KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
MASAUKIN SO
SHI NAKE JIRA
BA JINSIN MU BACE
HAMDIYA DA HAMNA

Bismillahir Rahamanir Rahim

????9⃣to1⃣0⃣

Yau har suka fita ‘KAUYEN basu samu mashin ba, haka suka ‘karisa makarantan a ‘kasa, domin sai da suka kusa zuwa makaranta sannan suka samu, Aisha zata tsaida, Joy tace “” Allah baza mu hauba, da yake mu asararrune mukusa makaranta sai mu hauko? to badani ba, yau akaiwa baba kud’in sa”” dariya Aisha tayi “” kai besty”” bata kulata ba suka cigaba da tafiya har suka ‘karisa makarantan, Joy na ba’in tsoron bulala amma miskilancin ta baisa mutum ya gane domin ba nunawa take ba.

Aiko sunsha dukan late, domin sai da aka musu bulala har goma, ko gezau Joy batayi ba, Aisha ko sai da tai kuka.

Sai faman tsine wanda ya bugesu take a zuciyar ta, “” basu da imani basu la’akari da nisan da mutum yake””.

Haka taita ‘kun’kunai har suka shiga class.

Auwal kuwa bayan ya shiga asibitin abinda ya kawo shi ya fara, sai faman yatsina yake.

3:00pm dai-dai yabar asibitin, gida ya dawo yayi wanka tare da dafa cous cous yaci, ya kwanta domin ya huta, ko ina na jikin sa sai faman ansawa yake alamun gajiya ne zaryan atare dashi.

Kai wannan Auwal d’in akwai la’kaumanci, ya saba komai masa ake, sai abinda ba’a sashiba zaka gansa kan gaba.

Girki kam ko mace albarka, domin sai dai mami bata shiga kitchen ba, indai tana ciki shi kuma yana gida zagewa yake yana taya ta aiki.

Saboda tayata da yake ba wani nau’in abinci da bai iya ba, banda wanan Auwal bada son jiki ba, kuma bai iya komai ba bayan wannan.

Amma akwai ‘ko’kari sosai ta fannin karatu.

3:45pm ya tashi yayi masallaci, bayan an idar da sallah sai ya fito, zama yayi a ‘kofar gidansa yana ganin masu kai da dawo wa, duk wanda zai wuce sai ya kafa masa ido yana kallon sa kamar zasu cinye sa.

Yana zaune Aisha ta fito daga gidan su, dauke da littafain a hannun ta, ga hijabi har ‘kasa dagani islamiya zata.

Kallo d’aya ya d’auke kansa, wuce shi tayi ba tare da ta kulasa ba.

“”To ita d’ayar fah?”” yace a cikin zuciyar sa, can kuma sai ya ta’be baki tare da cewa “” to ina ruwana”” haka ya d’au tsahon lokaci zaune a wurin nan, domin har lokacin tashin su Aisha a makaranta yayi ta dawo ta same sa a wurin da ta barsa.

Sai da yayi magriba da i’sha sanan ya koma gida.

             ***

Yau kwana Kwana uku kenan Joy na fama da ciwon ciki, kuma ciwo irin sosan nan, miskilanci ya hanata nunawa a fuska balle ta bud’i baki tayi magana.

Saboda miskilancin ta shiyasa sam uwar bata gane ba, da dare yayi haka ta tashi zata fita.

Har takai bakin ‘kofa uwan tace “”where are you going?”” turo baki tayi sanan tace “” gidan su Aisha zani, kina ganin dare yayi sosai ko?”” d’aga mata kai kawai tayi.

“” Karki dad’e”” shima d’aga kai tayi ta ‘kara gaba.

****Auwal zaune a ‘kofar gidan sa, yana shan iska, abin dad’i da ‘KAUYEN nan sam basu da sauro, kasan cewan ana zafi shiyasa ya fito yana shan iskan waje.

Dare ne, babu wuta sam a garin amma farin wata kamar rana.

Yana d’an kalle kallen sa, sai yaga Joy tsaye a ‘kofar gidan su kamar meneman wani abu.

Kallo d’aya yayi mata ya d’auke kai, tare da koran shed’an.

Domin sanye take da guntun vest da gajeran wando, wanda ko rabin cinyan ta baiyi ba.

“” Anya wanan yarinyan ba karuwa bace kuwa? A fuska kamar MUMMiNA SADI’QA (littafin sis rukyn Mamah, kuyi maza masoya ku garzaya karku bari abaku labari, domin ta baza basira da fasaha a cikin mashahurin littafin nan nata)., amma a zahiri abin ba kyan gani, kai Allah mana tsari da kyan d’an mazuru, tur””.

“” I hate her”” yace tare da to far da yamu.

Itako bata san yanayi ba sam, shigewa gidan su Aisha tayi da sallama d’auke a bakin ta.

Baban Aisha n da maman ta suna daga d’aki, Aisha ce kawai a tsakar gidan itace ta ansa mata tare da kallon ta da mamaki d’auke a fuskan ta.

Cikin ‘kasa da murya tace “” besty meye haka?”” cikin yatsina ta kalle ta tana neman ‘Karin bayani.

Tashi tayi ta jata cikin d’akin ta, Allah yasa babu ‘kannin ta duk sunyi barci.

“” Besty meye haka don Allah? look at you”” ta’be baki tayi tana mai kallon jikin ta.

Ta gane sarai mai take magana akai amma sai tai biris da ita, neman wuri ma tayi ta kwanta.

Tana mai cije le’be, domin a wanan lokacin ciwon taji ya taso mata.

“” Besty don Allah kibar irin wanan shigan, domin baida tsari sam ko addini ma ya han………, tsaya malama, kina manta cewa addini nan da naki ba d’aya bane ko? mu bamu takura sai kije can ki ‘kara malama”” tace cikin masifa.

Da mamaki take kallon ‘kawar tata, domin hakan ba halin ta bane sam, komai tace mata tana binta da idone kawai.

Kuma takan d’auki magana ta da mahimmanci, sa’banin yau.

Gani ta dafe ciki hawaye na zubo mata yasa ta ‘karisa da gudu gare ta, tana cewa “” menene besty? “” shiru bata tanka taba, tana ri’ke da ciki

“” Nine ko?, sorry na bari bazan sake ba, kiyi ha’kuri besty bansan kina irin wanan shigan sam, domin zai bawa ‘yan iska ko wad’an da basu kai zuciya nesa ba yin miki fayd’e, amma kiyi ha’kuri idan yayi miki zafi bazan sake ba “” tace cikin sanyin murya.

Shiru bata tanka taba, sai dai tabar hawayen, idon tama ta rufe kamar zatai barci.

Ta d’au tsahon lokaci a haka kafin ta tashi tayi gida ba tare da ta kulata ba.

Addu’a Aisha tayi a zuciyar ta “” ya Allah kaceto wanan baiwa taka””.

Barcin ranan batayi shiba, domin cikin ya matsa mata.

            ***

Washe gari Sunday, rana da Joy tsaneshi a rayuwar ta bata san meyasa ba, batason ranan.

Ko nace ta tsani zuwa church, indai maman ta tasa ta sukaje to mudin taje to sai ta kwana da ciwon kai mai tsanani.

Ranan ne ranan ni’ku ni’kun ta, balle yau ya had’e mata da ciwon mara.

Tuda madam Gloria ta tashi take mata fad’an ta tashi tayi duk abinda zatai, “” yau banzan d’au iskancin da kikayi na satin can ba,, ki tashi maza”” ko cikan ka batace mata ba.

Bata damuba domin ta saba da hakan.

Ciwon na cinta ta tashi 6:37am tayi bayi, wanka tayi ta fito, shiryawa tayi cikin gajeran blue d’in riga, ta wuce guwwa.

Rigan tayi mata kyau sosai, ta fitar mata da shape d’in ta sosai.

Tea uwan ta mi’ka mata “” ki kwana kinasha na tafi karki zo a kan lokaci, yau sai ma’kota sun ‘kwaceki””.

Tayi ‘kwafa tare da fita bubble d’auke a hannun ta kannan yasha gashin doki.

Toshi ina Joy ta samo suma ne?????. gare Ku fan’s ina jiran ansa.

Ruwan zafin kawai ta shanye bread d’in ta aje, d’aukan siririn gyalen ta ba’ki ta yafa ta rufo gidan ta fita.

Tafiyan ta na yau yafi na kullum nawa, daurewa kawai take take taka wan, domin duk d’aga ‘kafan da zatai sai taji cikin kamar ba nata ba.

A haka taje church d’in wurin 8:20am, lokacin har sun fara wa’ke wa’ken su da raye-rayen su.

Shiga tayi cikin ba’kin ciki.

Uwan na ganin ta ta banka mata harara, bata damu ba taje can baya tai kwanciyan ta hankali kwance.

Ciwon ranga ranga ya taso mata da kwanciyan ta kad’an.
Bata san sanda ta ‘kwala ehu ba.

Ehun ta yasa uwan ta nufota tana surkulensu.

Kan kace me hankali kowa ya dawo kanta, pastor ya fara mata addu’a, yanayi yana tatta’bata.

Ganin yaune damanshi na ‘karshe da zai maida miyonsa yasa yace akaita gidan sa zai mata addu’a na musamman.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button