KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Zanyi magana yace “oyo wuce kin makara, maza aji kar a ta’ba min lafia jikin ki” murmushi nayi tare da fita daga motan.
‘Daga min hannu yayi nima haka nayi cikin makaranta.
Sauri ya tada motan yabar wurin bayan yaga shiga ta aji.
Ina shiga Aisha ta tsare ni da ido, murmushi nayi tare da cewa “lafia kallon malama?”.
“Ina kikaje ne besty? naje gida mama tace kin dad’e da fita”.
” Gidan doctor ” nace murya ‘kasa ‘kasa, don malam ya shigo lokacin.
Zaro ido tayi tare da bud’e baki, murmushi nayi tare da cewa gab da kunnin ta “rufe bakin, kinsan wannan malamin mai rainin wayau ne, ki bari sai ya fita sai ki sake wani tambayan”.
Aiko kamar wa wuya ta kasa magana rufe bakin tayi muka natsu aka fara darasi.
Yana fita Aisha ba ta barni na koda matsa ba ta jefomin tambayan.
“Mekikai a gidan doctor fisabilillahi da girman ki da ‘kiman ki?” .
“Tashin sa a barci nayi, bayan haka na masa break fast”.
San’kare wa tayi a wurin.
Niko dariya nayi, in banda abinki Aisha ina ruwan arne……..
Rayuwa tama su Joy dad’i soyayya kawai suke kamar ba gobe, suna tsananin ‘kaunar junan su da kulawa da junan su
Sosai.
Amma fa Auwal bai sake sakacin barin ‘kofar gidan sa a bud’e ba, don yana tsoron Allah yana tsoron Joy.
Duk da haka bai tsira ba, a hakan tana yawan ta’ba sa, ko son shige masa jiki.
Wani abu da ta tsiro shine zuwa asibiti duk bayan ta dawo daga makaranta, sai tazo tawani kanai naye shi.
Haka suke ta tafiya har wa yau, yanzu haka saura jibi Auwal zai koma garin sa, ya gama sabis d’in sa, ya rasa yadda zai sanar mata.
Ganin cewa suna ta faman jarabwa, don bai son ya tada mata da hankali ko kad’an.
A haka har kwana uku tayi ba tare da yasan yadda zai ya gaya mata ba.
Can Abuja su mami sun kasa sun tsare suna jiran dawo wa Auwal shiru har washe gari bashi ba labarin sa.
Sun kira wayar sa a kashe, shiko yayi hakan ne saboda bai san mai zaice masu ba.
Sati d’aya da gama wan sa saura kwana biyu su Joy su gama jarabawa, yana zaune a ‘kofar gidan sa kawai sai hango motocin gidan su yayi guda biyu suna taho wa.
Farin cikin ganin ‘yan gida da fargaba suka taru suka diran masa a lokaci d’aya.
Mi’kewa yayi daga farin kujeran da yake zaune, dai-dai nan sukai parking, nufar motan sister d’in sa yayi.
Da farin ciki ya bud’e ‘kofar motan, ita ce hakin CE a bayan motan sai Akaram.
Ko bari ta fito baiyi ba yace “oyoyo sis, oyoyo my son”.
Harara ta maka masa, tare da cewa ” shiga mota muje” d’aure fuska yayi tare da cewa “kai Anty wani irin in shiga mota daga zuwan ki?”.
” Auwal ban wasa da kai nace ka shiga mota mu tafi” bud’e d’ayan motan da akayi ne yasa shi waiga wa.
Ba kowa bane illah Dady da kan sa, sai yaya wato Wanda ya kawo sa.
Ga farin ciki ga far gaba, amma hakan ya matse yayi musu barka da zuwa.
“Son mai kake a garin nan bayan ka gama abinda ya kawo ka?” cewan Dady ba tare da ya ansa sanu da zuwan da yake masa ba.
Shiru shima Auwal yayi, ganin zai ‘bata lokaci yasa Dady yace “shiga muje” rasa yadda zaiyi yayi tunda Dady da Kansa yace haka.
Kamar zai kuka yace “Dady kuje kawai gobe zan……….” bai ‘Kari saba sakamakon wani matsiya cin harara da Dady yayi masa.
Bai dan dara ba yace “Dady bari na had’a kaya sai muje”.
” Bama wani ka wuce muje” “akwai takadduna fa a cikin gidan”.
” Jeka maza rakasa” yace da yayan nasa, bai so hakan ba amma haka yayi gaba yayan yabi bayan sa zuwa cikin gidan.
Tarka ta takkdun yayi kaf tare da abubuwan sa masu mahimmanci suka fito, amma kafin su fito ya faki idon yayan ya rubuta leta ya aje a kan kujera d’aki .
Suna fito wa saka kayan a bot d’in motan yayi tare da kallon gidan yana mai jin wani iri a cikin ransa, gashi Joy suna makaranta yau bai san yadda ‘yar rigiman sa zatai ba.
“Dady bari na bawa gidan nan key d’in nazo”.
” Ga wani can bashi ya kai musu kana ‘bata min lokaci ” waiga inda dadyn yai nunin yayi.
Aiko ganin Muhusin ne yasamu kwanciya hankali.
Matsawa kusa dashi yayi tare da cewa cikin ‘kasa da murya yana mai tura masa abu a aljihu “‘kani na, don Allah ga wannan wayan da kye d’in nan Joy na dawo wa kaba ta, kace nace don Allah tayi ha’kuri zan zo bayan kwana biyu”.
” To yaya insha Allah zan gaya mata, yauwa ‘kanina nagode” yace tare da juyawa wurin motan .
Shigan sa keda wuya suka bar wurin………………..
.
To fah, wata sabuwa inji ‘yan caca????????
Comment & share pls
[11/5, 9:53 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????
‘KAUYEN ‘YAR KADDE
????????????????????????????
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
????3⃣5⃣➡3⃣6⃣
Tun shad’aya suka gama jarabawan su, tafe suke suna d’an fira har suka zo inda Auwal ya saba zama don jiran su, don basu ta’ba jiran saba kullum shike jiran su.
“Abin mamaki Aisha yau my heart bai zo da wuri ba” cewan Joy tana mai kafe wurin da ya saba parking da ido.
Aisha tace” Allah sa dai lafia, amin” nace ina maijin fad’uwan gaba na ya’karu fiye da yadda nakeji tun da na tashi a yau.
“Mu zauna daga nan mu jira shi besty” ba tare da nace komai ba na bita muka zauna a wata gindin bishiya.
Shiru muke zaune amma idanuna na hanya, muna zaune har na tsahon wasu lokaci babu doctor babu labarin sa.
Mune har 2:00pm babu shi, a lokacin kuwa zo kuga idanuwa na, idanuwa na fal da ‘kwalla, gabana sai faman bugawa yake.
Nayi zurfi cikin tunani mai ya hanasa zuwa d’aukan mu, fatana dai ace yana cikin ‘koshin lafia idan ba haka ba akwai matsala babba ma.
“Tashi mu tafi besty kinga rana tayi da uban yunwan da nakeji” cewar Aisha tare da mi’kewa tana kamo hannu na.
Dojewa nayi na’ki tashi, kallo na tayi tare da cewa cikin marai rai cewa “please ki tashi nasan wani babban uzuri ne ya tsayar dashi, don haka mu tafi kawai”.
Gamsuwa da zancen ta nayi don haka sai na mi’ke, tare goyin mukayi muka nufo hanyan ‘kauyen mu.
Tafiya muke amma gaba na na cigaba da fad’uwa, ‘karuwan fad’uwan gaba na shine sanda muka zo muka cimma babu motan Auwal a inda ya saba ajeta, don sam bai zuwa da ita ko’ina da ya wuce kaimu makaranta.
Sai wasu lokutan da idan bai da wani abun anfani sai yaje cikin gari ya siyo. Kuma bai tafiya sam ba tare da ya sanar dani ba.
Barin Aisha nayi da sallaman mai mashin ni kuma na nufi ‘kofar gidan sa, duk da na gansa a rufe.
Bubbuga gidan na farayi kamar mara kai, zuwa Aisha tayi tajani ina turjewa don jiki na ya bani ba lafia ba.
Da ‘kar ta jani cikin gidan mu, mama ce zaune a tsakar gidan da alamu dai shan iska take, don zaune take da ‘yar single a jiki ta sai faman fifita take.
Ko inda take ban kalla ba nayi hanyan d’aki, Aisha ce ta gaida ita tare da fita a gidan.
Ina shiga d’aki nayi wurgi da jakan makarantan, za gaye d’aki na farayi.
A haka mama ta shigo ta cimmini, kallo na tayi tare da cewa” lafia kuwa Joy? ” kallon ta nayi tare da kauda kaina.
Gajiya da zaga d’akin nayi don haka na fad’a kan katifa tare da cewa” wayyo” da ‘karfin gaske hawaye kuma suka fara ambaliya akan kyakkyawan fuska ta.
Da sauri mama tazo inda bake tare da d’ago ni tace” what happened Joy “.
” Mama ina doctor yaje yau bai gaya min ba?” Nace ba tare da naba ta ansan tambayan ta ba.