KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaishe da su Umma yayi cikin girmama wa, su Zarah suka gaida baba.
Daga nan baba yayi musu nasiha na zama lafia da ha’kuri da juna.
Daga nan sai Abdul yace bayan baba ya sallame su” idan kun gama ina jiran ku saboda kada muyi dare” daga haka yayi musu sallama suka ya fita.
Yana fita yasa mai gadi shigo musu da kayan abinci ya kira Aisha ya’kara musu da kud’i, albarka suka sa masa sosai sa’anan suka mai godiya.
Basu suka bar gida ba sai da sukayi sallan la’asar sannan suka d’auki hanya.
Saura sati biyu bikin Husna aiki yama Zarah yawa ga shirye-shiryen biki ga aikin office, haka take ta fama, komai za’a sai Husna ta nemo ta. Tsare-tsaren biki itace kan gaba.
Anfara gudanar da biki tun biki ya rage saura sati d’aya, yau wannan bidi’an gobe wancan.
Kuma har yau Zarah bata ga ango yazo ba, daga ‘kawayen amarya sai abokan ango aketa gudanar da abubuwa.
Da kyau dinner da za’ayi ana gobe biki bayan walima, sai Husna ta shiga damuwa na rashin halattan ango duk wurin shagulgulan biki, ta kuma gaji da tambayan da ‘kawaye suke mata na rashin ganin angon, tun tana ‘karya yanzu haka ‘karyan ya ‘kare kuma a rasa mai zata ce dasu.
Zaune take jugum a cikin d’akin Zarah ta buga uban ta gumi, har Zarah ta shigo bata san ta shigo ba.
Zuwa kusa da ita Zarahn tayi ta zauna tare da dafa ta.
Waigo wa tayi jin an ta’ba ta, ganin Zarah ne yasa ta rungume ta tare da fashewa da kuka.
Bubbuga mata baya Zarah tayi tare da cewa” lafia Husna? mai ya faru? mai akai miki?”
Cikin kuka tace” Zarah Auwal bai sona, da da yadda zanyi dana cireshi a cikin raina na huta. Zarah ina tsananin ‘kaunar sa”.
“Ni kad’ai nake haukata tunda aka fara shirin bikin nan, dai-dai da sau d’aya ya’ki halattan biki ko guda d’aya da aka gudanar. Gashi a halin yanzu ‘karyana ya ‘kare”.
” Ya zanyi Zarah? ki gayamin, gashi anjima za’ai dinner ban san yadda zanyi yai attending ba”.
Tace tana mai fashewa da matsanancin kuka.
Itama yanzu Zarah ta fara jin haushin abinda angon nan yake, mai yake ta’kama dashi?
Mai yasa baison Husna? Husna yarinya ce kyakkyawa, fara doguwa ga hanci ga zarara zaran yatsu, idanu.
Jiki ma masha Allah komai akwai, babu abinda tarasa na wanda d’ana miji yake so.
Uwa uba ilimi boko da na islama.
Ya fara bani haushi inason sanin abinda yake ta’kama dashi.
‘Dago Husna daga jikin ta tayi tare da cewa tana mai kallon cikin idan uwan ta had’e da share mata hawaye.
“Husna tashi muje mu same shi” zaro ido tayi tare da cewa cikin tsoro” gaskiya bazan iya zuwa ba inajin tsoro gaskiya “.
Tsaki Zarah tayi tare da cewa” tsoro ya kasheki ya kuma kaiki ya baro”.
“Tashi dallah muje” tace tana mai jan hannun ta.
Girgiza kai tayi idanun ta cike da hawaye tace” bazan iya ba, ya Auwal bai da mutunci nemo wani mafitan kawai amma ba wannan ba”.
“Kirasa a waya to” tace” ko nakira sa ba zai d’auka ba”.
“Bani number wayar sa” tace tana mai d’ako wayar ta.
Karanta mata Husna tayi ita kuma tana rubutawa.
Dialing number tayi, yayi ta ringing ba’a d’au call d’in ba.
Sake kira na biyu tayi sai da ya kusa tsinkewa sannan aka d’aga amma ba ai magana ba.
“Hello!” Zarah tace.
Zaune yake zumbur ya mi’ke tare da cewa” my baby, my Joyyyyyyyyyyyyyyyyyy”………………
COMMENTS
&
SHARE
Luv you all my fan’s????????????????????????????????????????????????