KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai da suka kusa barin garin sannan suka sami mashin guda d’aya, kamar yadda suka saba haka sukai wato hawa su biyu.
Sai makaranta, sai muce a dawo lafia su Joy………
***
Ga Muhammad Auwal kuwa barcin sa kawai yake ta shararawa a safiyar Monday bayan yasan Dady yace lallai yau ya wuce idan ba haka ba ransa zai mugun ‘baci.
Mami ta shigo yakai sau biyar bai tashi ba, haka ma yanzu ta le’ko haka zalika bai tashi ba, don haka ‘karisawa gare sa tayi tare da niyan tada sa, domin tana tsoron Allah ta tana tsoron mijin ta.
“” Son tashi haka don Allah, tukan Dadyn ka yafarga baka shirya ba”” tace tana mai girgiza shi.
Mi’ka yayi tare da shagwa’ba fuska tare sauke lumsheshun idanuwan sa a fuskan ta.
“” Mami kin tasheni ina barci na mai dad’i bayan kisan sai one o’clock zan tashi, please mamina in koma”” girgiza kai tayi tana mai jinzafin ba yadda zatai da mai gidan nata.
Ganin ta cikin tsananin damuwa sai yaji baiji dad’in hakan ba don haka sai yasakin mata murmushi tare da cewa “” mamina bar damuwa zan rin’ka dawo wa kullum bashine damuwanki ba?, a’a son ban yadda ba bason yawan bin mota ga gari mai nisa bari kawai, kuma ma Dadyn ka yace wai sai Kai five month sanan zaka zo sau d’aya……ina mami bazan yada ba, bazan iya ba sam, komi dady sai yarin’ka tsauwalamin, why mami?”” Yace, kwalla na taruwa masa a ido.
Shafa fuskan sa tayi tare da cewa “” yi ha’kuri son tashi kawai mubar maganan nan tashi maza ka shirya kazo Ahmad ya yakai ka””. Bai sake cewa komai ba ya mi’ke.
Bayan ya fito d’aure da towel a jikin sa, d’aya kuma na hannun sa yana share kai.
Mami ya gani zaune tayi tagumi, yarda towel d’in hannun sa yayi da sauri tare da nufan ta.
Cire hannun da tai tagumin dashi yayi tare da cewa “” mami kibar damuwa nan don Allah, idan ba haka ba Allah bazani ba sai dai Dady ya kasheni”” yana mai d’aura kansa a cinyan ta.
‘Digar hawayen sa yasa taji jikin ta yayi sanyi, don haka kauda damuwar dake kan fuskar ta tayi tare da share masa tana sakin murmushi ya’ke.
“” My boy, yaushe zaka zama jarimin mazane? kuka sam baima wuya, ehey sweetheart d’ina?””.
Zum’bura baki yayi tare da cewa “” mami nifa jarumine niba ragon maza bane””.
“”Okay naji maida wu’kar, nunamin zahiri, maza shirya muje, ka tada hankali sister d’inka why Auwal? yanzu haka mijin ta yasanar min sai kuka take wai sai tazo Nigeria””.
“” Oh my god! sorry my heartbeat, mami nakasa jurewa ne, mami banso bata nan ba, naji bazan iya tafiya ba tare da nasanar mata ba””.
“” Mami na yanzu ya zanyi? oho ma sanda zaka sanar mata meyasa baka tambayeni ba sai yanzu, kasan dai ciwon ta baisan damuwa da hayaniya ko?, ance kar a gayamata, kasan lamarin tsakanin ku sai Allah bata son damuwar ka ko kad’an. Yanzu don Allah mamina bazaki kawo mafita ba, my love na can banso ciwon ta yatashi, kuma ma Allah mami said a nace mata takwantar da hankali ta, insha Allah babu abinda zai sami ‘kanin ta. Ta kuma nunamin ba komai fah”” yace yana mai jin zafi a zuciyar sa.
Tausayi ya bata sosai ga time na tafiya don haka sai ta lallla’bashi tare da cewa “” maza shirya zansan yadda zanyi, Allah mami na?”” gyad’a masa kai tayi.
Turo baki yayi tare da marai rai ce, “” mami to kirata yanzu”” yace yana mi’ka mata wayar sa.
Ganin yadda ya marai rai ce, yasa ta nisa cikin tunani domin bata da abinda zata lallashi Rahama dashi, bata yadda da maganan kowa indai akan ‘kannin nata ne, Indai bashi ne yace ba.
Don haka sai tace “” son kirata kace mata da yadda nka zaka insha shi kenan, ki tabbata mami zata yadda? Eh mana””.
Don haka bai sake cewa komai ba sai dealing number ta da yayi.
Da ‘kar ya shawo kanta, tare da masa fatan alkhairi.
Wani gagarumin nfashi ya sauke.
Tare da rungume mami “” yes mamina ta ha’kuri, to haka dama nakeso maza shir……..bata ko rufe baki ba taji ehun mijin ta.
Don haka sauri ya shirya dama trolley sa tujiya mami ta cika masa da kaya.
Koda suka fito sai fad’a yake, basu ce komai ba illah fita da sukayi gaba d’aya harda yayan sa Ahmad da zai kaisa……..
Fatan alkhairi sukayi masa duka iyayen nasa, Dadyn kansa sai da yayi ‘kwallah, shi kansa bada son ransa zai tura shi ba, amma guma yayi masa haka ‘kila ya natsu yasan ba komai mutum ke samu ba duk kud’i sa.
Kila ya daina ‘kaman talaka, yasan talaka shima mutum ne ba abin ‘kama ba.
Haka suka d’auki hanya.
***
Bai ta’ba zuwa nasarawa ba sai wannan karan, da fari da yaga garin sai yace yana mai murmushi “”yaya amma garin nada Kyau fah, shine d’an isakan can yace ‘kyauye zani”” dariya kawai yayan yayi masa bai ce dashi komai ba.
Gani yayi anata tafiyan, sai ya sake cewa “” yaya wai haryan zu?, eh ai munkusa””.
Daga nan suka yi shiru duka sai da sukaje kwanan fiyanku sanan suka d’auki hanya, a nan ne zuciyar sa ta tsinke da gaske ‘KAUYEN zashi.
Bai sake mamaki da ba’kin ciki ba sai da yaga suna sama da ‘kasa.
Tafiyan suke kamar zasu tuntsura domin hanyan sam ba Kyau.
Hawaye yaji yana zubo masa don haka cikin kuka yace, “” yaya yanzu ‘kiyayyar da kuke min har takai haka? Yaya nifah ‘kannin kune, autan Ku, uwa d’aya uba amma kuke min ‘yan ubanci………..””
Wani gugugum da yaji yasashi yin shiru……….
Camment & share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????
‘KAUYEN ‘YAR KADDE
???????? ????????????????????
(Ta'kai taccen labari)
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
MASAUKIN SO
SHI NAKE JIRA
BA JINSIN MU BACE
HAMDIYA DA HAMNA
Masoya godiya nake, Nagode da bibbiyan na da kuke, inajin dad’i matu’ka iya wuya anatare????????????????
Antyna kina inah? ga sa’kon dubun gaisuwa ezuwa gareki (Sister Naje’atu).
Bismillahir Rahamanir Rahim
????7⃣to8⃣
“” Kutimelesi, yaya ji wuri fisabilillahi, ji wani rami, Allah har na sada’kar mutuwa zan, yaya please kamaidani, kumin rai Allah mutuwa zanyi, Allah ko sauro sai ya kasheni. Kaikakai, yaya ji wancan gadan cinyayye, don Allah mu koma, idan ba haka ba kuma shikenan yaron mami taka ta’kare wayyo autan mami, wayo d’an gatan Rahamatu, pls yaya mu koma kaga kai kana da masu maka addu’a ni kuma fah?, wanda zata haifanma ba’a haifeta ba bare azo……., zaci uban kafa, kasan dai niba sa’an ka bane ko? ko dun kaga kanata iskancin ka ban tankaka bako? to gargad’in mami ne, bancin haka sai na faffashe bakin rashin kunya, banza shashasha, guma kaje ko maji sa’kat. Allah ka sake magana sai naci uban ka, don wallahi ka fara isata zan aje zancen mami a gefe inci ‘kaniyan ka, idan yaso idan naje na bata ha’kuri sa’ba mata danai”” yaja tsaki.
Gum yayi da bakin sa domin yasan ba ‘karamar aikin sabane ya sassa’ba masa, don haka da ganin fuskan nan guma yayi shiru kawai don ba mai ‘kautarsa.
Haka koda suka zo gadan rutse ido yayi yana mai jin fad’uwan gaba, suna wuce wa ya sauke wani nannauyan ajiyan zuciya tare da kallon yayan, harara ko yasamu don haka bai sake cewa komai ba har suka isa cikin garin.
Aiko yara sai faman tururuwa suke gurin biyo motar manya ko sai kallon motar suke harda baki da hanci, kai gaskiya ‘KAUYEN ci baiyi ba loz.????
Shiko Auwal sai faman yatsina yake da harare harare.