KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
????3⃣9⃣➡4⃣0⃣
Joy kuwa rayuwa tama ta zafi, kullum cikin tunani take, duk tabi ta rame, ta zama kurman ‘karfi da yaji. Dama abinka ga miskila, abin sai ya’karu fiye da da. Kuka ya zama shine abincin ta, shine kullum dare rana. Anyi lallashi har angaji an barta, domin kamar ‘kara zuga ta suke. Magana daga eh sai a’a idan ta gada ma taso, idan bata soba to sai dai d’aga kai ko ta girgiza maka, ko tayi kamar ba da ita kake ba. Makaranta ma barin zuwa tayi maman tayi tayi ta’ki zuwa Aisha tayi amma a banza. Jarabawa haka suna kallo ta’ki zuwa ta’kari sa. babban takaicin ta na’kin kula kowa da’kin zuwa makaranta shine saboda har kwana biyu da barin sa bai kira taba har wayar ta mace saboda rashin charge. Da wanna dalilin yasa kowa haushi yake bata, wayar ma ajeshi gefe tayi don tace bai da anfani.
Rayuwa tayi mata wani iri bata jin dad’in shi sam, kullum addu’a take ubangiji dawo mata dashi lafia.
Haka aka d’au kusan sati, wata, shiru babu Auwal. Wanda a wanna lokacin ne sukayi hutu kuma har sun dawo, amma Joy ta’ki makaranta fir.
Koda yaushe bata da aiki sai tunanin da kuka, har tsawon wata hud’u.
Maman ta fara nema mata taimako daga wurin ‘yan uwan ta arna, shine aka fara samun sau’ki, don alhamdulillah yanzu tabar kuka, tunani ma ta rage sosai.
Makarantan dai ta’ki, ganin sau’ki na samuwa yasa basu matsa mata ba.
Rashin ‘kin makarantan Joy ba ‘karamin ba’kin ciki Aisha tayi ba.
Don Aisha ita kad’ai ke tafiya makaranta haka ma dawo wa.
Lokaci na ta tafiya, yanzu haka Aisha na SS2.
Joy na gida har yanzu, ganin yanzu ta kwantar da hankalin ta, yasa Aisha tazo har gida taro’ke ta har da kuka akan ta koma makaranta shine fa ta amince zata koma.
Tako koma d’in amma JS3 ta koma, ta mai da hankali sosai tana karatun.
Lokacin jarabawa nayi ta zana, koda sakamako ya fito sunyi farin ciki sosai.
Daga nan ta fara cuku cukun neman cigaba, ta kuma samu ta fara SS1 d’in ta cikin kwanciyan hankali.
Lokacin Aisha na SS3.
Karatu suke ba wasa don sun mai da hankali sosai.
Kada kuyi tsammanin cewa wai joy ta shafe babin Auwal a zuciyan ta.
Ko d’aya yana nan daram, kuma kullum bata cire rai da cewa zai dawo gare taba watarana.
Kuma kusan kullum sai tashiga gidan nasa, watarana ma a can take wanka da dai sauran su. Mama bata ta’ba hanata ba, don tasan zafin so, don shine silan rabuwan ta da iyayen ta.
Gidan na matu’kar d’ebe mata kewan shi sosai, yana rage mata wani abu.
Haka take tafiyar da rauywan ta cikin tsananin begen doctor d’in ta.
Amma dai-dai da rana d’aya bata ta’ba nuna ko a fuska tana damuwa dashi ba.
Nunawa take tama manta dashi, hakan ya faranta ran bestyn ta da maman ta.
Anzo anfara registration na waec da neco, sai Aisha tace ma baban ta ya biya musu, ya ansa akan zai biya, saboda haka da murna tazo gidan su Joy ta sanar mata.
Tace” besty an fara registration fah” shiru ta mata kamar ba da ita take ba.
Ta sake cewa” haba besty ina magana kina banza dani kamar ba dake nake ba” tare da ta’ba ta.
‘Dago dara daran idanun ta tayi ta kalle ta ba tare da tayi magana ba.
Aisha ba tai zuciya ba ta sake cewa” besty an fara registration na waec da neco, nama baba magana akan ya biya mana don banson na barki a baya”.
Ta tsaya tana kallon ta tare da jiran abinda zata ce.
Murmushi gefen baki tayi tare da cewa” ban bu’katan haka gaskiya, na fison nayi karatuna a tsari, banso wuce ba”.
Daga haka tai shiru tare da kauda kanta, juyo da fuskan nata Aisha tayi tare da cewa cikin ‘bata fuska” meye nufin ki wai?” shiru ta mata, tace” nufin ki na samu baba nace masa me bayan yace yau zaije ya biya? da yake tun jiya nayi magana”.
“Bazan yiba nace miki” kuka ta fashe dashi tare da cewa” shikenan tun da ke ba’a iya miki sai abinda kike so shikike so kikeyi ” .
Daga haka ta mi’ke ta fara tafiya da ninyan barin gidan.
Sai da takai ‘kofa sai taga bata kyau ta mata ba, don haka tace” kiyi ha’kuri na amince”.
Waigo wa tayi cikin tsantsan farin ciki tana kallon ta amma kamar ba ita tai maganan ba.
Fuska d’aure kuma kullum haka yake.
Dawo wa tayi da murna ta rungume ta.
Lokaci nayi suka zana jarabawan su cikin nasara da kwanciyan hankali.
Alhamdulillah sunyi nasara don certificate yayi kyau sosai.
Daga nan sai aka fara shirin jam.
Shima sunci don haka suka samu gurbin karatu a jami’an nasarawa.
Kowa fanni da ta za’ba aka bata, Aisha low, Joy fanin habibin ta ta za’ba.
Karatu suke cikin kwanciyan hankali, a lokacin duk kannin halitan cigakkun mata sun bayyana a tare dash, ko dama can Joy ba bata ba tana da komai.
Kyawawan ‘yan matane ajin ‘farko, Joy dai farace kamar yadda kuka sani siririya doguwa, mai yalwataccen gashin kai. Ga bakin ta madai daita, masu d’aukan hankali. Ga fararen idanu.
Akwai diri mai d’aukan hankali, komai nata ya ‘kara cika da fitowa, ba shakka Joy had’ad’d’iyar budurwace mai kimanin shekaru 20.
Kyawun ta mai d’aukan hankali ne, don a halin yanzu samari sun fara zarya ba kuma ‘kananun mutane ba, a’a irin ‘ya’yan manyan mutanen nan.
Bata sauraron su ko kad’an. Aisha ma babu laifi tana da nata kyau d’in dai-dai ita. Itama tana da samarin amma ba irin na Joy ba.
Kuma itama bata kula su karatun su kawai suke .
Da taimakon baban su Aisha suke karatun su cikin rufun asiri, yana matu’kar ‘ko’karin ganin basu rasa komai ba na bu’kata.
Dai-dai na talaka.
°°°°°°°°°°°°
Lokaci ba ‘karya bane, don a yanzu haka Joy ta gama karatun ta, Aisha ta riga ta gama wa tunda course d’in su ba d’aya bane. Aisha tayi service har ta gama, saura Joy. kuma dai-dai da sarannan Aisha ita da wani d’an mai kud’i.
Bata so haka ba amma bata da yadda ta iya saboda nacin wanna d’in da kuma mahaifin ta, don yace tunda angama karatu sai aure kuma.
Wata d’aya kacal aka sa, taso Joy ta tsai da wani a cikin maneman ta idan yaso a had’a ayi tare amma fir ta’ki.
Don da ta matsama tunda takama kuka sai da takwana uku bata magana da kowa ko abinci ta’kici shiyyasa ta ha’kura.
Shirye-shirye suke ba kama hannun yaro, daga ‘bangaren angon har amarya kowa shiri yake.
Biki ya rage saura sati biyu ango yazo musu da albishir d’in ya sai musu gida a cikin gari can G R A keffi, iyayen Aisha sunyi murna sosai.
Tare wa washe gari don a can za’ai biki.
Kuma gidan yace parts uku ne har da maman Joy, itama tai murna tayi godiya sosai.
Koda Joy ta samu labari fir tace babu inda zata, don bata son Auwal yazo bai same taba..
Don bata cire rai akan cewa zai dawo gare ta ba.
Sai da maman ta ta nuna ‘bacin ranta sosai sannan ta yadda suka bar ‘kauyen sai faman kuka take.
Gida yayi sosai ba laifi, wani babba bane amma ya burgeni sosai.
Bayan tare wansu da sati aka fara gudanar da biki, tun daga wanna lokacin Aisha ta fara kukan rabuwa da Joy .
Babban tashin hankali ta shine ba a gari zasu zauna ba, don angon d’an abuja ne, can ma yake aiki.
Ana shirin biki Aisha na ciwo, tun tana a tsaye har ta kaima kwanciyan a gadon asibiti.
Tashin hankali sosai wad’an nan a halin suka shiga, likita kuma yace a mata abinda take so, idan ba haka ba komai na iya faruwa.
Don haka iyayen ta suka tambaye ta damuwa ta a gaban angon da kowa nata.
Tana kuka take cewa” so nake Joy ta bini” koda aka tambaye ta ina baki shakku tace abuja.