KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Basu zame ko ina ba sai bakin clinic d’in, shiga ciki sukayi sukai parking asibiti ba wani mai girma bane, ‘karamin asibiti ne sosai dagani da d’add’an asibiti ne, domin pentin duk ya kurkurje.
Koda suka fito daga motan sai Auwal ya kama rufe hanci.
Buge masa hannun yayan yayi tare da gargad’i san nan ya saura rawa kansa.
“” Yaya”” waigo wa yayi tare da hararan sa, bai damu ba yasake cewa ciki marai rai cewa kamar zaiyi kuka “” yaya inyi magana don Allah, idan kayi sai naci ‘kaniyar ka, basan jin shirmen ka yanzu “”.
Turo baki yayi irin na yaran nan ‘yan shekaru uku had’u.
“”Toni bani ne zanyi maganan ba ai yaya, bakina ne keson yayi maganan”” dariya ne yaso su’buce ma yayan amma sai ya matse tare da mai kashed’i da ido.
Don haka sai yayi shiru bai sake cewa komai ba.
Office d’in babban mutum dake kula da asibitin suka shiga, domin yayan sai da yazo satin can suka gama komai da komai da mutumin.
Kawai kawo sa dama yayi.
Domin har wurin kwana ansa mar masa wani gida madai daici mai d’an kyau dashi kusa da asibitin ne.
Gidan na kusa da nasu Aisha, yana kallon jikin gidan su Joy, sayan gidan yayan yayi kawai don ‘kanin nasa kar ya takura sosai.
Komai na bu’kata ya samar masa harta kayan abinci ya zuba masa wanda sai yafi shekara anaci sai dai abama wasu.
Don haka koda suka gama da ogan sai suka fito ya rakosu domin kai Auwal gidan sa.
Bayan ya gama duk wani abu da zai masa sai yayi sallama da ‘kanin sa tausayin sa fal a ransa amma guma su masa haka, don haka kila ya sassautawa Kansa.
Suna saran ‘kila yayi hankali.
***
Bai dawo gidan ba sai da yaga tashin yayan nasa sanan ya juyo gida ba’kin ciki dam a cikin ransa.
A cikin gidan parlour ne mai dai dai ci, sai da kwai toilet da kitchen a cikin parloun, d’aki gudu biyu.
‘Daya ne aka saka masa gado mai d’an kyau, sofa da kayan bu’katan d’a namiji, suturu da sauran su.
‘Dayan ko dam da kayan abinci.
Kitchen ma komai yasa masa haka ya zaga ya duba komai na gidan, ya yaba da ‘ko’karin d’an uwan sa, domin yasan babu wanda zai masa sai shi.
Don haka wanka yayi tare da kintsa kansa cikin gajeran Wanda da farin singlet, domin garin da zafi.
Shiga kitchen yayi domin yanaji yunwa, domin sabda maganan tafiyan nan ba wani abu yake ci ba, baida kwanciyan hankali ci.
Don haka kar yama kansa horo da yawa, sai ya dafa abu mai d’an sau’ki yaci, bayan ya gama yaji kiran sallah la’asar don haka sai ya saka milk d’in jallabiyan tare da fito wa daga gidan bayan ya rufe ko inah.
Kalle kallen wurin ya tsayayi na wani lokaci sa’an nan ya nufin masallacin da yake hango wa nesa da gidan nasa.
***
Tunda ya fito mutane sai faman kallon sa suke, maza da mata, muslmai da arna, ba wai yau suka saba ganin ‘yan birni ba, amma wanann na daban ne, gani ma suke yafi wad’an can.
Kallon da suke masa haka yana ‘bata masa rai.
Har a masallacin ma bai tsira ba, wasu har ‘kus’kus suke suna tambayan wanan baturen daga inah? mai kuma yazo yi?, babu ansa don haka suka ‘karici gulman su sukai shiru.
Cikin ‘kan’kani Auwal yayi sallah, ana idarwa ya fito domin tsami kawai yake ta sha’ka “” wai ai sai cikina ya kumbura, fut”” ya tofar da yamu.
Nufo gida yayi yana mai yatsina, yana gaf da ‘karisowa gidan nasa ya hango ‘yan mata biyu suna tahowa da uniform a jikin su, kallon d’aya ya musu ya d’auke kai a zuciyar sa ko yace “” yanzu dama da makaran ta a garin nan shine ‘KAUYEN ci da gidadanci bai barsu ba? hu’um””.
Aisha tayi gida tana ce da Joy “” besty don Allah gobe banda latti, kinji?”” Kai kawai ta gyad’a mata ta shige gida itama tayi gida, dai-dai nan shima yazo jikin gidan nasa bud’e wa yayi ya shiga yana mai ta’be baki.
“” Wow, ashe akwai masu d’an waye wa?”” Domin tunda suka gansa suka d’auke kai.
Basu damu da ganin ba’kon fuskan da suka gani ba.
“” Kai amma faran nan zatai girman kantsiya, matsiyaci ji gidan su, kai zatai girman kai”” tsaki yayi.
“” Wayyo mami, zufa zai illatani, fanka ne kawai, ga inji ba, yanzu ya zan mami na? kum…….
‘Karan wayar sace tasa yayi tare da zuwa wurin wayar.
Ganin mai kiran nasa yasashi saki lallausan murmushi.
Da murmushi a fuskan sa yace “” My love ya kike?, bros kana lafia dai ko? babu wani damuwa ko? idan akwai please kagayamin kaji d’an ‘kanina, ina sauraron ka, tell me kaji my boy?”” .
Zum’ba baki yayi yace “” am not a boy, I’ m a big man”” smiling tayi ”naji to, yanzu ka girma ko?” banza da ita yayi.
Da gangan tayi, tasani sarai baison a kirasa da yaro, “” autan mami shalelen Rahama baka jina ne?, ina sauraron ka, fad’a min mai kake so “”.
Turo baki yayi kamar tana gaban sa ya shagwa’be murya “” ba komai, yanzu yaushe zaki dawo, kimin al’kawarin bazaki dawo da ciwon nan a tare dake ba, please sister ki warke da wuri ‘kaninki na bu’katarki kusa dashi kinji?”” tausayin ‘kanin nata ne ya kamata.
Hawaye taji na sauka akan kyakkyawan fuskan ta.
Sharewa tayi tare da cewa “” very soon zan dawo kaji, okay promise?, y promise “”.
“” Yanzu dai kace baka bu’katan komai ko?”” lumshe ido yayi sanan ya jadda mata baida bu’katan komai.
Sun d’au tsahon lokaci suna waya kamar karsu rabu.
Haka mami ta kirasa itama sun dad’e suna waya ta kuma kwantar masa da hankali.
Kowa na gida ya kirasa, kowa ya nuna damuwa akan sa, hakan yasa ya rage damuwan da yake ciki.
Don haka wunin ranan cikin kwanciyan hankali ya kwana.
***
Washe gari zai ya d’an tashi da wuri, saboda yasan zashi asibiti, bayan yayi sallah sai ya koma barci, bai tashi ba sai kusan 7:00am, don haka wanka yayi a sukuni, yayi break fast ya shirya ciki kayan N Y C E, kayan sun ba’in yin masa kyau, sun kar’besa sosai.
Kusan takwas saura a fito gidan yana rufe ‘kofar gidan su Joy suka fito daga gidan su Aisha da shirin makaranta a jikin su ko ba’a fad’a maka ba, kasan makaranta zasu.
Kamar jiya kallo d’aya Aisha ta masa ta d’auke kai, Joy kuwa kallon ma bai samu daga gare taba.
Shima haka take a gare sa.
Hanyan asibiti ya nufa suma dole tanan ne hanyan su, suna gaba yana bayan su, yana mai mamakin girman kan yaran.
“” Ji wancan ita kuma bata san tana tana da ‘kiba bane ta d’inka kaya yana baiyanar da suran jikin ta, jifah, anya ba ‘yar iska bace, ji yadda take kad’asu, oho god help me kada damuwa na ya motsa””.
Samun kansa yayi da ‘kin kauda idon sa har suka ‘kule masa shi kuma ya shiga asibiti.
Sunyi nisa suna ta ta’ba fira Aisha tace “”besty wallahi ba’kon birnin can ya tafi da emani na, ya had’u wallahi, banci yafi ‘karfina da nace inaso””.
Tsaki Joy ta saki kamar bazatai magana ba kuma sai tace “” amma dai ke banza ne, kina mace ki zubar da ‘kimanki ta ‘ya mace, tir miki wallahi “”.
Dariya Aisha tayi tare da cewa “”haka kawai sai na cuci kaina bazan fad’i abinda ke raina ba, wash har naji sa’kin abinda ke damuna saboda na fad’a wa besty na, jiya fa ko barci na kasa, don ko makaranta dare na kasa zuwa, saboda tunanin sa ya hanmin ‘karfi da kuzari”‘.
“” Besty don Allah idan mun dawo ki rakani wurin sa, na sanar ma ina tsanani ‘kaunar sa””.
Wani uban hararan da Joy ta wurga mata yasa ta had’iye sauran maganan ta.
Comment & share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????
‘KAUYEN ‘YAR KADDE
???????? ????????????????????
(Ta'kai taccen labari)
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili