KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Comment nd share
Luv you all my fan’s????????????
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????
‘KAUYEN ‘YAR KADDE
????????????????????????????
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO
My ❤, my kaka, my Hafsatuwa????, my Hafnan is back.????????????????????????????????????ina masoya ku fito, ga shahararriyan Marubuciyan nan da ta saba nishad’an tar daku, wato Marubuciyan, SHI SO ‘DAYA NE, FATALWAN MIJIN NA da kuma HIBBATULLAHI. ta dawo muku da wani shahararran littafin ta mai suna KAICON SO! Masoya ku hanzar to kar kubari a baku labari Hafsat Mustafah (Hafnan) ta shirya tsaf domin nishad’an tar daku, wa’azantarwa da ilimantarwa. Da abaka labari gumma ka bayar, saboda haka masoya ku fito ‘kwai da ‘kwar’kwata domin wanke idanuwan Ku, karrrrrrr kubari…………………
*you will never brave, if you don’t get hurt. You will never learn, if you don’t make mistakes. You will never be successful, if you don’t encounter failure………………Good morning????????????
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
????3⃣7⃣➡3⃣8⃣
“Wayyo Allah na, wayyo mami na. Wallahi mutuwa zanyi, mami in…………” Sai kuma yayi shiru, kallon sa tayi tare da cewa “indai na isa zan gani” daga haka taja hannun RAHAMA suka wuce ciki, Kamar zaiyi kuka ya tsaya kallon hanyan da suka bi. Yana tsaye ba’kin ciki fal a cikin ransa, amma ya ya iya, haka ya gama tsayuwan sa yayi ciki, ko kallon inda suke baiyi ba san da ya shiga.
Sati na zagayo wa akai gagarumin bikin bud’e asibitin, Dady yayi ‘ko’kari matu’ka ya cika uba na gari wanda kowani d’a zai alfaharin kasancewan sa uba a gare sa.
Ya zuba masa duk abinda ya kamata, had’a dasu manyan doctors, kayan aiki na zamani tun daga ‘kasanr waje da dai sauran su.
Amma abin mamaki koda na waiga inda mutumin ku yake sam babu alaman farin ciki a tare dashi, fuskan nan a murtuke.
Angama taro lafia sai dai fatan Allah sa albarka.
Ya fara aikin sa cikin nasara, yana samun girmamawa ga duk ma aikatan, suna matu’kar girma mashi, aiki sosai suke a asibitin ciki tsantsan ‘kwarewa.
Lokaci ‘kan’kani asibitin yayi suna, sun sami lambobin yabo daga wurare daban, don gaskiya doctor Auwal ‘kwararrene.
Kimanin wata hud’u da bud’e asibitin sa, amma Auwal bai ma kowa magana sai ta kama dole, walan gida ko asibiti.
Haka zalika fuska a d’aure, mata na son sa kamar zasu mutu amma babu fuska balle su san’kafa mai tayin soyayyar su.
Duk wata mace maiji da kanta da isa, burin ta Auwal ya kula ta.
Amma hakan bai samuwa sam, Auwal ya zama wani irin mutum.
Auwal ya zama fitinan nane ‘karfi da yaji, abi kad’an kayi kuskure zaka sha masifa ko kuma ya kore ka, gida ko asibiti. shiyasa duk wani mai son kansa da arzi’ki yana gujewa ‘bacin ran Auwal.
Ba gida ba ba asibiti ba kullum kwanan duniya ka sake kayi kuskure kad’an yanzu zai ‘kore ka, haka zalika ko sakon baka ‘karawa a wurin.
Zaune yake a bakin bed d’in sa sai faman kiran wayar sa da ya bawa Joy yake da ya zame masa kullum kamar ibada amma bata shiga.
Kamar zaiyi kuka yace” why my happiness? Kullum sai na kira layin nan yafi abinda yafi, ko ba’a baki bane? Kai inah nasan yaron nan sosai bazai ‘ki baki ba”.
“To amma meye na kashe waya?”.
” Oh Allah na help me” yace tare da sake gwada layin, still dai abu d’aya baturiyan nan take ta nana tawa.
Cikin fushi yayi wurgi da wayar, kwanciya yayi a gadon tare da runtse idanu.
Bai ankara ba kawai sai ga hawaye masu d’umi suna zubo mishi, bai hansu su zuba ba har sai da suka bar zuba don kan su.
Dai-dai nan yaji ana knocking, tsaki yayi tare da tashi ya nufan ‘kofan, bud’e wa yayi.
Ganin wacce ke tsaye yasa ya mai da ‘kofa ya rufe, abin mamaki fanz RAHAMA ce fa akai wa haka, lallai abin babbane.
Kuka ta fashe dashi, yana jin kukan har cikin ransa amma yayi biris da ita, da yaji kukan na damun sa ma sai ya tashi ya shige toilet abinsa.
Kuka tayi sosai kafin tabar wurin, daga nan ta zarce part d’in mami.
Da gudu ta nufe ta, tace cikin kuka “mami don Allah kuyiwa my brother abin da yake so, don Allah ku barsa ya tafi can d’in don samun kwanciya hankalin mu. Mami bai magana da kowa, baicin abincin gidan nan sai da matsi”.
” Mami jifa, ni na raine sa da hannu na, na kula dashi kamar uwan da ta haifesa, shine abokin shawarata, abokin firata, shine kesani nishad’i. Shike sani farin ciki fiye da kowa, baya son ya ganni cikin damuwa ko d’an ‘kan’kani ne, ya tsani ganin ‘bacin raina. ‘Kanina na sona, kullum…….” Sai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.
Rarrashin ta mami take, tace cikin lallashi “ki fita harkan Auwal idan ba haka ba ciwon ki na gab da dawo wa”.
“Mami ina fita harkan Auwal fa kika ce?” Tace cikin zaro idanu “amma mami bakiyi tunani ba sam, Mami Auwal fah d’anki ne na duniya da lahira, maraya ne kin sani sarai, mami kina tunanin share sa da kuke hakan ya dace? har yau kun’ki zama dashi kuji meye damuwar sa meye yake so?”.
” Shin haka ya dace kuyi ma maraya? kunyiwa maraya adalci kuwa? mami kamar bake ba, mami kiyi tunani da kyau shin abinda kukayi dai daine? Auwal d’ane d’an gata, saboda iyayen sa ma ‘yan gatan kune. Mami kiyi tunani “.
” Mami kamar bake ba, mami Auwal d’inki ne fah, yaron Anty ne fah. Anty baza ta ta’bajin dad’in ace yau ga yayan ta tabar mata d’a cikin wannan yanayi ba, kin bar mata yaro cikin damuwa”.
“Mami kin manta wannan shine jinin Anty ‘kwalllin ‘kwal? Shine ita fah tunda bata, mami ina son da kike mata ya tafi? wai yau da bakin ki kike cewa na rabu da jinin Anty na? Bayan Anty na itace uwata.”.
” Anty da Abbey mutanen kirki ne sosai ke kanki sheda ce, uwa d’aya uba d’aya kuke mami ko kin mata Abbey ‘kanin mijin ki ne uwa d’aya uba d’aya? “.
” Auwal jinin mune gaba da baya, da mamaci na magana da tabbas Anty ta sanar miki bata jin dad’in yadda kika bar mata yaro kamar mara gata ba, Anty ta mutu tana murna da murmushi na tabar farin cikin ta a hannun ki, saboda tasan bazaki ta’ba wofin tar mata dashi ba”.
RAHAMA ke zancen nan cikin kuka mai tsanani.
“Mami kije kiji mai d’anki yake so, mai yake bu’kata. Ki nemo yadda zakiyi Auwal yayi farin ciki, Anty ta baki amanan d’anta tana tunani kece kad’ai wanda take da ya’kini tilon d’an ta zai samu farin ciki daga gare ta”.
Daga haka ta tashi tabar d’akin mamin, jikin mami yayi sanyi sosai, don gaskiya maganan RAHAMA ya shige ta sosai.
Su uku ne, amma kuma itace abokiyan shawara firan ta duka, tace tana maiji kewan ‘yar uwan ta ta.
Tashi tayi cikin sanyin jiki ta fito daga d’akin nata, bata zame ko inaba sai ‘kofar d’akin Auwal.
Knocking tayi tayi amma Auwal ya’ki bud’e wa don a tunani sa RAHAMA ce ta dawo, don duk abinsa yana ganin girman mami fiye da kowa a gidan, shiyasa ita kad’ai yake d’aga wa ‘kafa.
Haka ta d’au tsahon lokaci tana bugawa amma ya’ki bud’e wa.
Kiran sunan sa ta farayi amma shiru kakeji tamakar bashi a d’akin.
Haka ta gaji ta ha’kura akan sai da safe.
°°°°°°°°°°°
Washe gari kuwa tsiro da wani abu yayi, suna idar da sallan asuba Dady na kallon sa yabar gidan a guje kamar zai tashi sama.
Dama yayi wanka sannan yayi alwallah, da mamaki baki sake Dady ke kallon hanyan da yabi.