba d’an gari bane , soyayya suke sosai batare da sanin iyayen ta ba, sanda soyayya tai nisa sanan ta sanar musu suka nuna basu amince ba, tayi kamar zatai hauka, ciwo riris kamar zata mutu.

Badon iyayen sunso ba suka amince, amma da sharad’in idan wani abu ya taso karta nemesu, haka ko tayarda batare da tasan asalin mutumin ba sukaje sukai aure.

Auren su da wata uku yayi had’ari ya mutu, tayi kuma kamar me haka ta ha’kura.

Komawa wurin iyayen ta tayi suka’ki kar’banta, don haka sai tabar garin tayo nasarawa state cikin wani gari mai suna ‘YAR KADDE.

Zuwanta garinne tafara laulayi, anane ta haifi Joy don haka joy batasan kowa nata ba sai maman ta sai gidan su Aisha.

Tare suka gama primary school d’in garin baban su Aisha yane ma musu wani acikin gari suke tafiya.

Wannan shine ta’kaitaccen tarihin joy.

More comments more typing.

Share & comment pls????????????????????????????????
[11/5, 9:49 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????

‘KAUYEN ‘YAR KADDE

????????????????????????????

 (Ta'kai taccen labari)

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
MASAUKIN SO
SHI NAKE JIRA
BA JINSIN MU BACE
HAMDIYA DA HAMNA

Dedicated to Muhammad Ahmad Bashir

Bismillahir Rahamanir Rahim

????5⃣to6⃣

Yau Monday, Monday tushen aiki wanda akace ko bature na tsoron sa, Joy ce zaune cikin uniform d’inta, mai kalar white and green, karya wa take cikin natsuwa. Tana idar da karyawan ta d’au bag d’in ta, cikin sanyi murya mai za’ki ta kalli maman ta tana mai cewa “” mama na tafi, to my dota a kula banda wasa kullum ina mai gargad’in ki daki kula kiyi karatu domin shine gatan ki idan kika kula yesu zai dafa miki, kije Allah tsare banda shashshanci.””

Cikin gamsuwa da zancen uwan ta gyad’a kai tare da fita daga d’akin.

A ‘kofar gidan suka had’u da Aisha saura kad’an su gwara kai, dariya Aisha tayi tare da cewa “” inace baki shirya bane, naga har kusan 8pm gashi mashin na mana wuya anan balle muhau, kisan idan munyi latti basu d’aga mana ‘kafa basu duban daga nesa muke””.

Smile joy tayi tare da cewa “” muje parrot ai ko magan nan naki yasa mu’kara makara, eh naji ai guma ni, anfi san mutum mai surutu da kurma”” murmushi still ta sakeyi batare da sake ce da ita komai ba.

Tafiya suke cikin natsuwa, majalisa dai tanan yauma kamar kullum, kuma mafiya yawancin masu zaman wurin ‘yan iskan ‘KAUYEN ne, kuma suna zama kawai domin gani suran jikin dake rikitasu, yake hanasu sukuni, dare ma saboda tsabar jaraba ya hanasu barci isah ko saboda tsanani son da yake mata yakan sa har yagamsar da kansa da dare saboda tunanin ta da yake yawanyi.

Yana son tunkaran ta ko nace dukansu ko don bu’katarsu amma kwarjinin da take musu yake musu shamaki.

Tunda ya hangota yake matse ‘kafa, haka suka wuce su basu bar kallon suba, har sai da suka ‘kule musu.

“” Kai wallahi wad’ancan gayun ‘yan iskane , sun cika kallon mutane, ina lura dasu idan suka ganki kamar mayu harda lashe baki suke”” Aisha tayi zance tana dariya, ta’be baki joy tayi ba tare da ta kokula zancen nata ba, domin sam basa gaban ta.

Itama sarai tana lura dasu sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button