KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani irin kallo na tayi tare da cewa” lallai doctor nada aiki tunda zai auri matar da bazai ta’ba fita ba sai da sanin ta da kuma izinin ta” ta had’a da tsaki tare da tashi tabar d’akin.
Eyhu na sake saki ina cewa ” wayyo doctor na ina kashiga ne zuciya ta zata fashe?” tare da rushewa da kuka.
Ranan babu zancen abinci, to yaya zakaci abinci ma bakaji yunwa ba? Toni ranan nama manta da wani abinci sam.
6:15pm Muhusin ya shigo gidan mu da uniform d’in islamiya a jikin sa.
Gai da mama yayi tare da cewa bayan ta ansa “Anty Joy na nan?”
“Eh tana nan shiga ciki” tace dashi, hanya d’akin yayi.
Ina kwance da uniform d’ina kuma har lokacin kuka nake ya shigo, naji motsi ban damu da sanin ko waye ba shiyasa ban waigo ba.
Ji nayi ance “Anty gashi inji yaya farin nan na kusa da gidan mu” ai da sauri na waigo hard murmushi na.
Nace ina kallon hannu sa “yana ina?” mi’ka min kye yayi tare da cewa” ya tafi gashi harda wayan nan yace na baki” yace yana bud’e jakan islamiyan tasa.
Gaba na ya fad’i na kalle sa tare da cewa” ina ya tafi?” Ina jujjuya kye d’in hannu na hawaye naji ya fara zubowa a fuska ta.
“Ban sani ba, wasu ne dai ‘yan birni suka zo a motoci da yawa ya shiga suka tafi” .
Yace tare da mi’kamin wayar doctor, kar’ba nayi shi kuma ya fita.
Bin wayar nayi da ido ina jujjuya shi har na tsahon wasu lokuta.
Dana wayar nayi ta kawo haske, photo nane ya bai yana a fuskan wayan, ban san sanda akai photo ba amma yayi matu’kar kyau.
Tashi nayi da kye a hannu na nayi fito daga d’aki, nufan hanya fita nayi mama na kallo na batace dani komai ba.
Gidan nashi naje na bud’e, shiga nayi har ciki.
Tun daga yanyin yadda falon yake naji wani iri tsoro da fargaba.
Shiga bedroom d’in sa nayi, kaya ne na gansa a hargitse, kuka na saki tare da d’aura hannu aka.
“Wayyo doctor na, wayyo! Wayyo mai yasa zaka min haka?, mai yasa zaka tafi ka barni?”
“Baka min adalci ba” nace tare da fad’a wa katifan sa ina mai cigaba da kuka na.
Haka na kasance a gidan nan har dare kuma baci basha sai kuka kawai. Bani na bar gidan nan ba sai 9:00pm.
Koda na shiga gida banyi takan mama ba na kwanta kawai ina mai cigaba da kuka na.
Da fitana mama ta biyo bayana, ganin inda na shiga yasa tai zargin wani abu.
Gidan su Aisha ta shiga bayan na shige gidan doctor, bayan sun gaisa da maman Aisha sai ta nemi Muhusin, tambayan sa tayi yayi mata bayani ita kuma tabar gidan.
Shiyasa bata ko nemeni ba, ganin kukan ya’kici ya’ki ‘karewa yasa ta matso cikin tausayawa ta kamoni tare da lallashi na.
Ta d’au lokaci mai tsayi tana lallashina, da’kar na dai na kuka.
Baccin ranan ban samu yin saba sam.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Auwal lafia suka kai gida, baiyi magana da kowa ba har da mami. Fushi sosai yake da kowa na gidan.
Duk wani gata da tarairaya da mami da uwar gayan suke sam bai burgesa, bai sa ya saki jiki ba.
Abinci sai anyi da gaske yake ci, kullum yana cikin d’aki, bashi da abinso dake saka shi nishad’i da jin dad’i wanda in har yana cikin yanayin zaka ga yana dariya ko murmushi, shine tunani masoyiyan sa.
Hakan da ya mai da kansa yasa damuwa mai tsanani a zukatan iyayen sa da ‘yan uwan sa, musamman mami da Anty RAHAMA.
A haka har akai sati biyu, a sati biyun nan ko yayi muguwan rama kai kace wanda yayi ciwon shekara.
Kuma a yaune yasha alwashin koma wa ‘KAUYEN ‘YAR KADDE tun da nanne farin ciki sa yake.
Shirya wansa yayi ba tare da ya sanarwa kowa na gidan ba.
Bayan ya gama shirya kansa cikin ‘kananun kaya wando na’ki da jan riga mai rane jah da fari sai wani zane na ‘baki kad’an wanda yayi matu’kar ‘karawa rigan kyau.
Kayan sun matu’kar kar’ba sa.
Fita yayi daga d’akin sa yayo main palon gidan. Da yake yau Saturday ne kowa na gida, zaune ya gansu duka, mami, RAHAMA, Dady har da yayyun sa maza.
Gai dasu duka yayi a cikin ciki ba tare da ya kallesu ba, ansawa duka sukayi idon su na kansa.
Sunji dad’in adon da yayi a tunani su ya kwantar da hankalin sane basu san ko kad’an ba hakan bane, domin kwanciya hankali sa shine yayi arab da za’bin ransa.
Gani sukayi ya nufi hanya barin palon, duk cikin su sun kasa masa magana.
RAHAMA ne kamar mai tsoro ta kira sunan sa, tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba.
Tashi tayi tare da zuwa inda yake.
Dafa kafad’an sa tayi tare da cewa” ina zakaje habibi?” Banza da ita yayi tare da zare hannu ta daga kafad’an sa ya bar wurin.
Wurin ajiye motocin gidan ya nufa, ‘barayin da motocin sa suke ya nufa.
Rufe suke ruf d’aga wa yayi d’aya bayan d’aya, gani yayi duka sunyi kura.
Cike da masifa yake ‘kwala ma mai wankin motocin kira.
Da gudu ya nufo sa, ma’kaitan kaf sunji kiran nan har ‘kwa’kwalwan su.
Hatta su mami sai da suka fito suga dalilin uban wannan kiran.
Abinda bai ta’bayi ba fuska babu walwala yana zuwa ya dur’kusa tare da cewa” gani yalla’bai” .
Ya bashi wani irin mari tare da cewa cikin masifa “wani irin iskanci ne zaka barmin motoci da ‘kira eyeh?”
Yace yana ‘kara masa wani, cike da girmamawa yace” yalla’bai go kwana hud’u baya sai da na wanke”.
“Sai akace maka kuma jiya ko yau karka wanke ko?”
“Maza wanke min wancan jan yanzu na baka minti biyar kuma ya fita, idan ba haka ba yau sai kabar gidan nan” yace tare da tsaki ya juya.
Kamar d’azu suna kallon sa ya wuce ta gefen su baikoyiwa wani daga cikin su magana ba.
Da mamaki RAHAMA tace idanun ta cike da ruwan hawaye “Dady don Allah muje mu bashi ha’kuri muji meye damuwar sa, idan ma zaman ‘KAUYEN yake so sai mu barshi ya koma idan yaso muyi masa ginin zamani a can. Sai ya rin’ka zuwa duk sati gida yana dubamu komu murin’ka zuwa”.
Tunda ta fara maganan yake hararan ta har ta idda maganan ta.
Yau da badon ‘yar gaban goshi bace tai maganan nan ai da tasha mari.
” Baki da hankali ko RAHAMA? ni kike so naje na bawa d’ana ha’kuri to bai zai ta’ba yuwu wa ba, don bashine ya haifeni ba, don ko uban sa……….”
Sai kuma yayi shiru “to bari kiji babu wata ‘KAUYEN da zai koma, nd kwanan nan zai fara zuwa asibitin sa, don an gama komai bikin bud’e wa za’a sai ya fara aiki kinji ko?” Daga nan yayi tsaki tare da barin wurin.
“Kema dai inajin mahaukaciya ce ke, wai da bakin ki kike cewa Auwal ya koma ‘KAUYEN da zama. Hmmm to bari kiji ko zuwansa sabis saboda ya rage wasu abubuwa da basu dace ba shiyasa muka dage kai da ‘kafa ya tafi”.
” Don sam bamu soba ke har Dady kan sa, saboda yayi hankali ne kawai muka kai sa” cewan babban wansu.
Kuka ta fashe dashi tare kallon mami da tai shiru .
Matsawa inda take tayi ta rungume ta tare da cewa” mami yanzu ya zanyi ya zanyi my brother ya dawo kamar da?” shiru tayi domin ita kanta abin na damun ta sosai.
Suna tsaye su biyu domin sauran sun bar wurin sai gashi ya fito.
Wuce su yake sonyi mami tace cikin matsawa da d’aure fuska.
“Ina zaka?” tsayawa yayi shiru ba tare da yace komai ba.
Tsawa da bata ta’ba masa ba shine tayi masa “dakai fa nake kayi shiru”.
Fukan nan a had’e yace” nasarawa zani ” daga haka yayi shiru.
“‘KAUYEN nan zaka ko?” Shiru yayi ba tare da ya bata ansa ba.
“Wai shin Auwal meye kakeso? Meye kake nema a ‘KAUYEN nan?” Still bai bata ansa ba.
“To tunda baka da ansan tambaya ta koma ciki” wani iri juyo wa yayi cikin tashin hankali yake kallon mamin.
Zaiyi magana tace” daga yau na sake jin sunan ‘KAUYEN nan a bakin ka bare kace zaka sai na………………………..