KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

‘KAUYEN ‘YAR KADDE

????????????????????????????????

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????

we are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all………DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO

Dedicated to my lovely fan’s

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

????4⃣3⃣➡4⃣4⃣

12:40pm yayi musu a ‘kofar get d’in gidan su Aishan, horn yayi mai gadi ya le’ko. Da sauri ya koma ya bud’e suka shiga.

Parking yayi Zarah ta fita daga cikin motan tabar Aisha, part d’in su ta nufa.

Zaune ta tarar da maman ta a cikin palo tana kallo tashan su na arna.

Jin motsin mutum yasa madam Gloria wai gowa, ganin Joy cikin wani irin yanayi kuma a baza ta yasa ta mi’ke tare da nufo ta.

Rungume uwan tayi tare da fashewa da matsanancin kuka.

Shafa bayan ta tayi alaman rarrashi har na tsahon wani lokaci, sa’an nan ta d’ago ta tare da cewa” mai ya farune Joy? lafia kuwa?” a lokaci d’aya ta jefo mata wad’an nan tambayoyin.

Kallon uwan tayi face to face tace” mama waye ubana?”

Kallon ta tayi da mamaki kwance akan fuskan ta tace” wani abu ya farune?”

Bata nata ansan taba ta sake cewa” nace waye ubana? yana ina? don ina bu’katan mahaifina a halin yanzu. Inason sanin dangina”.

Kauda kai madam Gloria tayi tare da cewa” ya rasu”.

“Ya rasu fa kikace? to naji ina ‘yan uwan sa? ko nace dangin sa?”

Tace” bansan inda suke ba”.

“Wani irin magana ne wannan mama, anya kuwa taya ma hakan zai kasance?, hakan ba mai yuwuwa bane”.

” Mama banson wani ‘boye ‘boye nazo nan ne saboda inason nasan wacecce ni?”

“Joy nace miki baban ki ya rasu, ya rasu naji bai da ‘yan uwane?”

“Eh” tace tana hararan ta, kallon uwan tayi na tsahon wani lokaci tana nazarin ta.

Can ta jefo mata wani tambayan tace” mama ina iyayen ki suke? tunda baki san na mahaifina ba “.

” Bani da” tace cikin masifa tare da cewa” banson ki sake min wani magana anan haka kuma ya isa”.

“Bai isa ba mama, ko dai cikin shege kikayi kika haifeni ya raboki da iyayen ki?”.

Hawaye ne ya fara kwaranya akan fuskan mama.

Cikin ihu tace” mama ba kuka nake da bu’kata ba, sanin ko wacecce ni nada matu’kar mahimmamci, kodai daga sama na fad’o?”

Mari uwan ta wanke ta dashi tare da cewa” ya isah, ya isa, haka Joy “.

Tana ri’ke da kuma tunta tace cikin d’aga murya” bai isaba, ba kuma zai ta’ba isaba waye ni mama? ki fad’a min koni wacecce ke ko cikin shegene kikayi ki sanar dani”.

“Joy ni kike ma magana na rashin kunya? am your mom fah?”

“Nasani ai, nasan koke wacecce amma bansan waye ubana ba, to a fad’a minin ko nakai ‘kara”.

” Joy nice fah? kalli kiga mom d’in kice fah” tace tana mai juyo da Joy d’in tana fuskan tan ta.

Zarah tace” na sani nasan kece uwata shiyasa nake tambayan ki ubana, don bai yuwuwa macce tayi ma kanta ciki ba tare da namiji ba”.

“Da namiji ake had’u a samar da ciki, mama ina ubana, d’an uwan mu’amalan ki?”

“Kada ki damu sanar dani bazan miki komai ba, ko shi kan shi kawai dai inason sanin shine, idan bashi ai yana da ‘yan uwa. To sanar dani ina suke?”

Kuka mama ta fashe dashi mai tsanani, niko idona ya rufe bai dameni ba, don babu abinda nakeso a halin yanzu ko ta halin ‘ka’ka.

Cikin kuka ta fara zaiyano minin da asalin ta har zuwa auren ta da babana da kuma sa’kon rasuwan sa da ta samu da kuma yadda sukayi da iyayen ta har tabar garin ta (idan baku manta ba na baku labarin maman Joy tun a farkon labarin).

Kuka suke dukan su babu mai lallashin wani, sun dad’e suna kuka kafin Zarah ta tsaigai ta tare da cewa” mama yanzu tunda kike dashi bai ta’ba gaya miki garin suba? ko wani nasa guda d’aya baki sani ba?”

Shiru tayi tana tunani kafin ta nisa tace” bai ta’ba gaya min ba, don a wani masallaci a Abia aka d’aura mana aure” .

Bata hakurin abinda namata nayi bayan hankali ya natsu.

A nan ne nake sanar mata da cewa na musulunta, bata wani damu da hakan ba tunda ubana ma musulmi ne.


Aisha bayan fitan Zarah ta bita da kallo tare da girgiza kai idanun ta cike da ‘kallah.

Dawo da idanun ta tayi kan mijin ta taga ita yake kallo.

Ganin tana son yin kuka yasa ya girgiza mata kai, had’iye kukan tayi tare da cewa” muje ciki to?” fita sukayi daga cikin motan tare da nufan part d’in Umman Aisha.

Sallama sukayi a bakin ‘kofan shiga falon, aka ansa musu, ba kowa bane illah Muhusin dake zaune yana home work, shigo wa sukayi yana arab da fuskan sister d’in shi ya taso da gudu yazo ya rungume ta.

Tare da cewa” oyoyo anty Aisha? ” murmushi tayi tare da cewa” sannu yaron Umma ina umman?”

“Tana ciki” yace tare da kallon Abdul yace” sannu da zuwa yaya Abdul”.

Hararan wasa ya jefa masa tare da cewa” ban ansawa, sai yanzu ka ganni?”

Murmushi yayi tare da sunkuyar da kai yace” yi ha’kuri yaya”.

“Nayi to oyah zo” zuwa kusa dashi yayi ya rungume sa tare da masa yadda yaga Aisha tayi.

Dariya Aisha tayi tare da cewa” bari naje na kira Umman”.

“Barta bari naje na d’an huta yanzu haka barci take kada a taso ta”.

” Yauwa hubby ka amince mu kwanan ko?”

“To basai kisa na amincen ba, komin dare yau zamu koma tunda kuka taso tafiyan da ba’a shirya ba”.

Yace yana hararan ta, murmushi tayi tare da cewa” Allah baka ha’kuri mijin Aisha to muje na rakaka”.

“Barshi na hutar dake, maza kuyi abinda zakuyi saboda mu koma da wuri”.

” To” tace dashi tana tsaye har yabar falon sannan taja hannun Muhusin sukayi ciki.

Sallama sukayi a bakin kofan Umma ta ansa musu, shiga sukayi.

“A’a wa nake gani kamar Aisha na?” turi baki tayi tare da cewa” waye to Umma idan bani d’in ba?”

Murmushi tayi tare da cewa” maraba da mutan Habuja, lale marhabun da amare”.

Murmushi mai ‘kayatarwa Aisha tayi tare da nufan inda Umma take tare da zama kusa da ita.

Tace” ina wuni Umma” “lafia lau, ya kuke?”

“Lafia qalau Umma” “to ya mai gidan naki?”

“Yana lafia, gashi can ma tare mukazo”.

“Maraban ku, ina d’ayan amaryan?” cewar Umma cikin sigan tsokana.

‘Kwala ya taru mata a idanu fuskan ta ya canza.

“Menene Aisha? ina take?”

“Tana part d’in su, lafia take?” tace kamar za tai kuka” eh”.

“Anya kuwa Aisha? nafa sanki musamman akan Joy, yanzu haka wani abu ke damun ta”.

” Lafia qalau take Umma, sai dai wani abu dake damun ta shine mukazo mama ta fad’a ma”.

“Kuma ma ta musulunta yanzu Fatima take muna cema ta Zarah”.

Washe baki Umma tayi tare da cewa” kai masha Allah, alhamdulillah. Amma nayi mata murna sosai, Allah kasa maman ta itama ta musulunta “.

” Ameen Umma”.

“To meke damun ta kuma?” shiru tayi ba tace komai ba sai ma wasa da yatsun hannun ta da take.

Ganin haka Umma ta gane bata son sani don haka bata matsa mata ba sai ma cewa da tayi” Allah ya yaye mata damuwan to”.

“Ameen Umma” tace cikin sanyin murya.

“Tashi kije ki kaima mijin ki ruwa da abinci”.

Tace” yaje ya dawo” da mamaki Umma tace” yaje ya dawo kamar ya? daga zuwa kuma ko ruwa bai shaba, ki barsa ya fita amma dai babu hankali a lamarin ki”.

“Sai ki kirasa a waya kice yazo yaci abinci”.

” To Umma” tace tare da ciro waya a cikin jakan ta.

Koda ta kira sanar mata yayi bashi a kusa, don haka sai ta fad’a ma Umma, Umman tayi mata fad’an kada ta sake haka.


2:10pm Zarah ta shigo part d’in su Aisha ita da maman ta, Zarah ta gaida Umma. Aisha ta gaida maman Zarah.

Sai suka kama fira kuma, suna firan ne Abdul suka shigo tare da baban Aisha da yake Umma ta kirasa to ya dawo kenan shima Abdul ya dawo suka had’u a compound d’in gidan shine suka shigo tare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button